BAK’A CE Page 51 to 60

Jida ta nuna mata cinyar Agaishat ta ce” ina ziga shayi ne ashe ta kawo hannunta ni kuwa na juyo shine ya zubun mata a nan,
Alhinayett ta aniya janye lafayar bayan ta dungure kan Jidda tana fadan ke komai zaki yi ba zaki yi shi hankali kwonce ba sai da katsamniya tamkar wata saniya?
Agaishat kam zufa ce ta ji a goshinta inda idonta ke rintse, dan Walahi bata ji zuwan abin ba sai zubarsa ta ji saman cinyarta , gashi ya gama tafasa kennan ga zafin shayi, ji take gaba dayama kamar kafar ce ta tsoma cikin ruwan zafi
Wardugu dake zaune bai san lokacin da ya rintse ido ba jin abinda ya faru, kokowa ya shiga yi da zuciyarsa da tunaninsa kan kar ya mike, kar ya je, kar ya je, ga kururuwar kanwar Alhinayett din nan dake kara caza masa kwakwaluwa, a hankali ya lalubi hanki yana kokari goge fuskarsa da bai san me zai goge ba wayarsa ta shiga kuka,
Lalubar wayar ya yi da sauri ya daga kiran baima tsaya gannin waye ba,
Walyn dake tuka mota ta ce ” Wardugu, gamu mun fito daga gidan su Alhinayett din an ce wai ba can take ba, ina ne gidan da take mu je?
Wardugu ya shiga yi mata kwatancen gidan kafin yake datse kiran ya tsurawa yatsotsin Agaishat ido domin Alhinayett ta kawota wajen tabarmar ta zaunar da ita da kyar ta samu ta bude wajen ta saka a kawo mata ruwan gishiri ta shiga tofa mata adu.a,
A hankali idannuwansa lumshe yake kallon yatsutsan kafar nata, dogayen yatsutsan kafa gareta, wa.inda suka kawatu da faratuna masu dan tsayi farare kar kar aman can samansu da dan jan lale, kafarta ta dama na dauke da dan karamin yatsa irin shidanin nan, sai yan kananun gashi dake saman kowace yatsa luflufluf da su,
Tsikar jikinsa ne ya ji ta tashi a hankali yake kokarin kawar da kansa sai dai ruwan gushirin da Alhinayett ta zuba mata ya saka ta jimke hannun Alhinayett da hannunta guda sannan ta kawo dayan hannun wajen kafar nata mai shidanin ta damki kafar ta cije lebenta kafin take kifa kan nata saman kirjin Alhinayett ta shiga sauke ajiyar zuciya,
Zabura ya yi ya karbe kofin ruwan giahirin kafin ya zabgawa Jida wata uwar hararar da ta sakata juyawa sumui sumui ta bar wajen ta koma wajen gashinsu a ranta tana ayanna kumurci!
Tsayuwa ya yi a kansu wanda ya saka Alhinayett dagowa tana dubansa,
Murmushi ta saki kafin ta girgiza kai a ranta tana ayanna zan ga gudun ruwanka gide, in sha Allah yar buzuwa ba zata bika ba kamar yanda sauran yan matanka ke binka, da yardar Allah zaka kawo kanka ne,
A hankali ya duka ya ci fuaka ya kai hannunsa ya daga wajen da ta kone din,
Wajen ba wani tashi ya yi ba aman ya yi duhu alamun jini ya kwonta,
A rayuwarsa ya ga ciwon da ya fi wannan girma, shi kansa a jikinsa ya ji mugun ciwon da ya fi wannan dan har harbinsa an taba yi,
Maganar zubuwar ruwan zafi kuwa idannuwansa sun ga abinda da za.a maimaita a yanzu ba zai iya fayacewa ba,
Sai dai abin mamaki wannan dan ciwo da ta ji ya ji hankalinsa ya yi mugun tashi, bai san lokacin da bakinsa ya buda ya dubi Alhinayett kan wada ya ji haushin tunda ya shigo gaisuwa daya kwal ta yi masa bata wani zo inda yake ba ta kara gaishe shi ba, ya ji bakinsa na fadin” mu kaita asibiti alhi
Alhinayett ta dube shi da mamaki, zata bashi amsa wayarsa ta kara daukan kuka,
Mikewa ya yi ya daga yana cusa hannunsa cikin sumar kansa ya amsa kiran,
Eh kawai yace kafin yake datse kiran ya juyo da dubansa wajensu inda ya sauko da gilas dinsa ya rufe jajayen idannuwansa wa.ina a yanzu ne suka dauki jan, labarin zuciyarsa ne ke isarwa gare su
Fitowa suka yi daga motar, ita da aminiyarta yar gidan gwomna matar minister,
Kowace ka duba sai ka kara duba domin tun daga suturun jikinsu zuwa kalar fatarsu da irin adon fuskarsu da takalman kafafuwansu da jakunkunnan hanayensu da irin kanshin da suke bazawa zaka gane manya ne ,
Fuska Walyn ta yatsina tana duban kawarta kafin suke bushewa da daria,
Kawar ta ce” wai ke da yarinyar yar gidan talakawa dangin talakawa ce har haka? Ke da Alhinayett din basu da komai a gari har kike tada hankalinki kar a je budurwar Oga ce?
