BAK’A CE Page 51 to 60

Kar ka yi mamaki idan nace da kai dan daidai, domin daidai fa sai Allah, ita mace a karkace take, wata barazana ke tsoratar da ita , wata sai an nuna mata jan wuya, wata yar a bi a laluma ce, aman du miji a gidansa kafin ya zama laushi sai ya zama tauri,
Nufina a nan shi ne, kai mai mata uku reras a jere, dole sai ka cire maganar so a ranka ka kamanta adalci
Kar ka ga kamar sun nuna basu damu ba, sun damu fiye da tunaninka, kuma shirunsu halaka ne a wajenka a lahira, don kuwa idan a nan ka fi karfinsu na zasu iya yi maka komai ba a lahira fa? Kuma ba zasu taba jituwa da wada ka fifita a kansu ba,
Dole ka kwatanta zaunar da su lokaci zuwa lokaci, kanai masu nasiha, wace ta taka dokarka ko wacece ka hukuntata daidai tsarin adinni, idan ka ga lamarin zuwa wajenka sun kasa daidaitawa ka soke zuwan , koda wani irin abin ne a yi hakurin zuwanka,
Numfasawa ta yi ta dubi mijinta da ya mike da jariri a hannunsa dan ya fara dan kuka ta maido dubanta wajensa ta ce ” ka yi hakuri, ina barar ka duba shawarwarina,
Murmushi ya yi yana gyada kai, shi fa wly du abubuwan sun shige masa ba wai dan bai sani ba , aa , sai irin yanda cikuluftun shara.ar mutanen garinma kadai ta ishe shi, gashi ita din irin yanda ta kasance mai masa biyaya daga bayan nan, hakan ya saka du ya watsar da wani ya zasu ji ko me suke tunani da hukuncinsa yake yanke abinsa , tabas yanzu ya yarda da laifinsa a irin zaman doya da man jan da ake a gidansa, .
Bayan wata uku
Taro ne na jama.a, datijai ne , bakake da fararan buzaye an cika kofar gidan yau asabar wajen karfe shida na yama,
Sojoji makil suna zazaune kan fafaran kujerun da aka jejera du yawanci da kayansu na aiki domin wasu daga aikin suke wasu kiwa zasu hau suka biyo wajen karbar sadakin abokin nasu,
Can kusan kofar gidan kuwa sun dukufa wakilan ango da amarya ana zantawa kafin ake miko jimgin kudin sadakin da ya baiwa jama.a da yawa mamaki, ba.a taba ji ba, yau aka fara, sadakin farar buzuwa haka?
Domin ana miko kudin mahaifin amaryar ya juyo wajen Wardugu da jimkin kudin a hannunsa , dan dukawa ya yi kusan kunnensa ya yi masa magana, inda Wardugu ya shiga gyada kai yana jinjinna girman datijon a ransa,
Kudi na mamaki har million goma ne suka zo da su a matsayin sadakin wannan zukekiyar yarinya sai dai mahaifinta ya katse masu hanzari ta hanyar irgar jika hamsin ya cire ya mika masu sauran kafin yake fadin” Allah ya saka masu Albarka, wannan ya isa sadakin *Alhinayett*, kaya ka yi mata abinda ka ga dama aman iya sadakin y’ayana kennan,
Du wajen sun yi mamaki inda suke bin datijon da kallo kafin a shiga shaidar an karbi sadaki,
Uzurinsu na bukatar a yi auren da wuri suka kawo inda mahaifin Alhinayett ya nuna in sha Allah ba damuwa dan haka a nan ya yanke ranar aure wata guda danma ya aan ba zasu rasa dan shirshiryensu na mata ba da me zai yi jira? Shi daman baya so a saka auren yaro ya jima yana yawo da sadakin wani a kansa, kayan daki kuwa in sha Allah ba zasu gagara ba domin mahaifin Alhinayett ba wani hamshakin mai kudi bane, yana nema alhamdulilah yana samu sosai.
A wannan lokacin aka karbi sadakin mai neman auren Alhinayett wato colonel Aba gana bisa sadaki jika Hamsin , inda aka saka aure nan da Wata guda.
Wardugu ne tsaye kan lamarin nan, ba wani washe baki yake yana babaga dariya ba, aman du wanda ya sanshi idan ya ga fuskarsa zai gane yana cikin farin ciki,
Bai samu ya dan zauna ba sai da mutane suka watse , inda mahaifin Alhinayett da yan uwansa sukai ta saka masa albarka kafin yake shiga motarsa ya nufi gidan da suke yana mitar wai dan za.a kawowa mutun sadaki sai ya bar gida?
