BAK’A CE Page 31 to 40

Anna ta sauke ajiyar zuciya tana dubansu ta ce” mahakurci mawadaci, du wanda ya ce zai yi hakuri Allah ba zai bashi kunya ba, sannu sannu kuma bata hana zuwa, sai dai a jima ba.a je ba,
Gaishata ta yi murmushin itama da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe ta ce” ni abinda ke bani mamaki Ba, wai shine har yake yi mana kallon mutunci?
Mariama ta tabe bakinta ta ce” na dan lokaci ne, idan kudin hannunsa ya kare zai dawo kamar da,
Anna ta ce” ki daina mumunan zato Mariama
Mariama ta yi mata wani malalacin murmushi dan kar ta yi fada,
Suna tsaka da zancen sai gashi ya shigo yana jan arzizimin wando bakinnan kuwa jajajir sansani su ta bata shi,
Bai yiwa yaren magana ba sai Anna ya kalla ya yi kiranta ya shige dakin
Da kallo suke binta dan gannin zuwa zata yi kuwa?
Gani sukai ta mike ta nufi dakin ba tare da ta yiwa kowa cikinsu magana ba
Tana shiga ya damko hannunta yana washe baki ya ce” Ke bakya marmarina? Kin jima baki neme ni ba, kin ga baki fice haihuwa ba, ki zo mu kara samun wata Bak’ar, ina son samun yarinya a gidannan,
Sakai kawai ta yi tana dubansa, kanta ta girgiza ta janye hannunta ta juya da niyar barin masa dakin
Ba da yannayin fushi ya ce” in kika yarda kika fita a dakin nan , sai na nuna maki na fi yan yamai *Niamey* iya rashin kunya!
Wani irin birki ta ja ta juyo da madaukakin tashin hankali da kuma tsoron da ya bayana karara a fuskarta,
Bakinta ta buda zatai magana sai dai ina jini ne ta shiga bin hancinta, juwa ta kwasheta ta zube nan tana fida wani irin numfashi
Karar faduwarta ya saka Mariama mikewa domin da marfin kwano a hannunta marfin ne ya kai kasa ya bada kara wanda sam Mariama bata yarda da shi ba dan haka da hanzari ta fada dakin tana mai kiran sunnan Anna,
Tana shiga daidai Ba ya kai kasa zai kamata jikinsa sai rawa yake,
Da mugun gudu da taratsi ta ce” kar ka tabata, kar ka taba mini uwata!
Bai sanma tana yi ba, shima fama yake ya ga ta mike, yau dai haukansa ya kaishi taka dokar da aka dodora masa na ya kiyaye kama mata sunnan garin haihuwarta, ya kiyaye du abinda zai alakantata da garin makarin duhun kan Anna shine Ba ya kusantata da asalinta, ya kama sunnan garin haihuwar Anna garin neman jarabarsa,
Ihun da Mariama ke yi masa ne ya saka yan uwanta shigowa suma a guje sunna nufar inda Ba da mariama ke turayar juna kan sai sun taba Anna
Gaishata ce ta dora hannayenta saman kanta da karfi ta ce” innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Ba Mariama ku dagata ku dagata na ce!
Tsai Ba ya yi , jikinsa na rawa ya nufo Gaishata tamkar zai maketa ya raba ta gefenta ya fice a gidan yana dumumuwa shi kadai ,
Da kyar suka iya cicibata domin Gaishata ba wani kokari zata iya yi ba sai su biyun ne suka iya kamata suka dora saman tabarmar kaban dakin
Hurhutu suke mata suna shafa mata ruwa aman ko motsi, sai numfashinta dake fita a hankali iamar a cicire ta samkame ita ba gawa ba ita ba rayaya ba,
Gaishata ce ta ciciba ta mike tana jin yanda mararta ke wani irin juya mata ta nufi kofa tana takawa da kyar tana saurin da zata iya ta nufi fada
Tunda ta karaso dogaran sarki ke mata sannu inda aka sakar mata hanya ta shige fadar suna mamakin ganninta domin sarki ya hanata zuwa fada kar a kake masa ita,
Kanta tsaye ta nufe shi inda ya mike da sauri daga kujerar mulkinsa dogarai suka shiga baza manyan rigunansu suna kare su, yan zama fada suka fara darewa da sauri sauri
Tana isa jikinsa ta zube wanda sukai taga taga dalilin kibar da ta kara ga kuma tsohon ciki,
A hankali ya samu ya daidaitata a jikinsa ya dora hannunsa inda ta dora nata wato saman cikinta da take ji baki daya yana wani irin yamutsa mata bayanta na sarawa,
Me ke damunki Gaishana,
Ya fada yana mai nuna tsantsar damuwarsa da tashin hankali, yanaiwa Gaisha soyaya mai karfin gaske,
Da kyar ta iya sauke ajiyar zuciya muryarta na rawa ta ce” Anna ce, Anna ce ta fadi, kuma tana numfashi aman ta ki farkawa,
Rigarsa ta jimke jin ciwon na tsananta ta ce” idan wani abin ya sami mahaifiyata zan shida duhu sarkina????????
