BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 31 to 40

Mu.azam na dubansa ya karaso ya zauna yana kara kare masa kallo, 

Wardugu ya ce” dan tausayi zaka aureta ko dan so domin Allah?

Mu.azam ya yatsina fuska ya ce” ina sonta mana, meye a tare da ita na tausayi? Nine ma ai abin a tausayawa,

Wardugu ya ce” kana ji, bana son ka yi auren nan da wata manufa, Mu.azam, ba zan jure gannin hawayenta ba koda kai ka jawo shi ranka zai bace, ka kara tunani !

Yana gama fada ya muke ya nufi bayi dan ji yake kamar ya yi ta ihu, sam baya jin dadin duniyar,

Yana kasan shower idannuwansa rintse, zuba take da karfin gaske ga ruwan sanyi karara da su, 

Idannuwansa da sukai ja ya bude ya barsu haka ruwan na shigar masa ido , hanunsa na dama ya jimke ya daki bangon yana wani irin nishi mai nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki, 

A kadan Wardugu ya kai minti arba.in a bayin nan sai da ya saisaita kansa ya kashe gudun showern ya dubi hannunsa da ya daki bango a kala sau uku wajen ya dan tashi abinka da farar fata, 

Towels ya dauka ya daure jikinsa ya fito ya nufi bed ya kwonta rigingine yana adu.a a cikin ransa

Da ido Mu.azan dake saman salaya ya bishi, kansa ya dukar ya ci gaba da jan carbinsa yana tunani barkatai a kasan zuciyarsa……….

          Bayan ta gama ibadarta , zuwa ta yi ta hada complet dinta biyu ta saka a jakar computerta, ta duba kudin dake jakarta , ta kuma duba wayarta da passport dinta ta koma bakin dan madaidaicin bed din da take kwana tun zuwanta ta dauki carbinta fari kar ya fito tana mai kuma kiran docter Elisabeth 

Dagawa ta yi suka gaisa, nan docter Khadija ta yi shiru,

Docter Elizabeth ta ce” kina ji, sati biyun nan shi dai kawai na iya sama maki domin kin ga aikinki ya kasance aiki mai daraja, bangaren zuciya bama so koda wasa masu kula da lamarin mu rasa daya koda na minti daya ne, na yi iya yina a haka aka tsaya, dan haka ki hanzarta zuwa niger din ki gama komai kafin likaci ya cika, ni dai fatana ki yi ki dawo da shi mu shiga aikinsa ,

Kanta kawai take gyadawa , bata san ya zasu kwashe da masoyin nata ba, ta so ta samu lokaci isashe sai dai hakan bai samu ba , zata je da wannan din ma Allah ya sa ya amince.

          *Timiya*

Tunda suka iso suka sauka wsjen baba tsoho suka fada masa abinda ke tafe da su,

Baba kam tsufa ya kara rufe shi, bawan Allah daga ringeshe yake binsu da kallonsa domin idannuwansa ramram suke ganni, murya irin na datijai ya ce” na ji dadi na yi farin ciki, aman me zai shaida min da gaskiyar maganarku? Ina mahaifiyar taku? Ina agaishat? Ina alwalin mai neman auren? menene shaidar da zata saka na aminta da ku?

Wardugu dake dubansa ya karaso a hankali kusa da shi, kai shi yanzu yana jin nauyin tsohon wanda a da nauyin bai kai haka ba, 

Yana karasawa ya kama hannun Baba tsoho cikin yaren buzanci ya ce” bamu zo da su ba, sai waya da na dauke su suna magana, mai neman auren Agaishat abokina ne , aminina, shine wannan , ya nuna Mu.azam, ya ci gaba da fadin” Allah ne shaidar mu, shi ne alwalin kansa, idan kuwa ni zaka baiwa amanar yarka zan dauka baba domin ina jinta tamkar kanwata ta jini,

Baba tsoho yana dubansa da wani yannayi, a lamarin Agaishat du idan ya yi istihara yakan hango wani duhu kafin ya ga haske, , dubansa yake ta kaiwa kan samarin biyu, Mu.azam da bai sani ba , da kuma Wardugu da ya zubawa ido, ya rasa me ya sa bai ji wani zumudi ba, 

Bashida ikon hanawa ko sakawa a lamarin agaishat duda shine silar zuwanta da mutanen nan, bai isa ya yanke hukunci ba, sannan idan ba zaka fadi alkhairi ba ka yi shiru, 

Shiru ya yi ya yi masu jagora inda suka talabe shi sosai suka shiga motar aka nufi gidan Ba

