BAK’A CE Page 31 to 40

Khadija ta sada kanta kasa ta ce” ni ke binsa yana guje min, ya fada mij zai yi aure, kennan dai auren ya yi? Meye laifina dan Allah ya dora min soyayarsa? Bani da ja da aurensa, bani da damuwa da matarsa, ni dai burina a yi masa aikin nan, idan da rabo ya samu tsayin rai,
Mikewa Wardugu ya yi, ya dubu wajen Tv din Walyn, kys din motarta ya dauka ya yiwa Khadija alama da su je,
Mikewa ta yi itama gabanta na faduwa, bayansa ta bi tana tunanin ya zasu kwashe da Mu.azam? Ya zata tsinci kanta idan ta gane shi da wata? Adu.a kawai take a kasan zuciyarta, sannan miskilancin Wardugu ya sakata shiga tatayinta sosai,
Gudu yake na balaki, jalabiyar nan ta jikinsa baka wace ta mahaukacin haska fatar jikinsa itace a jikin nasa bai canza ba, sai gajeran wandondake kasa, daga su ko yannayin gashinsa bai caje ba, fuskarsa fayau da ita ta bada wani ni.imtacen kyau du kuwa da irin yanda ya hade ta.
Da garajen dai ya danna cikin gidan Ayya inda ya fito da tarin balaki ya nufi wajen mai gadi domin ya bar kofar a bude, (za.a dai sauke masa fushi ne)
Nemansa yake bai ganshi ba, hakan ya sa ya dawo wajen motar inda take tsaye tana duban ikon Allah,
Tun shigowarsu Mu.azam yake kallonsu, domin yana kasan inuwar tsakar gidan Ayya yana ta tunanin rashin gannin Wardugu da yanda Agaishat ta kaurace masa kwata kwata bai ga fara.arta ba, danma tun dazu Alhinayett ta zo wajenta. Baii ga fuskar Khadija ba domin ta dayan bangaren ta fito kuma ta ba inda yake baya sai lokacin da Wardugu ya karaso ya yi mata nuni da bayanta ba tare da yace da ita ci kanki ba
Juyawa ta yi, inda likaci daya Mu.azam ya mike tsaye yana zaro ido,
Da sauri ta nufi wajensa inda shima ya tako suka hade tsakiya suna yiwa juna wani kallo mai wuyar fasara,
Hannunsa ya kai fuskarta ya shiga share mata hawayen da suka fara zaryo mata a fuskarta suna masu yiwa juna murmushi…..
Alhinayett ce ta fara fitowa, inda hankalinta ke kan Agaishat dake biye da ita suna hira harda dariya domin Agaishat ce ke fadin” ashe itama zata ga ranar da za.a ce ta yi saurayi wai harda aure? Ashe yan birni ba haka suke ba? A kauye bata taba tunanin ko mahaukacin kauye zai kulata ba,
Dif ta yi da maganar inda idannuwanta suka sauka kan Mu.azam da wata kyakyawar mata fara kar , jikinsu tamkar zai hade, sannan sai shafa fuskarta yake kamar mai rarashinta,,
Sanye Agaishat take da atampa an yi mata dinkin riga da sket, dinkin zamani ne ya mugun karbar jikinta ga dauri da Ayya da kanta ta caka mata mai shegen kyau,
Fuskarta ba wata kwaliya sai dan jan baki mai ruwan atampar sai annurin amarci domin amarya ko ta daji ce tana fita daban,
Sosai take fitar da kamshi mai nutsar da zuciya, annuri na fita a fuskarta, idan ta yi murmushi kuwa kaima zaka tsinci kanka da yi ne dan irin murmushinsu ke saka murmushi,
Idannuwanta dara dara da su sun sha kwali, dogon hancinta ya sauka kusa da dan madaidaicin bakinta mai lebe masu santsi da kyali domin kida yaushe tana amfani da rob san gyaran bushewar lebe da saka su laushi da kyali,
A hankali ya dora hannayensa duka biyu saman motar ya dora kansa ya tsura mata ido,
Wani abin ya fargar da shi inda ya yi saurin watsakewa ya juya da sauri ya nufi wajen garden,
Sai a lokacin Mu.azam ya ankara da su Agaishat, shi din ma gabansa ne ya fadi, inda har ya ji kafarsa na dan rawa, aman ya dake ya kama hannun Khadija suka suka nufi wajen su Agaishat……..
????????
