BAK’A CE Page 41 to 50

A hankali ya karkata dubansa wajen Khadija inda Docter Rogger ya raba ya fice, sauran docters din suka shiga bata hannu sunai mata murnar an samu nasarar aikin ciki sai fatan ya farka daga dogon barcin da aka luluka shi wanda farkawar shi ne zai shaida aiki ya yi ko bai yi ba wanda a kala zai iya kai sati biyun idan komai ya je daidai ko sama da haka abinda ba.a fata , sannan aka bata abinda aka cire a cikin kan , du suna yi suna nuna itace matarsa suna tayata murna wardugu na tsaye a wajen kuma da yarwn French ne ba abinda baya ji
Dubanta dai kawai yake uwa ya samu tv, ita kuwa ta ki yarda su hada ido da shi ko su samu zama daga ita sai shi,
Tana gannin likitocin samu tafi ta dan dubo shi a yannayin daburce ta ce” zan zan je na karbo takardun,
Bai bata amsa ba har ta bacewa ganninsa tana sauri tamkar zata fadi,
Juyawa ya yi yana kallon Agaishat da itama tunda suka nufi wajen likitocin take kallon su, bata san abinda ake ciki ba, bata iya yaren su ba, sai ta zama bakon Tv, dan dukan idannuwanta ta bude tana bin kowa da kallo ko zata fahimci wani abin,
Yana nan tsaye yana hangenta yana tunanin me zai ce mata Khadija ta dawo ,
Kanta take dan sosawa irin na mai laifi wand Wardugu ya gama karantarta watsi ne ya yi da lamarin da baya son shiga abinda bai shafe shi ba,
Rakardun ta mika masa ta shiga masa bayani kamar haka” kasancewarsa ma.aikacin asibitin nan wanda suka dauka da kansu yake karkashinsu zai biya rabin kudin aikin wanda ya kama millions 3 da dari takwas, sai riko gado kulawa shima tabin kudin ne ya kama jika dari bakwai namu na cefa,
Sai takardun magungunna da za.a ringa karbo masa a nan cikin pharmacy na asibitin shima yanzu zan je na karbo takardar da zata bamu damar biyan rabin kudadan magungunnan du zamuna karbowa ,
Sai da ta gama yi masa bayannin du yana karbar takardun kafin take miko masa carte din Mu.azam da kuma tata ta banki ta ce” ga carte din mu na banki, ga takarda mai dauke da code din mu wato reference din mu, idan aka hada na mu biyun na tabata kudin zasu isa har a salame mu,
Da yake du bayannan nan da take idannuwanta basa kallonsa dan mugun kwarjini yake mata sai da ta ji bai karbi takardar da carte din ba ta dago da dubanta a hankali ta dube shi,
Fuskarsa ya yatsina ya juya ya barta nan tsaye da takardar da kuma carte din, aman ya karbi baki daya na asibiti da za.a biya, na magungunnan,
Tana nan tsaye tana kallon sa ya fice ya tafi infa Agaishat ta bishi da kallo,
Kanta ta daga sama ta lumshe idannuwanta, a yau ta ji wani irin takaicin da bata ji ba na rashin karatun zamani da basu samu ba, ta zama tamkar kurma marar wayo a cikin mutane, bata gane yaren su , sun zame mata sababin mutane sun zame mata sabin halitu, gashi wanda ya kawota kasar take zaune dominsa kansa ake bayani aman bata san komai ba, yau kam ta yarda da maganar Ayya inda take ce mata” Agaishat, ban ki maganar baba tsofo fannin karatun zamani ba, aman ina son ki sani a rayuwa komai yana da anfani, karatun adini, karatun bokon ne , neman sani kan abubuwa ne, shi dan adam ana so ya zama mai yawan bincike kan lamarin zaman yau da gobe, neman ilimi ba laifi bane, jahilci baban ciwo ne wanda bashi da magani, idan aka ce jahilci kuwa ba ana nufin mutun jahili ba, ana nufin abinda baka sani ba yake a cikin duhu gareka .
