BAK’A CE Page 41 to 50

Yana shiga ya zarce wajen da ya tabata suna nan wato wajen dakin Mu.azam,
Bayin Allah sun dunkule waje guda sun rufa da hijabin Agaishat sai sauke ajiyar zuciya suke su duka,
Tausayinsu ya kara karyar masa da zuciya, tun ranar da Khadija ta je gidansa ya gama gane ba wai kawance ne kawai ya hada su da Mu.azam ba, duda ya ga irin yanda Agaishatma ke son Mu.azam din, aman yayi imanin da wuya in ta kai khadijar dan kuwa Khadija ta jima a soyayarsa, wa.innan bayin Allahn biyu su ne marayu kan rasuwar Mu.azam, shi kuwa ya rasa amini, aboki, dan uwan shawara, dan uwa na jini
A hankali ya raba su ya nufi wajen hangen Mu.azam din,
Ja ya yi ya tsaya ya tsura masa ido, irin kallon nan na kurullah,
Idannuwansa ya lumshe yana kada kai, dan kuwa idonsa nuna masa yake ya motsa yatsarsa manuniya,
Da yake kafafuwansa rufe suke da bargo ba.a gannin motsinsu, sai da ya kara motsa yatsar nan, a hankali fatar idonsa ta dan fara rawa, bugawar zuciyarsa ya fara karuwa kan na da da ya yi kasa sosai ya yi nisa,
A hankali bugawar zuciyar ke dan karuwa wanda ya saka injin dake sasarkafe jikinsa suka kwashi kuka,
Zabura Wardugu ya yi ya kara kurawa Mu.azam ido,
Tun karfinsa ya ce” MU.AZAM, MU.AZAM, MU.AZAM!
Ba.a jin komai daga ciki, sai su Agaishat ne suka mike a firgice, daidai nan likita ya shigo da gudu ana biye da shi ana taya shi daura rigar aikinsa da safar hannu da na rufe hanci,
Wata na tura abinda ke dauke da kayan aiki,
Ai kuwa sai gasu suna ta bilowa da gudu gudu , nanfa aka shiga kokowar fitar da su Wardugu daga nan din ma ,
Da kyar aka fitar da su waje inda du suka haukace sai tambaya suke jefo masa wai ya farka ne ? Farkawa ya yi ne?
Wardugu kam bai iya amsawa ba sai kai kawo yake yana kama sunnayen Allah a zuciyarsa , baya so ya amsa masu dan bazai so ya basu espoir kuma abin ya kasance ba haka ba,
A kadan sun dauki minti arba.in, lokaci lokaci zaka ga wani ya fito da gudu ya nufi can wajen dakin kayan aiki ya dawo da wani abin da gudu ya shige, koda sun tarye shi baya bada amsa har suka hakura suka dawo bin mutane da kallo. ( ya Allah ka jikan mama da gafara, wannan ciwo da ya kaita Allah ka sa bakin wahalarta kennan alfarmar annabi muhamadu sallalahu alaihi wa salam)
Ba su su gama kimtsa komai ba sai da aka dauki wajen awa da minti talatin kafin kake gannin sun fara fitowa suna tafia makwoncinsu,
Su kam sun zama tamkar mararsa wayo,
Can sai ga docter Rogger da Elizabeth sun fito,
Murmushi kwonce saman fuskarsu,
Hannu suka shiga mikawa su Wardugu, harda Agaishat dake binsu da kallo aman ta kasa karbar hannun ko daya dan ta kagauta ta ji halin da yake ciki
Wani murmushi ne Wardugu ya saki, wanda gaba daya hakoransa suka bayana,
Da sauri ya juya ya nufi bayi dan dauro alwallah, domin lokacin nafilfilu bai shige ba, tabas zai raya wannan dare wajen godewa Allah,
Khadija ta rungume Agaishat tana murna ga hawaye na malala a idannuwanta ta ce ” Agaishat, ya farka, kuma ya yi kyakyawan farkawa, dan ya gane su su duka, yanzu an ce a barshi ya huta zuwa safe mu shiga mu ganshi, Agaishat *Mu.azam dinmu ya farka*
Agaishat ta saki murmushi itama ta ce” Alhamdulilah, Allah mun gode maka, Allah ka bashi lafia mai anfani
Da amen take amsawa,
A haka Wardugu ya fito da tapis a hannunsa ya saci kallonsu kadan ya sauke ajiyar zuciya ya fice a asibitin,
Inda ya barshi nan ya same shi,
Goron ruwa ya mika masa bai masa magana ba ya samu waje ya shinfida dardumar ya tayar da sallah,
A sujadarsa ta karshe, Wardugu ya jima yanaiwa Allah kirari, ya gode masa bila adadin,
Bai tashi daga saman salayarsa ba sai da rana ta fara fitowa, dadaykun mutanen da suke fitowa motsa jiki na safe har sun fara tsayawa daga nesa suna kallon su Wardugu suna mamakin musulmai ne suna masu sallah a wuri,
Bai wani damu ba sai da ya gama jan carbinsa ya shafa fatiyarsa , ya kai dubansa wajen Mahaifinsa,
Fuska ya hade ya yi kicin kicin da fuska ya ce” ya farka a jiya,
Marahutt ya ce” na gane tun jiyan a yannayinka,
Wardugu ya dan tabe baki ya mike ya dauke abin salayar ya kai dubansa wajen asibitin ya ga an bude an fara shiga, dubansa ya kai wajen Marahutt ,
Kafin ya yi magana Marahut ya ce” na san hanya
Kansa ya juyar ya ajiye salayar nan kusa da mahaifin nasa ya juya yana neman taxi dan ba zai koma ciki daukan mota ba gaskiya.
