BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 31 to 40

Sai da ya gama ya ce” ki daina kuka, yau nima na yi jajen abinda ke raina ne.

Alhinayett ta ce” me ka fada bayan komai a dunkuke ka fada Wardugu? Me ke damunka a ranka?

Tsai ya yi yana tambayar kansa takamaiman damuwarsa har haka? Kan matar wani ko me? Da sauri ya mike ya mikar da ita ya jata har kofar gidansu ya tura ya turata ya ce” asuba alkhairi Alhi……..,

A wannan rana Wardugu ya ga dare tamkar rana, ya kwana bautawa allah inda ya roke shi yafiya da nutsuwar zuciya, kuma alhamdulilah ya samu nutsuwar harma ya kwonta da safe bayan ya gama salar asuba ya samu baci

        Gidan Ayya,

Kallon Mu.azam take kafin ta ce” aa, toh shi wardugun ya aka yi baku zo tare ba? Mu.azam yaushe abokinka zai yi hankali? Ina wayar da na ce ku dauko min komai?

Sai a lokacin ya tina ya mike da sauri ya je dakinsa ya dauko wayar wajen Ayya da ta basu lale lale su dawo mata da dauka,

Yana zuwa ya kunna mata ya mika mata inda ta tsurawa komai ido tana kallo har karshe domin daya daga cikin yaran wardugu ya dauko komai, 

Baya ta maido kadan tana duban yannayin wardugu, 

Kanta ta dago da niyar yin magana ta hango Agaishat ta farka tana saukowa a hankali, kanta na duban kasa, hankalinta a yannayin tashe, kayan bacinta ne jikinta dogon wando sakake da riga budadiya, kitson kanta cikin hula baka, a hankali ta sauko ta dago idannuwanta ta sauke kan Ayya,

Kuka ta fashe da shi ta karasa da gudu jikin Ayya tana ta shesheka

Hankali tashe Ayya ke bubuga bayanta ta ce” me ke damun ki? Lafia? Y’ata menene?

Agaishat ta kankame jikin Ayya ta ce” Ayya, mugun mafarki na yi, wai wuta na cin gidanmu, Aya gobara a gidanmu, an yi an yi da Anna ta fito ta kiya tana jira sai Ba ya bata umarni domin bata fita sai da umarninsa , shi kuwa ya tsaya yana ta dariya ya ki bata umarnin!

Ayya tana shafa kanta ta ce” mafarki ne fa Agaishana, mafarki ne, ki kwontar da hankalinki, kin ga jiya su Wardugu sun je din , an gama komai kuma harma Mu.azam yace da sakonki da Annarki ta bayar a kawo maki,

Gabanta ne ya yanke ya fadi, an gama komai? Kennan yanzu ita ta zama matar aure? Ta zama matar wani? Ta zama sa yi hani bari? 

A hankali ta dago da dubanta ta kai wajen Mu.azam, 

Ido ta tsura masa kamar yanda ya tsura mata, 

Murmushi ya sakar mata yana dubanta kafin yake karasowa dan kusa da su kadan ya ce” Anna lafiarta kalau, hakama su Mariama, du sun fito mun gaisa, baba tsofo yace a gaishe ki, du suna nan kalau,

Maimakun ta bashi amsa sai ta mayar da kanta jikin Ayya ta lafe tamkar mage, sannan ta lumshe idannuwanta gamgam 

Da ido Ayya ta yi masa magana tana murmushi tana shafa kan Agaishat inda ya mike jiki ba karfi ya nufi tsakar gida.

Karfe shida na yama jirgi ya ajiye su, inda fito bakin titi ta tsaya tana kallon yanda motoci ke ficewa, 

Tsarin garin ya yi mata ba dati ga kyau.

Taxi ta tsayar, don ta san ba wanda ya kai dan taxi sannin gari, ta san garin akoy tsaro, sannan ta san da wuya a samu wanda bai sani ba,

Tana tsayar da shi ta ce” *Gidan Elhaj Wardugu Marahut nake so ka kai ni* 

Juyowa ya yi yana dubanta ya ce” gidan su ko gidansa?

Tsai ta yi ta tuna yace mata idan ya zo wajen Ayya yake sauka, fan haka ta ce ” *gidan sa* domin tana son fara magana da shi kafin ta je ga Mu.azam!

To fa fans, shin bata san walyn ba? Ya kuke hangen wannan cakwakiyar?

                Ga kari????

???????????? *BAK’A CE*????????????