Zaunar da ita ya yi saman kujerar ya cire babar rigarsa ta turkudi ya rufa mata ya yi gyaran murya,
Dogari ne ya amsa masa,
Sarki ya ce” ka je wajen jakadiya ingozoma ka fada mata Gimbiya na Daka.
Da gudu ya juya inda sarki ya daga karewar da akai masa ya fita da niyar zuwa gidan su Ba, yau kam za.a yita ta kare, ba zai yarda haka ana tayarwa matarsa hankali ba, ! Gashinnan tashin hankali ya sakata nakudar dole,
*Niamey*
Tunda Ayya ta fara magana tana duban Agaishat da dukan kulawa kan Agaishat ke kasa tana zubar da hawaye,
Abaya ce baka mai shegen kyau , bata da wata kwaliya sai zif din da ya hadeta a jikinta, gyaran fatar kwana biyun da Ayya ta yi ta dilketa ya saka fatarta ta kara wani haske da santsi wanda ko a ido ka dubeta zaka ga ta gyaru iya gyaruwa,
Dan kwalin Abayar ne ke dan zamewa tana rikeshi har ya kai karfinta ya kare ta sake shi ta duke sosai tana kuka inda gaba daya jikinta ke jijiga
Idannuwansa ya rintse da karfin gaske, sannan ya jimki kujerar da yake kai,
Kansa ya juyar gefe yana jin saukar kukan nata tamkar ana narkar masa da dalma a kahon zuciya,
Mu.azam dake gefensa shima cike da tausayin matar tasa ya mintsini hannun Wardugu yanai masa nuni da ya yi wani abin mana?
Wardugu ya juyo inda take suke Ayya na rarashinta itama na sharar hawayen ya hade fuska sosai ya ce” ke!
Yannayon yanda ya ambaci ke din sole ka tsorata, yannayi ne ya garwaye da halin da yake ciki,
Da sauri ta juyo tana kara shigewa jikin Ayya,
Mikewa ya yi ya ce” mu je!
Da sauri ta waigo wajen Ayya, wace rake cikin damuwar rabuwa da yar tata, wace kamar da wasa shakuwa mai girma ta kara shiga tsakaninsu,
Tun jiya ya dace su tafi aman cikin ikon Allah Agaishat ta rikice ta yi ta kuka har zazabi ya rufeta wai ita ba zata bisu ba,
Ayya ta yi gargadin ta yi fadan, ta dawo lalaba tana mai shaida mata tamkar suna tare ne, ga waya, ta bi mijinta zai dawo da ita da wuri
Kamar da gaske ta yarda a jiya da dare, a yanzu da suka shirya har Wardugu ya zo rakiyarsu ta kuma birkicewa,
Ayya ta ce” Wardugu kar ka yi mata da zafi mana, rabuwa da iyaye ba dadi ka lalabata na roke ka,
Wardugu ya juyo yana duban Ayya, idannuwansa sun kade sun yi jajir, a ransa kam birgeshima suke , su sun samu kukan, sun huta,
Lebensa ya dantse kawai ya girgiza kai ya dawo da wani irin taku ya dauki dan kwalinta dake kasa ya rufa mata , da idannuwansa ya yi mata nunin ta fice ko jikinta ya gaya mata,
Da sauri ta yi gaba tana waiwayen Ayya, wace ta koma saman kujerar tama fasa rakasu dan ba zata juri yanda Agaishat ke kukan ba zata je wata kasa ba, ba zata je ba ta fasa auren!
Ko a cikin mota Mu.azam na gaba ne, Agaishat da Mariama na baya, direba na jansu, ta madubi yake duban yanda ta yi lakwas da ita, yana matukar son ya rarasheta aman yana jin nauyin Mariama, baya so ran Mariamarma ya bace dan haka ya adanna rarashin idan sun sauka zai mata, duda har yanzu Mariama bata ce komai game da auren nasa ba, bata nuna damuwarta ki farin cikinta ba, haka shima kwata kwata baya nuna zumudinsa ko wata shakuwa tsakaninsa da amaryar tasa,
Mita wajen biyarce ke tafe har aeroport, suna karasawa inda ake ajiye motoci du suka firfito banda taron sojojin dake tare da su,