BAK’A CE Page 31 to 40

Da ido ya nunawa Mu.azam ya fice fa,
Mu.azam ya turo baki ya bude motar ya fitar da kafa daya ya juyo fa haushi haushi ya ce” idan ka batawa abin kaunana rai , sai na tarar da wannan matar taka na nuna mata waye bos Mu.azam!
Wardugu dai bai ce da shi komai ba har ya fita a motar ya tsaya yana kallonta kafin ya bude mata gidan bayan ta shiga motar jikinta a sanyaye ta gyara hijabinta ta kai dubanta Wajen Wardugu,
Yana son magana da ita wanda zai fuskanceta, ya sani shi ya dace ya koma baya ko dan saboda gaban ana iya kallon su ta gaba du wanda zai fice, aman wani abu ya tsaya masa ya hana shi fita ya koma bayan motar,
Dakewa ya yi , ya ce” dawo gaba.
Agaishat dake duban gaban motar ta kai dubanta wajensa, a ranta fadi take” shi koda yaushe fuskarsa ba wani fara.a zai wani tantankewa yake yiwa mutane, to ni me na yi masa ?
A hankali ya dago da kansa ya juyo fuskarsa dan bai ji ta motsa dan bin umarninsa ba,
Kamar na dazu yanzun ma idannuwansu ne suka sarke da juna, a tare gabansu ya shiga luguden duka ,
Wannan karin Wardugu kasa cire idannuwansa ya yi a nata , tsai ya tsaya cikin kogin idannuwanta yana mai jinsa baki daya a cikin idon,
Da sauri Agaishat ta janye kwayoyin idannuwan nata a nasa ta shiga kokarin bude motar hannayenta na rawa baki daya tana neman nutsuwarta na neman gagararta,
Bude motar ta yi ta fita, shakar sansanyar iskar duniyar ta yi kafin ta juya da dukan kuzarinta ta bude gidan gaban ta shiga,
Shi kam binta kawai yake da kallon da bai ya kureta da shi har haka ba, sam bai san yanai mata kallon da ya fice ka.ida a adinnance ba,
A hankali ta ja ta rufe kofar, aman wannan karon ta gagara dubansa cikin ido kamar yanda shi ya tsareta da idannuwansa wa.inda ta rasa gane me yake kallo,
Zuciyarta ke ingizata da ta dube shi, domin bayan ta dawo gaban ma ya yi shiru ne bai ce da ita komai ba, hakan ya saka a hankali ta kuma buda dara daran idannuwanta cikin nasa,
Lumshe ido ya yi ya kuma budewa kan fuskarta, haka kawai ya ji baya iya yi mata magana tun karfi ko eani gatsai gatsai, ji yayi yana kokarin sanyaya muryarsa fiye da yanda yake yiwa kowa magana a duniya, girmanta, tausayinta ne ya ji a lokaci guda, yana jin kunyarta wace bai san ko ta meye ba, ya ajiye hakan kan dan tana abar kaunar amininsa, tabas zai ci gaba da jin haka a tare da ita balema idan ta aminta da zuciya daya zata kular masa da amininsa,
Sangartar da muryarsa ya ci, marainiya ta zama a makogwaron sa, da kyar ya iya sarafata wajen fadin” *Kina son sa? Zaki rayu da shi?*
Ajiyar zuciya ta sauke mai cike da ma.anoni, kanta ta sada a hankali ta ce” *shi ne zabina*
Furucinta da faduwar gabansa ba zai tantance wane ya fi wani karfi wajen saka jinnin jikinsa gudu a karfin da ya zarce yanda yake, kirjinsa ke duka da sauri sauri inda ya ji hankalinsa ya tashi, ya rasa menene haka? Me ke faruwa da shi,
Dakewa ya yi ya cire hular kansa yana dan alamun fifita da ita, bai daina kallon Agaishat ba, ya ce” zaki iya rayuwa da shi da zuciya daya? Ki so shi domin Allah? Zaki sadaukar da komai na rayuwarki wa shi?
Dagowa ta yi ta tsurawa fuskar Wardugu ido, a hankali ta ce” *ka damu da amininka ko ka damu da amanarka?*
Bai bata amsa ba, domin bai fahimceta ba, dan haka ta gyara zamanta ta ce” a gida, muna da Anna daya, du yaran gidan yan uwa ne, daga bakin ranar da Anna ta baiwa Ayya ni na zama yar Ayya, hakan na nufin ni kanwarka ce, baba tsofo yace idan iyaye ko yayu kai dangi baki daya zasu yiwa yarinya aure hankalinsu a tashe yake, su ne bincike kan waye mijin? Halaya da sauransu, su ne tabatarwa idan yarinyar na son sa ne domin Allah, kai dai a firgice suke,
Dan Allah, *zaka zama yayana?* mai saurare na? Mai share kukana kamar yanda yayuna ke yi?