Idannuwanta ta dan bude gannin Khadija ta koma wajenta na da ta zauna, bata ko nemi zuwa wajen da Agaishat take ba bare ta kwatanta mata wani abin,
Tabas hasashen Agaishat ya gama tabata a kan Khadijar da mijinta,
Dan ka fito daga birni, baka yi karatun boko ba, ba ana nufin kai din wawa sakarai bane, kana hankalce da komai, hasalima ka fi wasu yan birnin lura da gane lamura a kallo kawai bama sai an fada maka ba,
Ji ta yi an shiga hakkinta da yawa, ji ta yi ba.a mata adalci ba, zuciyarta ke ingizata da ta mike ta tarar da khadijan ta fada mata ta gane soyaya suke da mijinta, aman tana so ta fada mata halin da yake ciki, ko ba komai a tunaninta kusancinta da shi zai fi da kowa duba da itace matarsa, wada ya dace ta zama sirinsa, aman sai ya kasance itace wace bata san komai game da shi ba, wata zuciyar ta ce” ki ce da ita me? Wato ke mai hayagaga ko? To dan ya mayar da ke baya cikin komai nasa sai me? Me kika sani , ina kika sani, me zaki iya yi masa a cikin lamarin? Ke ko a kauye kin zama koma baya cikin y’ayan Ba bale a birni, birni mai abin mamaki, birni mai mota mai jirgi mai kalolin fata? Birni mai madafi a daki? Birni mai tv mai abin allo? Ke kama kanki a hakama ya isa, ki saka ido ki yi adu.a, ki godewa Allah hakama ai ci gaba ne!
Idannuwanta ta yiwa wal wal wal irin ta harari kantan nan, ta dafe gaban goshinta da hannunta na hagu sannan ta dafe daidai zuciyarta da hannunta na dama, ji take zuciyarta na doka mata da sauri, takan shiga irin yannayin nan idan tana cikin yannayi na tsoro,
Ya kai minti talatin da fita kafin yake dawowa shi da wasu mutane biyu , dayan ya girmanta dayan kuwa shima saurayi ne mai jini a jika,
Su duka hannayensu da wasu manyan takardu masu dauke da tambarin asibitin wa.inda a cikinsu ne aka zuba magungunnan da take a way,
Karba ya ringa yi yana ajiyewa kusa da khadija ba tare da ya yi mata magana ba,
Sai da ya gama ajiye komai ya dawo wajensu suka yi magana ,
Khadija dai na kallon su inda Agaishat ta kawar da dubanta daga bangaren kowa kawai ta sada kanta tana mai dana carbinta,
Sara masa suka yi kafin su yi musabaha , kys din motar saurayin ya mikawa Wardugu yana mai nuni da takardun motar da komai a ciki kafin su juya, ashe yaransa ne dake zaune a kasar da sunnan Niger.
Kys din ya saka a aljihun wandonsa, ya dawo wajen Khadija dake kallonsa tana sarawa girmansa harma ya fi yanda Mu.azam ke fada mata, lale Wardugu ya nema kuma ya samu, rikeken hamshaki ne da baya nunawa ko yinkaho sai dai ka dube shi kawai ka gane nitsatsen hamshaki ne,
Takardun shaidar ya biya komai ya mika mata, a gajarce a kuma dunkule ya ce” an gama da wannan , sai na gaba.
Take a way din ya duka ya dauki takarda biyu ya bar mata guda ya juya ya nufi wajen Agaishat,
Yana zuwa Ya tsaya ya ce” mu je,
Maganarsa kawai ta ji saman kanta, dan haka ta dago da sauri, sai ganninsa ta yi saman kanta fuskarnan a hade,
Mu je? Mu je ina? An salame mu ne? To ina Mu.azam din?
Tambayoyin da ta yi ta jerawan kanta kennan ,
Gannin bafa mai amsa mata gareta ba sai ta mike tana leken Khadija dake kallon su , tana so ta yi mata magana aman Wardugu ya tsare wajen dama gidan baki daya, dan haka ta juya sumui sumui ta fara fita a wajen kafin yake daga kafa ya shiga gabanta
Sai da suka fito harabar asibitin wajen motocin dake parke ya ciro ky din ya danna dan command din dan gannin wacece motar?
Motar da ta yi kara dan amsa kiran da akai mata ya tsurawa ido yana dan shafa gefen fuskarsa, aman lale comandan Munkaila ya raina masa wayo, wannan motar ta samari wanda suma idan zasu shan iska suke hawa ne ya bashi? Gaske da ya tambayeshi marque dinta ya ki fadi ,
Kansa ya girgiza, shi ba shiba yake ji, yarinyar nan zata iya zama cikinta? Bata da sama , gaba daya saman a bude yake gashi garin ana yannayi na sanyi ,
Zuwa ya yi ya bude ya shiga inda ya waiwayo gannin Agaishat bata biyo bayansa ba,