BAK’A CE Page 31 to 40

Rigar jikinta ta atampa wace akai mata dinkin zamani ya dora hannunsa wajen mararta ya samu ya dage rigar a hankali,
Lalausan hannunsa ya dora saman mararta, a hankali ya shafa ya jara shafawa, ba zai gane komai ba shi dai yanda cikinta yake ne bai wani canza ba, tana da dan teba kadan, ko dan an ce cikin bai girma bane?
Kalonsa ya maida wajen fuskarta a hankali tamkar bai so magana ba ya ce” ina son cikina Walyn, kema kina so?
Wani katutun abu ya tsaya mata a makogwaro, ina ita fa ba zata iya wannan lamarin ba, ka haifi dan uban ya dawo sonsa fiye da kai, ba zata iya barin wannan cikin ba duda kuwa azabar da ta sha,
Gannin tana ta yamutsa fuska ne ya saka shi kara kusanta kansa da ita ya ce”wani waje na maki ciwo ne?
Da haushi haushi ta dube shi ta ce” tun cikin bai zama gudan jini ba, ba.a kai ga halitarsa ba, har ka fara manta abinda ya dace ka fara damuwa da shi? Har ka fara manta nice damuwarka ta farko domin nice zahiri?
A hankali ya janye hannunsa daga wuyanta yana dubanta da wani irin yannayi, tafia ya yi ya dawo basu wani hadu ba, tun maganar da ta yaba masa a agadez basu wani hadu ba, shima ya shareta ya shiga harkokin gabansa, yanzu sun hadun zata wani saka shi gaba da hayaniya kamar yaronta, du irin murnar karuwar da ya samu da dokin da ya afka sai ya ji lokaci guda ya dishe, dubanta ya yi irin na tsai din nan,
Hannunsa ya saka a aljihun doguwar jalabiyarsa ya ciro cart dinsa ta bank,
Ajiye mata ya yi nan ya juya ba tare da yace da ita ufan ba,
Tana kallonsa har ya fita a dakin,
Ba.a jima ba mahaifiyarta ta shigo dakin tana dubanta ,
Wani uban tsaki ta ja ta ce” kin masa haukan ne?
Walyn ta dafe kanta ta dauki cart din ta mikawa uwar ta ce” Ma, ga abinda kike nema! Plz kama ki barni na ja numfashi mai dadi!
Yannayin maganar walyn, da irin furucinta bai taba zuciyar mahaifiyarta ba, hasalima dokin karbar tikitin bankin Wardugu ya sakata sakin murmushi ta karba ta fita da hanzari bayan ta shaidawa yar zata turo a tayata komawa gida ta karbi code number dinsa.
Bayan ya karaso gida dakinsa ya shige,
Yana shiga ya cire rigar da ya kusan wuni da ita ya kaita wajen injin wankinsa ya ajiye ba tare da ya wanke ba dan hankalinsa ba nan yake ba
Dawowa ya yi ya shige bayi ya yi wanka ya dauro alwallah,
Sallah ya yi a nitse, bayan ya salamce ya mika hannu ya dauko wayarsa android ya kuna,
Yana kunnawa data na hawa domin baya kasheta kwata kwata,
Ba.a jima ba messages suka shiga shigowa na mutane daban daban, tun daga abokan aiki, manyan mutanen da yake hulda da su, da yawa kan harkar mota ne da yake siyarwa, wasun kan kamen da ya yi ne watani da suka shude, wasun baima bude ba dan bakin number ne,
Yana bin messages din yana karantawa sai dai baya bada amsa,
Nan ya fita ya shiga Facebook, roger banasaran da suke harkar motoci da shi ya masa sababin zubi, zubi na sababin motaci na manyan mutane,
Yana dubawa ya ga number yarinyarnan dai sai kara turo masa gayata take , a whatsupp ma sai message take turo masa tana karawa,
Fita ya yo ya koma whatsupp ya shiga message dinta,
Duka kalamaine na rarashi, da magiyar ya kulata, da yannayin kaskantar da kai, wai ita BASMA yar gidan minister,
Hotunanta da take ta turo masa ya bude,
A hankali ya tsurawa hotunan ido yana kallo,
Kansa ya girgiza ya fita ba tare da ya bata amsa ba,
Mesage ta turo kamar haka” du bakin da zai furta kalmar so ba makiyi bane, sannan adini bai haramta mace ta nuna tana son namiji ba, kuma ni ban roki wayar gari da kaunarka ba, kar ka ja zuciyata a kasa dan Allah ya baka dama,
Mesage din yake bi yana karawa, bai iya bata wata doguwar amsa ba sai mikewa ya yi da wayar a hannunsa ya haye saman bed dinsa ya kwonta ya jawo pilow ya dora kansa, a ransa ya ayyana” haka fa suke idan suna so, da dama ta same su sai su fara gwada halaya na rashin tarbiya da hadama,
Yana kokarin neman baci wayarsa ta shiga ruri,
Kansa ya shafa yana jan tsaki,
Kin kula wayar ya yi sai da ya ga mai kiran ya fishi naci ya dauko wayar ya daga yana fadin” ai aikin nan sai kai daman!