Tunda ta fara labarin lebenta yake kallo tamkar mai koyon yaren da take magana da shi, a hankali ya ringa jinta a jikinsa har ta zagaye ilahirin jikinsa, wani irin nanauyan abu ya ringa ji wanda zaka ji shi ne idan kana son abu, ko dan uwanka ko wani na jikinka sosai , farat daya Wardugu ya ji ya yi kanwa daya kwalin kwal, jal, kwara , wace yake mararin samu, ya jima yana son samun kanwa daga mahaifiyarsa dan ya shagwabata , ya ririta ta, ya sangarta ta, ta fi yar shugaban kasa gata, a yau a yanzu ya aminta da bakuwarsu, ya ji ta zama jikinsu, zai iya cewa ya samu kanwa, zai kare mata duka cuta, zai iya yin fito na fito da koma waye kanta! Agaishat Agaishat kanwa ce a ransa wace yaje jinta tamkar jini daya suka fito,
Ji ya yi zai iya sakewa ya yi hira da ita irin ta dan uwantaka, lokaci daya ta shiga kokonta idan ya aura mata mu.azam ya kyauta mata kuwa? Nan da nan zuciyarsa ta kwabe shi ta hanyar tunasar da shi ai komai na Allah ne , .
A hankali ya dan jirga jikinsa bangarenta yana dubanta , ya dan saki fuskarsa ba laifi, dan karamin yatsarsa ya miko mata ya ce” zaki zama kanwata?
Murmushi mai hade da dariya da farin ciki ta dan yi masa ta ki bashi hannun sai alamu da ta nuna zata hade hannayen nasu ita da shi ,
Shima murmushi ya sakar mata yana mai nuna alamun dimple dinta har biyu sun shige sosai,
A hankali ta ce” yayana,
Duda suna ne wanda kowa ke fada, karamin suna, sai da ya ji dadin abin, ya amsa mata da ido,
Agaishatt ta ce” *ina son sa!*………………………………
I.m back????????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
????????????????????????????????
A hankali murmushin fuskar nasa ya bace, shima ya yi kalar serius ya ce” kina son sa? Zaki aure shi?
Agaishat ta dan kawar da kanta daga dubansa, ta ce” *eh zan aure shi,*
Ajiyar zuciya ya sauke ya wauga bangaren Mu.azam, ya ga yana zaune kasan wata bishiya yana dadana wayar hannunsa, dubansa ya dawo wajen Agaishat, ya dan jima kafin ya ce” *Zan aura maki shi*,
Agaishat bata ji wani yannayi na daban game da abinda wardugu ya fada kan aure da za.a yi mata, duda abu ne da take cike da murnar itama zata yi, aure da mutun kamar Mu.azam, itama zata yi rayuwar aure, aman zumudin da farin cikin ba wani can can ba , bata san dalili ba ko fargaba ne ya hanata jin madaukakin farin ciki kan lamarin?
Murmushi ta sakar masa ta kai dubanta wajen Acn motar da ya gama kashe mata gabobin jiki dan mugun sanyin sa,
Wardugu a hankali ya kai hannun sa wajen ky din motar zai kashe sai kuma ya bari, duban Agaishat ya yi ya ce” mu ga kitson yan matan Ayya?
Ai kuwa ya washe baki tana zabga murmushi cike da farin cikin irin yanda ya sauko daga hararanta ya mayar da ita mutun gashi har ya damu da kitsonta take dubansa tana kokarin jan hijabin baya ta bude masa kitson tana fadin” Alhinayett ne tace kar a yi min kananuwa dan kar na wahala sosai, ka san me, kuncewa yake yi fa, Ayya ne taki yarda na daina kitson nan, kuncewa yake yi shi kadai…..ta karashe tana dan turo bakinta irin na shagwababun yaren nan,
Murmushin da a yau ya kai sau hudu da ya yi du a gabanta ya kuma sakar mata yana duban kitson har ta rufe , bai san ta ina ba bai san lokacin ba sai ji ya yi ya ce” aa, ki yi ta yin kitson ki, yana yi maki kyau,