BAK’A CE Page 31 to 40

Wardugu ya bude gefen da yake ya fara fitar da kafarsa ta dama kafin ya fitar da ta hagu,
Yau a kakin sojoji yake, ya nanade hannayen rigar har saman damtsen hannunsa hakan ya baiwa rigar damar tamke shi, jijiyoyin hannunsa sun yi rado rado ,
Da karfinsa ya taka ya shiga inda iya su suka bi bayansa
Bakin gilas ne rufe da idannuwansa , duda haka zaka gane fuskarsa a tamke take ba alamar fara.a
Polisan dake aiki a wajen du idan ya zo ficewa sai sun sara masa, shi kuwa sai dai ya shige yau arzikin daga hannunma basa samu
A haka har suka karaso, yauma Allah ya so su da sun rasa jurgin domin lokaci ya tafi har an fara shiga
Tsaye ya yi a inda iyakar yan rakiya kennan, ya juyo wajen Mu.azam dake biye da shi,
Hannunsa ya kamo suka damke juna,
Murmushi Mu.azam ya sakar masa yana mai nuna masa ba komai ya kwontar da hankalinsa,
Bai bashi amsa ba sai kafadarsa da ya daka da hannunsa ya nuna masa sai ya zo,
Gaba Mu.azam ya yi shima yana mai jin zuciyarsa na tsintsinkewa ya nufi wajen da zai shiga jirgi dan an kirayi sunnan Khadija har ta yi gaba .
Du takunsa dan nufar wajen da take tsaye wanda wajen ya kasance hanyarsa ta fita, daidai da bugun zuciyarsa ne, bai so tsayawa ba, sai dai ya ji ya tsaya facing dinta
A hankali ya dora hannunsa dake dan bari kan habarta ya dago da ita inda ya tsare idannuwansa da kallo,
A hankali ya saka hannunsa na hagu ya share mata hawayen dake mata zarya,
Wayar hannunsa ya saka cikin hannunta ya dan ja gefe ya kama hannunta ya jata a hankali har inda Mu.azam yake ya saka hannun nata cikin na Mu.azam ya dan yi tsai sannan ya juya da wani mugun saurin da sai da ya gansa a waje shi kansa
Da sauri Mu.azam ya kama hannunta suka shiga taka matatakalar jirgi, wanda ya kasance hawanta ya farki, shigarta ta fari suka shiga
Kusa da Khadija ya zaunar da ita shi kuwa ya je kujerar bayansu , du yana haka ne kar Khadija ta kulace ahi, wanda shirunta ke damun nutsuwarsa
Share this
[ad_2]