Hotel ya je ya saka kaya masu sauki ya shiga fakin gymnastic ya motsa jikinsa sosai ,
Dawowa ya yi ya yi wanka da ruwa masu sanyi karara ya fito ya saka kaya ya fesa turare ya dauki kys ya bude dakin ya sauka , nan ya karbi kayan da ya yi order ya shige taxi din dan ya mayar da shi asibiti
Yana zuwa ya shige ,
Nan ya gansu zaune Marahutt na kusa da su suna hira jifa jifa inda Agaishat ta bada hankalinta suna hira dan sosai yake sake mata gashi yana kiranta da yarsa, hakan ya saka take son datijon da gannin girmansa
Wardugu na shigowa idannuwansu suka sarke ita da shi,
Wata harara ya sakar mata kafin ya dauke kansa,
Kamar yanda ya saba ya mikawa kowa nasa harda Marahutt,
Karban dai yan matan suka yi aman ba wada ta kai niyar ci,
Bai takurawa kowa ba, ya dai bude ya dan tataba nasa dan a jiya da azumi ya wuni banda bakin ruwa ba abinda ya sha,
Wajen karfe tara likita ta zo da kayan pensement, shiga ta yi ta yi masa ta fito,
Wajen karfe goma docter Rogger ya zo ya shiga ya bashi abincin da ya dace ya ci,
Bayan ya fito ne ya ce” da bibiyu zaku shiga, kuma kar ku yi masa hayaniya da yawa, kar ku saka shi magana, kar ku nuna yannayin damuwa a fuskarku a gabansa,
Zamu kara rike shi na dan lokaci har mu kare yi masa pensement sai mu sake shi, Docter khadija ki zo ki karbi takardunsa baki daya ki kawowa Wardugu,
Musabaha sukai da Wardugu kafin Khadija ta bi bayansa tana faman ta yi ta dawo ta shiga,
Wardugu ne yad dawo daga rakiyar doctern ya nufi dakin da niyar shiga
Marahut ya ce” Wardugu, ka shiga da matarsa mana?
Ja ya yi ya tsaya , a hankali ya waiwayo, da hannunsa ya yi mata nuni da ta shiga,
Da sauri ta mike ta tafi ta kama kofar a hankali ta tura ta shiga inda wardugu ke biye da ita a bayanta,
Tunda suka shigo ya tsura masu ido gabansa ya fadi, kunyarsu ya jo ta lulube shi, wato dai a duniya bashi da gatan da ya fi Wardugu da ahalinsa, ya san yanzu zai ji haushinsa a yanzu, aman ya tabata daga baya idan ya ji dalilinsa, zai fi kowa murnar hakan
Murmushi ne shinfide a fuskarsu har suka karasa kusa da bed din da yake kwonce,
A hankali Wardugu ya karasa kusa da shi ya dan rage tsayinsa,
Hannunsa ya kama ya damke musabaha da nuna farin ciki,
Agaishat dake tsaye ta zagaya dayan gefen ta taho kamar zata kwonto gefensa,
Ido ya zaro yana dubanta, hannunsa ya dago yana son tsayar da ita,
Ja ta yi ta tsaya tana sakar masa murmushi,
Tsoro ne ya kama shi, me hakan ke nufi? Jikinsa ne zata hau?
A hankali ya kai dubansa wajen Wardugu, duda yana halin rashin lafia, duda ya tabata A wannan lokacin wardugun na cikin farin ciki, aman abin ya daure masa kai,
Murya ciki ciki ya samu a hankali ya ce ” War, bababaka ga message dina ba?
Wardugu ya ce” sakon wasiyoyin har a wayar ka turo min ko? Allah ya shirye ka.
Mu.azam kam kasa cewa komai ya yi, ya sakar masu murmushi shima, a haka har suka gama ganninsa sukai masa salama da fadin sai kuma shigar gobe dan sau daya tak zasuna leka shi,