Kamar yanda ya yi tunani hakan ne,
Alhinayett bata da wasu kawaye, sai abokanannan aiki wa.inda bata fada masu ba tace sai aure zasu ji,
Tsakar gida suka shinfida tabarma gidan kanwar matar Abansu ce mai suna Fatima zahra suka je,
Gefe sun jika zobo sun saka masa kankara suna yi suna kurba,
Gefe guda kuwa nama ne suka yanyanka suka tsitsira a tsinke Agaishat ta yi garwashi suka dora gashi saman abin gashin auntyn nasu ,
Redio ne kanwarta mai suna Sajida wato jida ta kuna sai shayin da ta dora masu wanda yake dahuwa a yar tukunyar shayi,
Su takwas ne, su uku nr zaune saman tabarmar inda Alhinayet ta sha lafaya fara kar , Sajida ta saka doguwar riga blue wace kadan ta fi gwuiwarta , Agaishat ma lafaya ta dora kan doguwar rigarta wace itama bata kai har kasa ba sannan ta dan kama jikinta ta yi mata kyau mai ruwan ja, suna zuwa suka cire lafayar suka shiga shagalinsu suna dan taba rawar buzaye domin sun saka guitar ne a redion yana tashi,
Gefe kuwa yan matan ne wa.inda kanun Alhinayett ne suma suna ta raharsu suna casunsu dan kowa murna yake domin Alhinayett ba ruwanta da wani bambaci tsakaninsu, tana taimakawa kowa da abinda Allah ya hore mata, ba ruwanta da kai kararsu, idan abin ta fada maka gaskiya ya kama zata dubeka ta fada maka sai dai idan ka gama fushin ku dawo ku shirya,
Jida wato sajida ce ta dubeta a lokacin da take ziga shayi ta ce” Aunty, wai ke ina kawayenki ne?
Agaishat dake juya naman dake saman abin gashi ta juyo itama da yaren buzanci ta ce” ba gamu ba?
Alhinayett ta girgiza kanta tana duban message din Aba tana murmushi,
Jida ta ajiye zugar shayin ta nufin Wajen Agaishat ta dan duka irin yanda Agaishat din ta yi , ta saka hannunta tana gyarawa Agaishat gashinta dake zubo mata yana faman hanata aikin da take kafin take cewa” mu? Mu fa kika ce? Ko ban san shekarunki ba na san aunty ta fi ki sosai, kawa fa kamar ana nufin kamar ni da Leila, da Nana, da Mariam, aman kin san da aunty Alhinayett bata da kawa sai aboki?
Agaishat dake jin dadin hira da yar budurwar buzuwar ta bada hankalinta kanta tana ji tamkar kanwarta da ta rasu , a hankali ta daga kai tana hangen yan matan, take yan uwanta da mahaifiyarta suka fado mata a rai, ko ina suka shiga? Wardugu ya je kauye a lokacin sarkima bai dawo ba wai sun shiga birni wajen dangin Anna, gashi ya ce zai koma aman har yau bai samu ya koma ba dan aiki ya sha kansa,
Hankalinta ta maido wajen jida da ta hi zaman yan bori gabanta ta ce” sai ki fada waye abokin nata?
Jida ta yatsina fuska tana girgiza kai irin abu ya bata takaicin nan ta ce” ko kin ji ana fadin wani Wardugu?
Agaishat ta zaro ido bata bata amsa ba,
Jida ta ci gaba da fadin” bana zaki kasa sannin General Wardugu ba, wannan gabjejen katon mai ruwan samudawa, yana nan dogon nan fari aman fuska uwa kashin safe takwaf ba annuri, ni du zaman da nake rayuwana zan ce saurayinta ne, domin dai kin ga Abanmu tsauri ne da shi baya barinmu kula maza in ba wa.inda zamu aura ba, aman abin mamaki wai shi abokinta ne,
Ai ni kalonsu kawai nake, har a school ina fadawa kawayena ai yayata soyaya take da General Wardugu du wace ta taba ni zamu rufeta,
Wai kawai yanzu wai ace wani Aba? Hm na yi mamaki
Agaishat ta yi murmushin da ya bayanar da wutsiryarta ta mike dan dauko abin fifita wutar dan garwashin ya yi sanyi sai dai me? Ganinsa ta yi tsaye daga bakin kofar shigowa gidan, ya harde hannunsa saman kirjinsa, idannuwansa sanye da gilashi, aman yannayin fuskarsa kamar ita yake kallo,