BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

Ina son na rayu War, ina son na rayu na haihu nima na ga yarana sun girma, sai dai ban san ba ko zan samu haka? 

Magangannun suka fadowa Wardugu a rai,

Idannuwansa ya rintse suka kara rikidewa sukai wani ja mai duhu! 

Wani lokaci sun je kauye mai sunna Matamai nan yankin damagaran kusa da nigeria ya ga yanda garin keda ni.ima, tsarin rayuwar garin ta mugun birge shi inda ya nace sai da suka kara kwanaki kan wa.inda sukai niyar yi,

Suna lambu ne cikin garin sansayar iska na kada su yace” ka san Wani abu Wardugu?, duda an ce mutun idan ya mutu halayensa ke binsa, khairin ko sharin gwargwadon aikinsa gwargwadon kabarinsa, aman zan so na mutu a garinnan ni.imar garin ta yi min ,

Wardugu ya daki kafadarsa ya ce” sai kace wani saudiya? Kai fa haka kake motsi kadan mutuwa motsi kadan mutuwa, du inda ta zo fatan shine a cika da imani,

Ji yake jikinsa na yi masa nauyi, zuciyarsa ta cinkushe,

Wayarsa ke kuka kamar ta fasa aljihun wandonsa ta fito aman kunnayensa basa ji, 

A fili ya ce” ya zaka bar wasiyoyinnan a kaina Mu.azam? Wa ya fada maka ni inada karfin zuciyar da zan iya saka hannu a takardar da zata bada damar a cire maka damar shakar numfashi ka tafi na dindindin? Wa ya fada maka cewar ni inada karfin da zan iya daukan gawarka na kaita inda zan kaita? Kai wama ya fada maka cewar ni din zan jure gannin an rufa maka dara? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,! 

Wayarsa ya lalubo jikinsa na wani irin kadawa , zafi kuwa ya dume masa jiki baki daya ya danna numbobin da bai yi tunanin idan an daga zai samu mutumen ba,

Da asalamu alaikum aka amsa wayar,

Wardugu ya ce” Mu.azam ne yace wai na saka hannu a takardar cire masa oxygene,

Shiru ya yi , inda hankalinsa ya tashi, murya a dan rikice ya ce” kana ina? Kuna ina?

Wardugu ya amsa da ” muna paris, muna ma.aikatar Mu.azam, Mu.azam ya ki tashi! 

Mikewa ya yi daga zaunen da yake , da hannunsa ya yiwa abokinsa alama da ya tafi ya fice ya nufi aeroport dan gannin ko zai samu jirgin da zai sada shi da Paris a yau yau, inda hali a yanzu????

                       ????

Wa Wardugu ya yi kira,?

MU.azam ya tafi kennan?

Agaishat, Khafija, Wardugu????????????????????????????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          5️⃣7️⃣

Tafia ta manya ce ya yi, in ba dan manyan ba daga shi sai suturar jikinsa sai cart dinsa ta banki, da ita ya ciri tiket, ya zauna yan mintuna inda jirgi ya daga da su, da ita ya ciri kudi ya yi shatar taxi ta kai shi asibiti

A kofar asibitin aka hana shi shiga, domin dare ya ratsa har wajen karfe biyun dare,

Ba yanda bai yi ba, da kwatance da komai aman masu tsaron kofar suka kiya dan su basu sanshi ba, gashi mushulmi, su kam aa yama bar masu kofar asibiti

Gashi bai san numbersa na garin ba, 

Waje ya samu dan nesa da asibitin ya shiga kai kawo, dare ne ba damar ya sayi wata wayar du an rufe, gashi ba wata takarda ya zo da ita ba ko tiket ciran kudi muraran ya yi masa sun san shi a yanda yake da yawo kasashe ya shige abinsa idan ya so ya san yanda zai yi,

Kansa ya shafa a lokacin da ya tuno da whatsupp, duda ya san abune mai wuya wai ya duba whatsupp , aman sai ya shiga ya aniya kiran number Wardugu baya dagawa,

Ya yi masa kira ya fi a kirga, dan haka ya nemi guri ya zauna hankali kwonce dan waje ne mai tsaro, kuma da garaje ba za.a kama mutun ba duda suna da tsarguwa da musulmi suna tsoron yan jihad,

Daga nesa yake hangen tafiyarsa, da kyar yake daga kafarsa, 

Ido ya tsura masa, daga ina yake? 

