BAK’A CE Page 41 to 50

Da ido ya yi mata nuni me take jira? Dan haka ta karaso tana kallon inda zata bude ta shiga, ita bata taba gannin kalar mitar bama dan ba wani yawo aka kaita ba, yar fitar da suka yi daga gida zuwa asibiti kuwa hankalinta a tashe batama kalli garin ba bale ta san me ke zuwa da zowa,
Bude mata ya yi daga ciki ta shiga ta zauna tana gyara hijabinta da kyau,
Tayar da motar ya yi ya dauki hanyar gidan Mu.azam dan ya san gidan kuma bai ji yace da shi ya kaura daga nan ba,
Ita dai kanta a kasa dan ji take iska ta yi mata yawa, aman da ta sada kan sai ta ji sauki sauki,
Tuki wardugu yake yana tunanin abubuwa da yawa da ya ganni kan zuwansa zuwa yanzu,
Ko yanzu sai da ya koma wajen docter Rogger ya nuna masa komai tsarin a tsanake ya kwatanta masa inda za.a mayar da shi da kuma bashi takardar da ko a wani lokaci ya zo zai iya shiga kansa tsaye
Yana tunanin nan har ya karaso kofar gidan nasu,
Fita ya yi itama ta fito tana biye da shi ya dana ya bude suka shiga,
Ita dai kallonsa take har ya je ya daga wani katon peau na flower ya dauko ky ya zo ya bude mata,
Tsaye ya yi har ta zo ta shiga, sai kuma ya mika mata take a way din guda wato rabonta ya juya da niyar tafia,
Agaishat ta yi kundunbala da tsoronta da komai ta ce” shi fa?
Birki ya ja, a hankali ya dan juyo yana mai cire gilas din da ya mayar ya yi mata kallo daya jal,
Mayar da gilas din ya yi ya saka ya juya bai bata amsa ba ya fice a gidan,
Abincin ta saki nan ta juya da sauri ta karasa wajen kujera ta zauna kasa ta hada kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka, da yaren buzance take fadin” wayo Annata, wayo baba sofona, wayo Ayyata ku zo ku dauke ni, bana so, bana son auren, shi auren haka yake? Wayo zuciyana ciwo yake,
Bata ji motsi ba, sai karan ajiye kys da ta ji dan haka ta dago a tsorace
Shi ta ganni da abincin nata ,
Bai ce da ita komai ba ya je ya dauko plat da spoon ya darwaye ya zo ya bude ya fitar da abincin ya bude ya juye cikin plat din,
Zuwa ya yi inda take zaune shima ya zauna ya ajiye mata abincin kusa da ita, sai da ya yi da gaske kafin ya iya fadin” ki yi hakuri, an masa aikin kuma in sha Allah zai warke ya dawo gida,
To ka kai ni wajen shi Wardugu , Agaishat ta fada tana hade hannayenta,
Wannan karron kam ba kallo daya ya yi mata ba, tsai ya yi da idannuwansa kan fuskarta,
Hannunsa ya sa ya shafa goshinsa da kyau kafin ya ce” ki yi hakuri zai dawo kin ji?
Da kai ta amsa shi , ya nuna mata abincin,
Dauka ta yi ta shiga ci a hankali tamkar tana cin magani,
Wardugu ya yi ajiyar zuciya har ta gama ya mike ya ce da ita” zo ki rufe ba.a barin gida a bude kin ji? Idan kin rufe ki samu ki yi wanka ki huta zan dawo na kai ki ki ga Mu.azam,
Da to ta amsa shi da alamar murna, dan kam so take ta ganshi, ta yi missing dinsa fiye da tunanin mai karatu a dan lokacin da bata ganshi ba, sabo tirken wawa, Agaishat kam ta kamu da son mijinta, tana son abinta,
Haka Wardugu ya fice a gidan Agaishat ta rufe ta cire hijabinta ta nufi dakinta,
Tana shiga ta je wajen gadonta ta dauke matasan kan dake ajiye ta yaye abin shinfidar ,
Nan takarda ta fado wace in ba zata manta ba tun lokacin da Mu.azam ya raka Khadija ya dawo a lokacin da ya janyo abin rufa zai rufawa Agaishat ya saka mata kasan matashinta wanda ya san ta ganni , bayan ya saka din ne ya dubeta ya furta kalmar “Ki yafe min”,
Gannin takardar ta fado ne ta je ta dauke duda ba wata baba bace ta kai wajen shafe shafenta ta ajiye tana fadin” bawan Allah ya mance *Takardarsa* ko ajiya ne ya bani? Bara na kara kilaceta,
Dan haka ta dauke daga nan ta kai cikin akwatinta ta saka ta dawo ta canza zannin gadon ta canza na jikin pilow din ta kwashe wa.infa ta cirw ta yi bayi dan wankewa, dan kuwa sam bata wani kai kaya wajen tara kayan dati, ita ke wanke abinta da kanta.