Zaune suka same shi kofar gida , ya tisa sansaninsa a gaba yana zaune kan tabarmar kaba yana ta gyara sansanin yana kukulewa da zaren daure abu yana kashi kashi , shi nan sana.a ce ya fara,

Da ido ya bisu har suka firfito infa ya hade rai yana hararar baba tsoho 

Daidai wannan lokacin suka karaso inda sukai masa salama, 

Wani kallon ya bisu da shi, yana tatare sansaninsa,

Wani uabn tsaki ya ja ya ce” ai ko ba.a birne gawarta ba sai na siyar da tabata , ka ga bakin ciki, du ranakun nan baku zo fada min ta mutu ba sai ranar da zan fara sana.a? Ni na san *Bak’a* bata son ci gabana, wato dan ubanta mutuwarma ba zata yi ba sai ranar da zan fara sana.a

Baki dayansu dubansa suke, wardugu da tunda gari ya waye jikinsa a mace yake bai iya ce masa komai ba sai sakin baba tsoho da ya yi wajen Mu.azam ya karasa saman tabarmar ya zauna ,

Hannunsa ya mika wajen sergent,

Da sauri ya karaso ya dire wata bakar jaka ya koma wajen da suke tsaitsaye,

Bude jakar Wardugu ya yi ya shiga fitar da daurin daurin kudi cefa yan jika goma goma yana direwa gaban Ba,

Du daurin nan million guda na cefa ne, sai da ya dire ashirin wanda zuwa lokacin Ba sai zufa yake jikinsa na rawa yana fitar da harshe tamkar kare shi ya ga kudi,

Wardugu ya ce” bata mutu ba, da ranta da lafiarta, aurenta zaka bamu, ga gudin auren nan idan kuwa sun yi kadan a karo! Domin *Darajarta* ta fi karfin a yi cinikinta! Ta fi karfin a aureta dan kudi, *Agaishat* na da daraja a idannuna! 

Gaba daya dubansa suke, magana ne yake daga zuciyarsa, fuskarsa ta nuna wani yannayi mai wuyar fasara, ba zai iya jure wulakancin Ba a wannan halin ba, sannan ba zai iya biye masa su yi ba dadi ba ko dan albarkacin haihuwar Agaishat da ya yi, 

Wani irin rawa jikinsa yake, auren bak’a da sadakin da ba.a taba bashi ba na sauran yayansa? 

Wani irin zama ya gyara yana fadin” ai kawai a matso a daura domin kuwa ya shirya, ba ruwansa da tambayar da wa za.a daura, ina take? Tana so? Ina zata zauna? Waima da ranta? 

Jiki na rawa Ba ya umarci baba tsofo ya yi alwalin Agaishat inda nan da nan sarki ya karaso da jama.ar anguwa ana ta yaba sadaki (kar abin ya baku mamaki ko ya girgiza ku, na gani da idanuwa sadakin buzuwa million arba.in na kudin nigeria bama niger ba, ana amsan karamin sadaki kamar jika hamsin aman yawanci auren garinmu kama daga agadez da kauyukan bugaje ana kashe kudi na mamaki wanda ba.a dauki hakan a matsayin laifi ko wani almubazaranci ba,),

A wannan rana , gaban duban shaidu, Mu.azam ya zama alwalin kansa inda Baba tsoho ya zama na agaishat, aka daura auren Mu.azam da Agaishat bisa sadaki mai tsoka lakadan, 

Sai bayan an gama daura aure Ba ya tatare kudin nan jiki na rawa ya zube a cikin rawaninsa ya daure, bai wani tsaya ya bi ta kansu ba ya yiwa gidan tsinke sai washe baki yake yana ihun kiran sunnan Anna inda ya yi fatali da sansanin,

Da amarya ya fara cin karo sai murkashi take ymtana rauda kai domin cikin nata mai matukar bata wahala ne, tana ta fama da kanta du ta lalace, 

Tsayuwa ya yi ya tofa mata yawu a fuska ya ce” ke kadarara, jeki na sake ki! 

Daidai lokacin da Anna ta fito tana dubansa sai kiranta yake yana kashe murya irin za.a tuna da din nan,

Yana karasowa ya ce” ashe *Agaishat alkhairi ce?*

Da mamaki take dubansa tana jiran karin bayani, Agaishat kuma? Ita tana tunanin rabonsa da ya kama sunnanna da daraja haka tun rada mata shi da ya yi, me ke faruwa? Ina yarta ? Innalilahi wa ina ilaihi raj.une, sam bata daukan fara.ar Ba a alkhairi, hakan ya sa ta fito da sauri ta yi waje ko zata ga Agaishat din

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button