BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 41 to 50

A firgice ba tare da ta tuna da wani rufe kanta ba ta fito da gudu gudu ta zo ta bude dakin

Bata shirya ba, bata san zata ji ba, kai batama san wai hakan zai faru ba sai jin saukar wani fitinanen, gigitacen hautsinanan mari da ta yi imanin da bata yi fitsari kafin ta yi shirin kwonciya ba da ta sake shi ba wani ja.

Jinta da ganninta ne suka dauke na wani dan lokaci kafin take samu su dawo, a tsorace ta shiga ja da baya jikinta ya kwashi bari tana dubansa ba tare da ta yi masa magana ba, Khadijama a tsorace take biye da bayansa tana mai dora hannu a kai da fadin” Wardugu?

Wardugu da har jikinsa ke rawa shima na bacin rai ya ce” ashe ya sake ki kike zaune a gidansa? Wannan wani irin natacen so kike masa da har zai sake ki , ki ci gaba da zama a gidansa kina shan ruwan gidansa? Tir tir tir da wannan zuciyar Agaishat sai yaushe zaki fadi cewar ya sake ki? Ko jira kike ya dawo ki lalabe shi ki bashi hakuri ya mayar da ke? Tambayarki nake kike kallona tamkar kin samu sabuwar halita? 

Bakinta na rawa tana kankame jikinta dan har lokacin marin na ratsata, sannan wani mahaukacin tsoronsa ne ya diro mata wanda bata taba ji ba, a yanda ya zo bata taba ganninsa daga shi sai yar rigarnan ba, ga abin bacin rai gaba daya wani yannayi nasa dake boye sai ya bayanna, kirar jikinsa, jijiyoyin jikinsa, gashin kansa ba a nitse ba aman a waje guda sama saman ne ya tatashi, 

Bakinta na bari ta ce” ban ban gane me kake nufi ba Ya Wardugu, ban gane me kake cewa ba, wa aka saka? Me me 

La ferme Agaishat, (churup Agaishat) ki min shiru kar ki fada min karya a nan, bai baki takardar saki ba? Ko don son da kike masa zaki ki gwadawa ne? Na tashi na je gidanku mahaifiyarki ta damkan amana gashi ba.a je ko.ina ba har na ci? Ina takardar da ya baki tun kafin na karya ki gida biyu!?

Zubewa ta yi kan gwuiwoyinta ta hade hannayenta inda tuni kuka ya kece mata, tana kukan ta ce” sai nake jin kana nufin kamar mijina ya sake ni? Ya sake ni? Me na masa? Yaushema aka yi auren da har ya mayar da ni karamar bazawara? Wani umarninsa na taka? Sannan ni dake zaune a gidansa ban san da ya sake ni ba? Har aka tafi da shi asibiti *yana shigowa har dakina*,

Ido Wardugu ya rintse tare da shiga wani tashin hankalin, yana shiga dakinta? (Kalma mai fasara biyu), 

Katseta ya yi ta hanyar fadin” bai baki takarda fara ba?

Kai take girgiza cikin yannayin firgici kafin ta tsaya tsak, 

Mikewa ta yi da gudu ta fada dakinta ta bude akwatinta ta ciro takardar da ta adanawa Mu.azam wace a iya sanninta da shi ita kadai ce takardar da ta taba wani hada su,

Jiki na bari, tana jin kamar ta kifa ta karaso ta mikawa Wardugu takardar inda ya bude ya karanta, 

Tsaf takardar saki ce Mu.azan ya dankarawa yarinyar da suka dauka suka wanke suka bashi, a cikin kasar da bata san kowa ba sai shi, a lokacin da ta shaku da shi, sai wata yar takardar a hade da dayar inda ya rubuta” Agaishat, ki yafe min, ina son ki ba dan bana sonki ba, sai dai hakan da na yi shi ban yi kai tsaye ba. *Ina son ki*,

Dubansa ya kawo kan Agaishat dake tsaye tana jiran karin bayani daga nesa kadan da shi , sai khadija dake kukan gannin rashin dacewar abinda Mu.azam yayi duda kuwa da hakan na iya mata dadi da a lokacin da bata san su waye Wardugu a rayuwar Mu.azam ba, aman a yanzu da ta ga waye Wardugu, ta kuma ga irin halacinsa sai ta ji ta shiga wani yannayi na rashin jin dadin abinda abin kaunarta ya aikata, duba da irin yanda ran Wardugun ya baci sai hankalinta ya kara tashi, 

