BAK’A CE Page 51 to 60

Mikewa dogaran suka yi suna tsayar da shi tare da tambayarsa abinda ke tafe da shi
Asadeek baban dan kasuwa ne a garin Timiyar, ya kasance makiwaci, yana kiwon rakumansa yana shiga sahara da su, a kadan idan ya yi tafia sai ya kwashe wata shida sai dai abin mamaki wannan tafiar duka duka kwanansa uku da tafia abinka da karamin gari an san kowa an san me wane ke ciki, dan haka suka shiga mamakin ganninsa a irin wannan lokacin gashi kuma dauke da mutun
Asadeek ya janyo akalar Rakuminsa ya matso kusa da su,
Kamawa suka yi aka sauke mutumen dake saman rakumin, ba rawani a kansa wanda da sauri aka shiga neman rawani dan a nada masa domin buzu ba rawani tamkar tsirara yake jin kansa , tozarci ne a gare shi, ko alwallah zai yi yana yawan yi bayan idon mutane dan kar a ganshi ba rawani,
Da sauri suka luluba masa rawani , kafin suke maida hankalinsu kan Asadeek dake gurfane gaban sarkinsa ,
Duda da yawan cikinsu sun gane ko waye a wajen, aman basu nuna ganewar tasu ba gannin sarkin bai wani gane shi ba domin ya kyankyadare ya fita a hayacinsa tun ba.a je ko.ina ba,
Asadeek ya ce” Allah ja zamani, na je wajen rijiya dibarwa rakuma ruwa na ganshi kwonce gefen rijiyar a sume, da alama ruwan ya je dina sai dai karfinsa ya kare hakan ya sa ya fadi wajen ga zafin rana ga kishirwa ga iska ga idan yama ta yi sanyin sahara ya jigata ban san adadin kwanakin da ya dauka a haka ba ni dai na yi iya yina ya farfado inda ya hada wuta ya tatsi sabon nono na dan tafasa na bashi , hakan ne ya saka ya dan dawo hayacinsa aman gashinnan baya magana sai dai bina da ido da yake sai zazabin dake ta hawa yana sauka a jikinsa,
Da tausayi Sarki ke amsawa inda ya dubi mutumen da ya yakune tsofo sak ya ce” bawan Allah daga ina? Tafia ta riskeka yankin sahara? Kai din dan ina ne?
Da mamaki dogarai ke dan kara sada kansu dan sun gane sarki bai fa gane ko waye ba, sai dogari mai maimaici da ya daga murya ya maimaita maganar sarki,
A hankali ya dago kansa inda gaba daya jikinsa ke bari ya dubi sarki, wanda hakan da ya yi ya saka sarki zabura ya mike tsaye yana dubansa,
Hannunsa ya nuna ya ce” Algabiit? Daman kai ne? Daman kana yankin timiya ko dawowa ka yi?
Algabiit dake zaro idannuwa murya irin ta wanda ya sha wahala ya dago hannunsa zai nuna sarki da yatsarsa wani yaron dogarin ya saka mafici ya buge hannun yana fadin” hatara dai tsofo kar a nunawa mai garin timiya yatsa, kimtsa zamanka da lafazinka ga sarkin timiya
Sarki ya juyo ya yi masa wani kallo mai nuni da bai ji dadin duke hannun da aka yi ba, hakan ya sa suka kwashi masa kirari da ban hakuri,
Algabiit ya dan ja baya yana dubansu , baki na rawa ya ce” ina ka kai mini ita? Da yarana? Masu neman aurensu sun zo bakwa nan sun baza nemana kan idan ban biya ba sai dai su tafi da ni? Ina zasu kai ni? Me zasu yi mini? Ka fada mani inda suke ta bani yarana in basu ko zasu shafa mani lafia!
Sarki ya girgiza kansa yana dubansa, wato dai bai nutsu ba, alamun gajiyawar ba har cikin zuci ba,? Baya tunanin zai iya dogon bayanin fahimtar junna da wannan bawan Allah, arziki daya ya ci na haihuwar matarsa da ya yi, dan haka ya ce”
Baka da labarin ta dawo hayacinta? Tana garin Niamey gidan Kugunni ka je can ka dauko su,
Wata zabura ya yi yana dafe kirjinsa, yana duban sarki ya ce” Gukunni? Shikennan ka tona mani asiri, ka wulakanta ni, sai ka sakar mani y’ata, idan baka sakar mani y’ata ba sai na zame maka fitina a rayuwa da mulkin da kake takama da kwonciyar hankalin gidanka!