Mu.azam ya yi murmushi, ya ce” me tace da kai Wardugu,
Wardugu ya yatsina fuska ya ce” wace fa?
Mu.azam dake zaune yana hangen shige da ficen Agaishat kicin tana girki ya ce” wardugu mana, bakuwata man
Wardugu ya bude idannuwansa ya ce” meye tsakaninka da ita bayan amintaka?
Mu.azam ya yi tsam gabansa na dan faduwa, a hankali yake goge zufar da yake ya ce” amintaka ce mafi kusanci,
Budurwarka ce? Wardugu ya kaste shi,
Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya, ya kasa magana hakan ya tabatarwa da Wardugu zarginsa
Ransa ne ya ji ya mugun baci, hannunsa ya jimke ya kaiwa garu duka ya kausasa murya ya ce” dan me ka shigi yarinyar mutane bayan ka san amana ce?
Mu.azam ya mike zumbur dan yannayin muryar Wardugu ya shaida masa ransa ya baci,
A nitse ya ce” ka kwontar da hankalinka Wardugu, bamu yi soyaya da ita ba, itace ke so na, bamu tana soyaya da ita ba, ban zowa Agaishat dan na cuceta ba, kuma ba zan taba gigin cutar nata ba,
Wardugu dake tsaye shima ya dafe gaban goshinsa, baya jin zai baiwa Mu.azam amsa a wannan maganar,
Mu.azam ya ce” Wardugu, dan *ina sonta* na aureta,
Wardugu ya matse karfen jikin bed dinsa yana rintse ido, kansa yake ji na mugun sara masa, hakama juwa na dibansa,
Mu.azam ya kara sasauta murya ya ce” ina son mu tafi , na san ka san komai game da abinda yarinyar nan ta zo da shi, Wardugu koda ban auri Khadija ba tana da darajar da ba zan misalta maka ba a raina, tamkar yar uwata na fauketa kamar yanda na dauke ka, zan bita a min aikin nan, idan Allah ya yi na rayu zan tashi na rayu da *Matata*, idan ban rayu ba na san zaka kula da *Iyalina*, gobe ake bani passport din Agaishat, Khadija bata zo ba sai da ta shirya domin komawata da shigana block duka ta irga min kwana tara ya yi saura, Wardugu ka……
Wardugu ya katse shi da wani irin yannayi ya ce” *Zaka rayu in sha Allah*! Ku ci gaba da shirin tafia, in sha Allah ina nan za.a shiga aikinka, zaka rayu Mu.azam……
????
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????*
____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
Na
*SAJIDA*
4️⃣9️⃣
Bai jira amsar Mu.azam ba, Wardugu ya silale yana dafe kansa, a fili ya furta” *ban shirya ba, ba zan iya dauka ba, bani da karfin kokowa da hakan, sannan haramun ne a gareni, ya Allah baka dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba, Allah ka cire min wannan gingirmin mikin , domin ni dai ban saba ba*!!!!!
Timiya
Duniya sabuwa ce ta budewa Ba, wannan karon da sabon salo domin kuwa tafe yake da isa da takama da nuna kansa a matsayin uban *BAk’a*,
Anna dubansa kawai take idan yana abubuwansa, bata taba buda bakinta tace da shi uffan ba, a cikin kudin ya basu million guda wada Mariama ta karbe , ya canza masu katifa ya kawo masu buhun dawa guda ya yar masu sannan ya shiga fakar takun Anna yana so ta koma turaka
Kamar yau, zaune suke su hudu domin Gaishata ta zo masu , labari suke duka yawan zancen a je a dawo ne a tile kan maganar Agaishat,