Wani tausayinsa ne ya lulube shi, dan kuwa Wardugu in dai hankalinsa a tashe toh baya zama, zai yi ta yawo ne a kafa, idan wani abin fada ne ya hada shi da wani toh a hanyar yawon nan nasa kan mai tsautsayi zai kare ne,

Aman yanzu yana hangensa a wani yannayi na rashin karfi, har ya karaso inda yake zaune,

Dama Wardugu na hangensa, tun zuwansa har artabun da suka sha da masu tsaron asibitin da kiran da ya yi ta faman yi,

Yana zuwa tsaye ya yi gabansa yana dubansa,

 A nitse ya mike shima yana dubansa, 

Hannu ya mika masa da nufin su yi musabaha,

Wardugu ya miko masa nasa hannun shima, nan ya ji wani irin zafi hannun nasa,

Hankali tashe ya ce” aman Wardugu me kake yi haka? Yau ka fara yin rashi ne ko yau ka fara shiga tashin hankali mai tsanani? Ka tina wannan lamari gaban wanda baka da ikon motsi, jan numfashi sai ya umarta ne, kaima lokacinka na nan tafe, dan kulu nafsin za.ikatul maut,

Ba wanda ya isa, ba wanda zai iya, ba wanda zai yi in ba shi ba, kar ka manta ya rasa iyayensa a lokacin da yake saurayi, ya karba da hannu bibiyu ya rayu a cikin duniyarnan mai cike da rudani, 

Idan Allah ya karbe mana shi a yau sai mu yi masa biyaya , mutuwa ta zama rigar kowa, mutuwa mai yankan kauna ne, mutuwa ba ruwanta da baba ko yaro, itace mai dauke uwa a lokacin da ta sako dan jariri, itace mai dauke jariri daga hannun mahaifiyarsa ta mika shi a kaishi wajen wanda ya fita son sa, mutuwa mai raba miji da mata, ta raba abokai, ita ba inda bata ratsawa da lokaci ya yi ya dauka ta yi gaba abinta, a halin arziki ko talauci, birni ko kauye,

Ka yiwa amininka gata mafi girma wato adu.a da kyakyawan sutura,

Wardugu ya zube kasa nan wajen kasa zaune, 

Bakinsa na rawa dan ciro magana , da kyar ya iya samu bakin ya bude masa ya ce” ya ya ya bar wasiyun da sukai min tsauri da yawa, *MARAHUT* na tsinci kaina a halin da bana iya aiwatar da komai, karfin ikon Allah dole na karba, na kasa kuka, na kasa saka hannun, ana min ikirarin ni jarumi ne? Na gwada jarumta ta hanyar sadaukar masa da abinda nake so a nan gidan duniya aman yau an wayi gari na kasa daukan jarumtar saka hannu a bakar takardar da za.a cire masa abin numfashi, 

Marahut ya zauna shima kusa da shi ya daga kansa sama ya ce” kalu *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE*, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une…….

Haka Murahut ya yi ta maimaita masa har shima ya karba sukai ta yi , sukai ta yi , sukai ta yi,

Can Wardugu ya shiga ajiye zuciya, a hankali ya dora kansa saman kafadar Murahuttt,

Murahutt ya yi shiru na dan Lokaci kafin ya ce” ka san cirewar ko shi ne samun rahama a gare shi? Idan ka yi duba da musulunci ya zo mana da idan mutun ya rasu a yi gagawar yi masa sutura?

Shin wace hikima ce a boye a nan? Allah baya abu kawai, 

Idanfa an jima da zare ransa kune ke gannin yana numfashi? Idanda gawar ce kwonce kuke kallo? 

Wardugu ya rintse idannuwansa da karfi ya ce” mai yiwuwa kuma likacin ya buda idannuwan nasa ne basu yi ba?

Kennan dai ba zaka hakura ba ? Marahut ya tambaye shi,

Wardugu ya ce” bani da karfi, ban isa na ja ba,

Marahut ya gyada kai, sukai shiru su duka 

Can Marahut ya ce” ina Agaishat?

Wardugu ya dago da sauri ya dubi Marahut, shi sai yanzu suka fado masa a ransa, mikewa ya yi zurbat ya yi gaba da sauri inda Marahut ya bishi da kallo, bai yi wani gigin binsa ba dan tuni ya yi nisa a tafiar sai ido da ya zuba masa har aka barshi ya shiga asibitin,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button