Dogarai du suka mike inda sarkin bulala ya zabura ya mike bulalar hannunsa ta shiga wulgawa tana karawa,
Sarki ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa,
Fuska hade ya bada umarnin a shiga da Algabitt dakin sirri!
Jansa aka yi yana ihun a sake shi , aman ina ba zai iya kwatar kansa ba aka nufi dakin sirrin sarki da shi, wanda bai san wani dakin sirri a gidan ba sai yau, su kuwa suna zuwa tamkar wani kayan wanki suka jefar da shi suka fito abinsu suna baza rigunnansu, inda sarki ya ci gaba da shara.arsa kafin yake gamawa su tashi salar isha.i,
Bayan salar ne da ya shiga gida bai fito ba domin ya hada tarin gagawa na matarsa da sirikinsa da shi din kansa wanda zasu wakanar a dakin sirrinsa dake daf da shiga cikin gidan matansa. Wannan kennan
Niamey
Kanta na rawa , dan malolon mayafinta a hannunta ta afka gidan inda kawarta ke biye da ita,
Sai dai me? Kafin take idasa shiga ba da salama ba ta hango keyarsa don ya baiwa kofar shigowar baya ne,
Bata taba sannin ta iya gagawa irin wannan ba, domin a lokaci kankani har ta ja mayafinta ta rufa a kanta sai jansa take dan ya dan sauka hakannanma, ta shiga gyara daurin dankwalinta, sannan ta dan waiwayo dan fadawa kawarta Wardugu ne , sai dai da mamakinta ta fice tuni a gidan, wato ta yi baya, kennan ta gane ko waye,
Nutsuwa ta gayato karfi da yaji kafin take watsawa yayan buzayen harara ta kakaro murmushi ta yi salama tana karasawa gurin su, don zuwa lokacin Wardugun dai ne ke tsaye kikam cikin zafin ranar garin ya tsurawa wajen da randa take kamar hankalinsa na wajen shinkuwa idannuwansa kawai suke wajen,
Su Alhinayett kuwa suna zaune a tabarma inda Agaishat ta ja ta rufe wajen da ya bude ya ganni ta dauki wayarta dake ta ruri ta daga,
Ayya ce ke kiranta dan haka ta amsa murya sanyaye inda Ayya ta shiga tambayarta lafia? Dan muryarta ta yi mata kama da wace ta yi kuka,
Ajiyar zucia ta sauke ta ce” lafia kalau Ayanna,
Ayya ta ce” Madame Rukaya ce ta zo karbar excercice din da ta baki , ni kam ko kin yi? Kina dokin zuwa sadakin nan tun jiya?
Agaishat ta kwabe fuska ta ce” Ayya, na yi , yana cikin dakina kusan gado, Ayya ni fa ke zaki zo daukana ni dai
Ta karashe tana kyakyabe fuska irin na batatun yaran nan,
Ayya ta ce” kar na ji an min kuka, meye a su zuwa dauko ki? Da kin gama ki yi kirana zan zo na dauko ki yar autana,
Murmushi ta saki kafin su kashe wayar,
Alhinayett da ta gama amsa barkan Walyn ta dan zunguri Agaishat ta cuni mata baki ta ce” mai baci kawai,
Agaishat ta yi mata gwalo kafin take kokarin mikewa dan tunda ta juyo ta lura da uban hararar da ta samu daga wajen matar banban yaya,
Wardugu dake zaune shima saman kujerar kwal dake wajen a ransa ya ayyana ina kuma zata je?
Ta cikin gilashin yake kallon yanda da ta mike sai da ta daga hannayenta biyu ta harhada gashin kanta ta saka dan ribom dinta fari ta daure shi, sannan ta juya masu baya ta kwonce laylfayarta da kyar ta dan kakabeta a jikinta sannan ta samu ta nada kayanta har kanta,
Juyawa ta yi ta shiga dingisa kafarta ta koma wajen gashin naman dai inda Jidan dai take,
Kuma tana zuwa suka shiga kokowar sai ta karbe cokalin juyawar tana fadin ita ba dafa shayi bane aikinta,
Ina ba zai yiwu ba,
Shi ne abinda ya fada a fili, kafin yake mikeqa ya hade fuska ya ce” Ke, dawo ki zauna,
Tunda ya ce ke din, du ke din dake wajen ta dawo da hankalinta wajensa dan kar a je ita ke din yake nufi, domin ke dai lakanin suna ne da ake cewa mace halita wato Ke,
Inda hankalinsa ya fi kaiwa du suka kuma mayar da dubansa, wace qkiwa kallon itama ta ji uwa ta tsunduma a guje dan tsoron ihun da ya yi da kuma du kallon da suka yo mata,