BAK’A CE Page 31 to 40

Juyawa ta yi wajen madubi tana kallon kanta, a fili ta ce” nima mai karfi ce!
Yana shiga falon ya tarar da su Mu.azam da Ayya da Khadija dake zaune zuru Ayya fuskarta a dan hade ba kamar kowani lokaci ba,
Tana ganninsa ta bala masa harara ta kauda kanta,
Murmushi ya yi a fili ya zauna yana duban Alhinayett dake son karantar yanayinsa, ya maida dubansa wajen Mu.azam,
Murmushi ya sakar masa sannan da ido ya yi masa maganar da shi kawai ya gane,
Mikewa ya yi ya bi bayan Ayya da ta mike ta yi sama dan ya san tana son ganinsa ne aman ba zata fada ba a gaban mutane
Yana shiga ta mike da zafi zafi tamkar zata wanke shi da mari ta ja tunga gabansa ta ce” kai! , kai! Ka fita a idona na rufe! Kai Wardugu na fika danyen kai, yanzu dan raini ka zo na baka damar zuwa daurowa yarinya aure ka dawo dan bahagumen tunani ba zaka zo ka fada min ya aka yi ba? Sannan yau ya shigo min da zankadediyar budurwa ya fada min aminiyarsa ce? Ohk tare kuke amintar kai da shi da yan matan ko? Ba zai yiwu ba, ba zan bashi y’ata a wannan halin ya je min da ita wata uwa duniyar ba, ba zan lamunci ya dauki y’ar amana ya tafi nesa da ita ba, wannan yarinyar tamkar marainiya take nesa da iyayenta, nice uwarta nice ubanta, kuma ina son abina, Wardugu ba zan lamunci shashancin nan ba!
A hankali ya ja hannunta har bakin gado ya zaunar da ita, idannuwansa sun kade sun masa ja, ya kamo hannun nata ya ce” *Ayya, a cikin gidan duniya, lungu lungu, ba inda kafata ba zata shigaba dan gannin halin da take ciki, ba zan lamunci ko kuda ya yi mata ilah ba!*
Da mamaki take dubansa, yannayin yanda ya yi maganar har wata jijiya a gaban goshinsa take motsawa irin magana ne yake da zuciyarsa da gangar jikinsa,
Mikewa ya yi ya yi taku biyu zuwa uku ya dawo yana mai yamutsa gashin kansa ya zauna ya ce” Mu.azam bashi da lafia, wannan aminiyarsa ce mafi kusanci da shi, ta zo min da maganar tana so a yi masa aiki wanda idan Allah ya taimake mu aka dace zai tashi, Ayya na roke ki, ki saki ranki, ki yiwa dukan lamarinnan kyakyawan gani, ki bashi matarsa su tafi,
Galala take dubansa har ya karasa maganar ya mike ya nufi fita,
Kuma juyowa ya yi ya ce” Walyn ce ta ba lafia, zan je clinik
Damuwarta ta nuna da yi masa adu.a, taso ma binsa aman ya nuna ta yi zamanta dan yayi imanin in dai Walyn na cikin hayacinta sai ta batawa mahaifiyarsa duda tana boyewa shi ai ba makaho bane,
Yana fitowa ya tsurawa kofar Agaishat ido, wani abin na tunzura shi ya je wani na hana shi,
A hankali ya taka ya je kofar dakin ya tsaya,
Hannunsa ya dora saman abin budewar ya lumshe ido,
Da sauri ya saki ya juya sai dai me Alhinayett ce tsaye, bai san lokacin da ta hayo ba, bai san ko tun fitowarsa take wajen ba, idannuwansa sun rufe,
Hade fuska ya yi tam irin karma ta ga fuska ta kawo masa raini,
Rabata ya yi ya fice ya sauka kasa inda ta bi shi da wani irin kallo,
Hannayenta biyu ta dora saman kanta, ta shiga girgiza kai da yaren buzanci ta ce” na shiga uku Nauyin baki ya saka aminina tafka barna, Wardugu me ka aikata haka?
Tura kofar Agaishat ta yi ta shiga da salama,
Agaishat dake kwonce saman bed ta mirgino tana amsawa da murmushi shinfide a fuskarta tana duban Alhinayett,
A nitse Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat inda ta mike zaune tana duban yannayinta,
Hannayenta Alhinayett ta kamo tana dubanta cikin yaren buzanci ta ce” Tarhanine (masoyiya), ina son mu yi magana da ke.