*Takarda kuma?*
Yawan comment samun wani page ehe????????????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
5️⃣5️⃣
Wardugu na fita hotel din da aka kama masa ya nufa,
Yana zuwa ya fiya ya baiwa mai gyara mota ky ya yi gaba ba tare da ya dau komai ba,
Mai gyara motar nan ya gama gyarawa ya ciro komai a motar ya mikawa masu shigar da kaya hotel din,
Sai fa aka yi scaning din jakar kafin a dora saman abin turawa a nufi guichet, nan suka fada masa dakin da Wardugu ya sauka ya tafi kai masa
Daidai wannan lokacin Wardugu na zaune ya lumshe idannuwansa saman kujerar dakin hotel din fara kar ,
Mikewa ya yi ya bude ya karbi jakar , nan wanda ya haudo masa kayan ya mika masa wani album mai dauke da hotunnan yan mata kala daban daban , na kasashe daban daban ciki harda hausa girls, cikin shiga na tsiraici suna tala , idan mutun na so zai zabi wace ta yi masa da farashinta da numberta ya danna kira ta amsa kiransa (????)
Jefar da album din ya yi ya nufi bayi bayan ya danna kira katon butik din hotel din ya yi order kaya da siz dinsa da coler
Wanka ya yi kamar zai canza fata dan rabonsa da yi tun jiya da dare,
Ya dauro alwallah dan gabatar da sallar magarib
A nitse ya kamala komai ya saka kayan da aka kawo masa kannanun kaya ne masu tsari na manyan mutane, kalar baki ne dai sai chemise din ta ciki fara kar da cravate .
Agogo ya daura a tsintsiyar hannunsa ya fesa turare ya dauki katuwar wayarsa dan sai a lokacinma ya kula da waya,
Ayya ya fara kira , wada kamar jira take ta daga, tun kafin su gaisa ta jejefo masa tambayoyi,
Murmushi ya yi ya kora mata bayani cikin girmamawa da shagwaba irin na dan shagwaba a wajen mamansa,
Murmushi ta saki jin Alhamdulilah, ta yi adu.ar Allah ya tashe shi lafia, ta ce” ya yarinyata? Ta warware? Ta kara jiki? Ta yi kyau? Tana da wani abu ne? Hankalinta kwonce? Tana samun kulawa ne?
Tsai ya yi ya ciro wayar daga kunnensa ya tsurawa sunnan ido, Ayya, Ayya, kai ya girgiza ya mayar a kunnensa ya ce” idan na hadu da ita sai na baki ita Ayya ku yi maganar ko?
Ayya ta ce” kai wardugu bana son wulakanci , an gaya maka bama waya ne? Muna waya da ita aman kulun sai tace wai lafiarta kalau komai kalau, aman yanzu kai da ka je ba sai ka fada mani ba? Tana da wani abu ne?
Wardugu ya ce” wai menene wani Abu kuma?
Ayya ta ce” kai, baka san wani abu ba? Ina nufin an samu karuwa ne?
Kansa ya dafe , shi fa bai san me take nufi ba, dan haka ya ce” Ayya zan yi kiran ki , zan je wajen Mu.azam din,
Bai jira amsarta ba ya kashe kiran yana sauke ajiyar zuciya, toh shi yaushe zai tsaya kallon ta yi kyau ko wani abin? Shi inama ruwansa da kurewa matar mutane kallo????.
Kira a whatsupp masu yawa inda yarinyar nan wato *BASMA* kiranta ya fi a kirga, ga na Walyn da messages dayawa, ga na abokan aiki da mutanen arziki,
Wa.inda ya dace ya maidawa ya shiga ya maidawa, wa.inda ba lale sai a lokacin zai maida masu ba kuwa ya bari sai ya zauna ya jefa wayar a aljihu ya fice
Garin dare ne aman kamar rana, haske ne ko.ina, wasu a lokacinma suke dawowa daga gudun motsa jiki, wasu na yawon kafa da iyalansu, kowa dai na sha.aninsa ba wanda ke kula da sabgar wani,