Murya dake ya ce” fice mu tafi,

Ido ta zaro tana dubansa kafin ta shiga yarfe hannu, murya na rawa ta ce” ina son sa, ina son mijina, ka hashi hakuri ya maidani dakina, ba zan kuma yin abinda na yi ya sakenin ba, ba zan yi ba, Wardugu daga aure sai a sake ni? Me Anna zata ce? Me baba sofo zai ce? Ya zasu yarda da wannan abin? Wardugu ina son sa,

Wardugu ya dan saki hanya ya nuna mata hanya fuskarnan a hade tamkar ya shaketa haka yake ji, dan rashin sannin ciwon kai wai a bashi hakuri, 

Da sauri ta ratsashi ta fice tana waiwayen Khadija dake son ta baiwa Wardugu hakuri aman tana tsoro,

Itama murya na rawa ta ce” Wardugu toh bari na dauko mata hijabinta fan Allah, kafin na je na same shi asibitin,

Ja ya yi ya tsaya, juyowa ya yi yana dubanta kafin ya ce” *Tana da gata fa, itama yar dangi ce, ko bata da kowa a duniya tana da ni, idan kin je asibiti wajen masoyinki! Ki fada masa na gode! Na juya nigeria zan dawo gannin jikinsa in sha Allah, zancen hijab ki bar shi, wannan suturar ta jikintama zan dawo da ita, na haramta mata du wani abinda zai fito daga hannunsa komai kankantarsa! Mu.azam da Ni Wardugu yake magana!*

Haka ya tafi ya bar Khadija tsaye cikin tashin hankali ya shiga motar ya jata a tsoyace yana tukin irin na dazu inda Agaishat ta hade kanta da gwuiwarta ta afka duniyar tashin hankalin da ya fi na kulun, wai ita Agaishat har namiji ya nuna mata hali tun ba.a je ko.ina ba? Ita Agaishat, itace aka dankarawa sakin da ba laifi? Ita agaishat itace zaune a gidan kato da sakinsa a kanta tana wadaga tamkar gidan ubanta? A yau ta karasa yin tir da rashin ilimi, a yau ta ji duniyar ta fice mata a rai, a yanzu da aka ce ya saketa ta ji wani kaunarsa ita kuwa, ta shiga tsaka mai wuya ga Wardugu yaki koda kallonta bale ya nuna mata wani yannayi na tausayawa, ya tafi a bacin ran irin wulakancin da Mu.azam ya yi masa da tunanin yanda zasu kwashe da Ayya, 

………bai koma hotel ba sai da ya je ya samu takardar komawa Niger ta mutun biyu kafin ya juya Hotel da ita!

                   Timiya

Tafiar su Anna tafia ce mai nawa, domin dai ana fitowa daga cikin Timiya saman rakumi ne, gashi Anna sai da ta dauko baba tsofo du kuwa da irin yanda ya kiya aman fir itama ta kiya sai da shi ya saka aka yi dabara aka dora shi amale tun yana tsugune , maza hudu suka tatare har amalen ya mike kafin suma sauran su hau nasu su kama hanya,

Tafia ce mai tsayi idan ba.a gagawa, tafiar sahara ga tarin yan rakia da guzurinsu, dan jariri kuwa a nade a cikin tufafi mai laushi a jikin Anna rata yi masa goyon gaba,

Ana tafiar ne ana tsayawa a baiwa baba Tsofo abinci da ruwa hakan ya sa suka wuni cir kafin su shigo gari 

Dogarai ne suka juya dabrakuman inda su kuwa suka dauki motar sarki daya kwal mai baya bude suka nufi garin Agadez

Ba su su shiga garin ba sai da isha ta yi, suna zuwa direct gidan sarkin suka je 

Bayan an sauko daga salar isha.in ya kara ganawa da sarki, wanda ya bukaci gannin Anna,

Anna na shiga Sarki ya mike yana dubanta, kamar gatanan a fili ta mahaifiyarta, mace mai mutunci da mutunta mutane,

Ba bata lokaci ya hada vidio call da aminin nasa,

Dagawa ya yi yana mai saka gilashinsa na karin gani yana fadin” Sarkin agadez da kansa

Sarki ya amsa yana murmushi mai kayatarwa kafin ya hasko masa Anna dake tsaye 

A zabure ya mike tsaye yana mai……

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button