Agaishat ta bata hankalinta sosai ,
Alhinayett ta ce” ban taba aure ba, aman a islamiya an fada mana irin girma da darajar aure da kuma girman ikon miji a kan mata,
Sunna ce ta ma.aiki, daga lokacin da aka daura aurenki maganar mijinku ta fi iko kanki fiye da ta iyayenki, kin ga kuwa banban nauyi ne da bawa zai kasa rintsawa idan ya tuna,
A yanzu ba maganar kina sonsa ko bakya sonsa, ba maganar ke wata ce ko wani ya tsaya maki, in dai mace na tsoron haduwarta da ubangiji to ya zama dole ta gane itace karama mijinta ne baba, ta yi masa biyaya.
Agaishat, ki yiwa Mu.azam biyaya, kin samu tarbiya domin zaman da nayi da ke na dan lokaci jifa jifa ban ga rawar kai , tsayaya a tare da ke ba, zan so mijin aurenki ya yabe ki, ki ci gaba da girmama Ayya domin uwace a gare ki, ki nuna mata hankalinki ya kwonta da auren ko natama zai kwonta, kar ki tsananta bincike Agaishat, ke dai ki yi ta rokon Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi,
Tunda ta fara Agaishat kallonta take, ita sai yanzuma tsoro ya shigeta, aure, aure, bautar Allah, sunnar ma.aiki, da tana tunanin ta yi nisa da iyayenta a hankali hankalinta ya kwonta da su Ayay harma ta samu gurbi mai girma ta basu a zuciyarta, aman yanzu gashi an mata aure? Kuma bama a kasar zasu zauna da mijin ba domin Mu.azam na shirye shiryen su daga da Agaishat ne?
Hannayen Alhinayett ta damke tana dubanta ta ce” *ina jin tsoro, bana son barin su*,
A hankali ta dora kanta saman cinyar Alhinayett inda ita kuwa take dan bubuga bayanta alamar rarashi
Yana zuwa kai tsaye office din likitan ya je, wanda ya tataba za.a mika takardun matarsa can ne dan hatsari ne
Gaisawa suka yi inda likitan ya nuna masa wajen zama,
Labarin lokaci da yannayin da aka kawota ya bashi, inda ya ce” tanada shigar yaron ciki ne kuma ta karya da cokacola mai karfi bata ci komai bayan hakan ba,
Shi ya hadasa mata ciwon ciki mai tsanani ko nace mara hakan ya saka gudan jinin ya shiga barazanar zubewa, tana cikin wannan halin ta samu hatsarin domin ciwon ya girmami nutsuwarta,
A hankali ya dago da idannuwansa ya sauke kan doctern, idannuwansa ya lumshe yana jin wani irin dadi na ratsa shi, ciki, a daidai lokacin da ya rasa wani abin ya samu wani,
Murya a kausashe ya ce” *Cikina, ba abinda ya samu cikina?*
To fa????????????, na zama raguwa, tun safe nake tsakurar rubutun nan????????????????????????????????????????????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
Na
*SAJIDA*
4️⃣8️⃣
Da sauri docter ya bai Wardugu amsa gamsashiya tare da nuna masa echo din cikin, cewar bai yi kwari ba ya so zubewa aman Allah ya tsayar da shi, dan haka a kiyaye du wani abinda zai zo mata da garaje har ya zauna ya yi kwari,
Kansa kawai yake gyadawa kafin ya mike ya nufi number dakin da aka fada masa take
Yana zuwa ya kwonkwasa , bai tsaya an bashi izinin shiga ba ya tura ya shiga,
Walyn ce zaune tana rusawa mahaifiyarta kuka inda uwar ke fadan da bai fahinci na meye ba,
Gannin mai shigowar ya saka gaba dayansu sukai kit suka daina maganar inda Wardugu ya nuna tamkar bai ga abinda suke ba,
A hankali ya karasa wajen kujerar dake dan nesa da su inda mahaifiyar Walyn ta saki hannunta ta mike daga kujerar dake kusa da walyn din tana mai son ta bar dakin
A nitse ya gaisar da ita inda ta amsa kafin take barin dakin tana jin wani irin haushin Walyn, ta sha jus din nan ne dan cikin ya zube, da ba.a yi gagawar kawota asibiti ba da tabas sai mai afkuwa ta afku, bata san wa zata fadawa dan ya tsoratar da Walyn ba domin ba wanda take tsoro!
Bayan fitar mahaifiyarta a hankali ta kwonta saman bed din tana kallon sama,
Wardugu dake yi mata kallon kasa kasa ha jima a haka kafin yake tasowa ya dawo kujerar dake kusa da ita ya ja ya zauna,