???????????? *BAK’A CE*????????????
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4️⃣7️⃣
Yana karasawa ya dan fara kame kame yana dan susar kai, da kyar ya iya sakin murmushi yana duban Agaishat ya ce” wife, ga Khadija, khadija ga matata.
Kanta ta juyo daga duban su Agaishat ta sauke kwayar idannuwanta cikin nasa, wanda ya ki bari su hada idon ya kawar da nasa wajen Agasihat wace itama su kawai take kallo inda ta ji wani irin faduwar gaba,
Khadija ta yi iya yinta ta karasa kusa da Agaishat da Alhinayett ta mika masu hannu tana sakin murmushin yake ta ce” asalamu alaikum,
Hannu Alhinayett ta fara bata tana mai amsa salamarta suka gaisa, hakama Agaishat wace Khadija ta ji hannunta wani irin laushi (toh ba dole ba, tunda ta zo Ayya ke tsaye kan du wata gaba ta jikinta , jiki kuwa na samun gyara nan da nan yake hadewa ya yi cas), ta yi mamakin irin kaushin hannunta duda ta tarar da ita a gidan su Wardugu,
Daga nan dugunzuma suka yi cikin falon Ayya inda Agaishat ta haye dan kanta ke sara mata, ita ta kasa gane wacece kuma tare da mijin da aka aura mata jiya? Sai a lokacin ta mike zaune daga saman bed dinta ta nufi wajen window ta daga labule dan gannin ina ya je? Ina ya tafi ne? Ta ganshi harma sun yi ido hudu inda ta yi masa murmushi shi kuwa ya hade fuska, daga nan bata san ina ya nufa ba, aman motarsa na nan wajen hakan na nufin yana gidan.
Tunda ya je ya ja ya tsaya waje guda yana duban yanda lambun yake da irin sanyayan sanyin dake tashi a ciki ya afka tunani, tambaya daya ya yiwa kansa wace ta saka kansa sarawa, idannuwansa ya lumshe ya dubi hannunsa a ransa ya shiga yiwa kansa fada kamar haka” ba kanka farau ba, da yawa sun rasa sun ci gaba da rayuwa, dole ya girgizaka domin kaima mutun ne mai rai da lafia mai zuciya mai motsi, aman kuna yarda da wannan jarabawa zai kara daukaka darajarka a wajen ubangijinka, kai ba kowa bane face dan adam da Allah subahanahu wata ala kan jarabta a rayuwar yau da kulun, dan ka shiga hali na jarabawar rayuwa ka aminta shine cika namiji,
Murmushi mai ciwo ya yi a fili ya ce” Wardugu, ? Kana bata time dinka bayan wannan baya cikin tsarin rayuwarka! ……..
Zai ci gaba da yiwa kansa magana yar wayar da baima yi tunanin ya dauko ba ta dauki tsuwa a hankali tana kidan nan na sojoji tamkar ana harba bindiga,
Shiru ya yi da maganar ya tamke fuska bai dauki wayar ba , bai kuma ci gaba da magangannun da yake ba,
Ya kai sau biyar ana kiran wayar dan haka ya saka hannunsa ya cirota ya duba sunnan,
WALYN,
Dagawa ya yi ya kara a kunnensa yana sauraro,
Asalamu alaikum General, docter Sagir Sulaiman ne, an kawo matarka emergency minti sha biyar da suka shige ne, yanzu da muka dan daidaita lamarin ne ta bamu wayar dan mu yi kiranka,
A dake ya ce” wani asibiti?
Likitan ya ce” dan clinique dan gawo ne domin a inda ta samu hatsarin nan ne mafi kusanci da ita.
Katse kiran ya yi bai bashi amsa ba ya saka hannunsa cikin gashin kansa ya yamutsa ,
Juyawa ya yi da tafiyarsa mai kama da yana sauri aman a gadarance ya nufi cikin gidansu wajen Ayya,
Tunda ya nufo wajen ta tsura masa ido, kallonsa take tana murmushin da bata san na meye ba,
Dan yatsanta ta nuna inda yake zuwa ta ce” ban taba gannin mutun mai rihima irin dan Ayya ba, ya san kan rigima, ko dan Allah ya bashi dama ne? Wannan mutumen idan kokowa ta hadaka da shi ba zan so ganninka a karshe ba,
Dan bakinta ta murguda ta ce” ke Agaishat kin manta karfi daga zuciya ne?