Na *SAJIDA*

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

 ____________________________________

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

                        4️⃣6️⃣

Tafia mai nisa suka yi kafin ya dangana da tankamemen kofar gidan wardugu,

Kamar kowani gidan baban iko , kofar gidansa sojoji ne ke gadi wa.inda suka canji wasu,

Can gefe katuwar motarsu ce ta iko, sunna dan hira tsakanninsu lokaci zuwa lokaci kuma suna kule da aikinsu yanda ya kamata,

Tana sauka ta biya mai taxi ya juya inda ta nufi wajen sojojin .

Kamar yanda suke kallonta haka itama ke kallon su, har ta karasa dan kusa da su

Daya daga cikinsu ne ya yi mata tambayar wa take nema a nan?

Amsa ta bashi gamshashiya ta kuma nuna masa carte dinta shaidar ko ita wacece din,

Waya ya dauka ya yi kiran layin ogan, 

Ya jima yana ringin kafin ya daga,

Yana dagawa ya kora masa bayani,

Wardugu dake bacin gajiya ya bada umarnin a sayota a gwada mata part din Walyn su hadu a can.

Mikewa ya yi ya shiga wanka, bai wani jima ba ya fito da alwalarsa ya tayar da sallah ya yi ramuea domin wani nanauyan baci ne mai wahala sosai ya yi,

Yana gamawa ya bi ta dayar kofar ya fice dan nufan bangaren Walyn wace ya gama tunanin kar a je tana can tana zuba hauka!

Maradin Walyn baya kunya,

Yana tura kofarta ya tarar da bakuwar tsaye rike da jaka tana kallon kasa, jikinta da bakar abaya doguwa ta yane kanta da mayafin Abayar, 

Walyn kuwa na zaune saman kujera ta dora kafa daya kan daya tana kadawa ta turo daurin dan kwalinta gaba tana kaskaskas da cingan

Salama ya yi mata yana duban Walyn, kafin yake fadin bismillah zauna mana ga kujera,

A hankali ta karasa wajen da ya nuna mata ta zauna tana mai duban Walyn, 

Gaisawa suka yi cikin mutunta junna, kafin ya yi shiru yana sauraronta

Gyaran murya ta yi ta ce” Wardugu sunana Nana khadija Canel Noor, muna tare da Mu.azam ne a can wajen aikinsa inda yake aiki can muka hadu, akoy shakuwa tsakanina da shi mai girman gaske , na biyo…..

Bata kai ga karasa maganar ba walyn ta bushe da dariya tana dubanta,

Hannunta ta nuno mata ta ce” halan saurayinki ne?

Da mamaki take duban Walyn, ashe tana jin french? Da ta zo ba yanda bata yi ba Walyn ta fahimci maganarta aman ta juye yaren tubanci ta yi ta dura mata zagi da hannayenta kuwa ta nuna bata san yarenta ba, sannan ta daure fuska ta tsare gida ta jefa cingan a bakinta tana taunawa tana kada kafa tana chating.

Walyn bata yi kasa da gwuiwa ba ta ce” wace irin shakuwa ce tsakanin mace da namiji? Ke jiya fa aka daura masa aure, jiya suka je suka dauro aurensa,

Walyn! Wardugu ya fada da kakausar murya wace ta saka ta yi shiru tana binsa da kallo sai kikifta ido take uwa ta yi karya,

Kansa ya juya ya ce” ki je dakinki,

Baki ta turo gaba ta mike ta yi wata girgiza ta juya ta nufi dakinta tana rauda jiki ita matar general,

Tunda ta fadi maganar nan, jikin Khadija ya mutu, ta sada kanta kasa, hankalinta ya gama tashi, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shine abinda take ta fada a ranta, kuka take so ta yi aman ya ki zuwa, 

Wardugu da ya dago ya yi mata kallo daya ya kawar da kansa ya ce” desoler (Sorry),

Wani abin ta hadiye da kyar kafin ta ce” ko ka san da bashi da lafia? 

Wardugu ya rintse idannuwansa, ya gyada mata kai,

Ta tatara dukan kuzarinta ta ce” Wardugu, ana iya yi masa aiki, tabas aikin na da mugun hatsari aman idan Allah ya nufa sai ka ga an dace, ana tashi sosai, wa.inda nasu ya yi mugun tsanani ma sun tashi , ka taimakeni ka saka baki ya biyoni mu je a yi masa aikin nan, bana tunanin idan ya mace a haka zan iya wata rayuwa, Wardugu ka taimake ni,

Menene tsakaninki da shi mai girma haka? Excuse moi (excuse me), kina magana ne tamkar rayuwarsa na tafe da taki, na san ki, ya min maganarki a matsayin kawa, kawance ne ko da wata maganar? Wardugu ya fada , bai yi niyar yi mata wani kwakwaf ba, aman yannayinta ya tsorata shi, kar dai Mu.azan nada wata ya zo ya auri Agaishat? 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button