Walyn ta yatsina fuska kafin take bushewa da daria ta ce” ba zaki gane ba, na rasa wani irin abu ne tsakaninsu, aman yau mu shiga mu keta mata rashin mutunci yar gidan taki zama!
Tafawa suka yi suka nufi yar kofar gidan da niyar shiga su shikawa Alhinayett rashin mutunci da ikirarin ta rasa wardugu sai dai yaransa (han)????
Wayo azumi na matsowa, ni kam kamar nace da ku da sai mun hade in da ranmu bayan azumi????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣3️⃣
Ya jima kafin yake cewa” ni babu wani madaukakin bambanci da nake nunawa a tsakaninsu, abu daya dai na sani idan sako ne zuwa wajena fada du wace ya kasance dole sai na ji a lokacin da nake zaune da talakawa sai an bi ta kanta, wannan kuma dalilina shi ne, zata shigo min da nutsuwa koda kuwa sakon mai firgitarwa ne,
Abu na biyu, sababin suturuna na ajiye a wajenta, dan ita ke kilace min ta yi masu wajen da ba mai zuwa sai ni,
Sai idan zan yi bakin kunya, ita ke girkinsu dan ta iya girkin sannan takan sako mini a kwanon da ba zan ji kunya ba
Ni kam iya abubuwan da zan iya tinawa kennan, sai wa.inda a rashin sani ne,
Hatimi ta gyada kanta ta ce” wa ke saya masu kwanoni? Shin kai ne? Idan kai ne kana saya kowace iri guda?
Ka taba baiwa wata cikinsu ajiyar kayan aka bata? Ka nuna mata dalilin da zai sa zaka kwashe bata kula ba?
Sai maganar tarar da kai wajen taronka da talakawan garinka, shin watansu ta taba zuwar maka a hargitse ne? Ta tayar maka da hankali? Ka zaunar da su ka nuna masu ga yanda kake so su kasance idan zasu je wajenka basu kiyaye ba?
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce” kwanoni ni ke sayan masu du idan na shiga birni,
Nasu na bacewa ne da wuri sai su ce wai yara ke lalatawa, kuma ba ruwansu ba zasu nemi gyarawa ba idan na yi bakon sai dai na ga wani abin tashin hankali cikin har hada min marfi ake daban da kwano,
Sannan gaskiya ban taba zaunar da su na fasa masu su kilace min suturuna ba, a ganina irin girman miji a gurin matarsa har sai na fada masu haka? Da girmansu da komai? Ita ai ba fada mata na yi ba,
Sannan a gaskiya sau biyu aka yi irin ina cikin mutane, idan abin kuka ne za.a shigo mini da gudu jiki fata fata a ja a tsaya an ci damara a gwaza kuka ana jijiga , har sai na yi rarashi da roko kafin a gwaza min abinda ke faruwa, hakan ya saka na soke tarar da ni fada ,
Murmushi ta yi ta ce ” ka yi hakuri mai martaba, mace du girmanta idan ta takarkare ta tafka maka wani abin wani lokacin sai ka yi mamaki,
Kar yannayin da Gaishata ke nunawa na kimtsi ya saka ka tunanin ita kadai xe kimtsatsiya a cikin matanta ko mai tarbiya, idan fa tana haka ne dan bata fara haihuwa ba?
Yau da gobe ai sai Allah, dole rayuwar yau da kulun sai ana tarowa ana gargadi, ana uzuri, ana nuna hanya, ana nuna bacin rai a abu kafin ka ga dan daidai,