BAK’A CE Page 51 to 60

Ajiye cokalin ta yi, zuwa lokacin du sun kawar da dubansu banda Walyn, Wardugu da Alhinayett,
Walyn mutuwar zaune ne ta yi, bata gane komai ba, aman irin ihun da ya yi kan ta zo ta zauna ya sakata itama tsura mata ido, a hankali ta maida dubanta kansa, ita din dai ya tsare da kallo har sai da ta karaso ta zauna kafin yake daukan babar wayarsa ya shiga dadanawa,
Zama ta yi tamkar mai kallon tv, don ta yi juyi ya fi a kirga tsakanin yannayin mijinta da shirun da wajen da ya yi, da yar hirar da su Alhinayett din ke yi fa yaren buzanci inda Alhinayett ta rage murya wajen fadin” ke da kika ji ciwo me ya kai ki tashi?
Agaishat ta ce” wannan har wani ciwo ne Alhinayett? Wajen da ko tashi bai yi Allah ya yi masa tsawa? Ina dan dingisawan nan ne dan zaman da na yi kafafuwana a tankwashe sun min tsami,
Alhinayett ta ce” Eyah, ai shi Wardugu bai gane ba,
Warsugu da suke zancen da yaren buzanci shima da yaren nasu ya ce” kar ki saki ki tashi, ki zauna ya huce, kin ji na fada maki,
Agaishat ta dube shi, yanda ya yi magana da yarenta abin sai ya mugun birgeta, murmushi ta saki kafin ta kawar da kanta ta tuna ashe fa yana jin Buzanci, Allah ya taimaketa ba wani abu ta fada ba da ya ji,
Alhinayett ta kai dubanta wajen yan matan gannin sun fitar da kayan zuba abincin sannan sun fara zuba shayin sai dai du suna tsoron zuwa wajen dan Wardugu da ya hade rai,
Walyn ta hadiye wani abu a zuciyarya kafin take kokarin cicibawa ta mike tana duban Wardugu ta ce” mu tafi Wardugu dare na yi kar dare ya yi,
Dubanta ya yi da kulawa, ko dan mutanen dake wajen baya saurin gwasaleta gaban mutane, dan haka ya dubeta da kyau kafin ya ce” ke da motarki daban tawa daban, kuma ba ke kadai bace? Ki je kawai gani nan zuwa,
Tsam ta yi tana bin yan matan da kallo, yanzu a cikin wannan zuga zugan yan matan zata tafi ta bar mijinta?
Sai dai ta makaro tunda ta mike idan tace zata zauna ko wani abin za.a samu matsala, dan haka ta yi masa murmushi ta juya ta fice ba tare da tace da su sai an jima ko su ci kansu ba, sai Alhinayett ce tace da ita ta gode,
Bata bata amsa ba ta fice tana ta tunani ta tarar da kawarta na shating da waya inda ta gyara zamanta ta tura masa sako kamar haka” namijin duniya , jarumin jarumai, na hangoka, ka kara sacen zuciya Warduguna, ina son ka koda kuwa kai baka so na,
Hango Walyn da ta yi ya saka ta yi gagawar gogewa ta fita a whatsupp din baki daya ta daidaita kanta daga tafia yabon mijin aminiyar nata da ta afka, ita fa ta fice da class din Walyn aman saboda ta samu shiga wajen Wardugu ya saka take yawo da ita a gari,
Motar ta bude ta shiga ta rufe da karfi kafin take juya dubanta wajen kofar shigan,
Dankwalin kan nata ta tuje ta yi tsai tana tunani kafin ta dubi kawar tata ta ce” kina tunanin Warduguna zai iya kula *Bakar Mace?*
Ido ta zaro ta ce” Bak’a kuma?
Walyn ta gyada kai tana dubanta,
Shewa ta yi kafin ta juya idannuwanta ta ce” ke, kina zaune da mijin naki baki san waye shi ba? Wardugu? Mutumen da a jarida ake bayannin kasashen da ya taka? Kin san kasashen da ya je mata tamkar su suka halici kansu? Ke dan ki zama mai sa.a a cikin mata shi ne zaki yi tunanin wai Wardugu zai dubi wata bak’ar mace? Me aka yi aka yi *Bak’a*? , me zai tayar da hankalinsa ya ja ra.ayinsa a bak’a ko yar gidan uban waye? Ke a bakar mace ina jin dadi? Bare harka? Me zai duba? Bakaken yan biyun ko bakin ogan?
Daria suka kwashe da ita suka tafa kafin walyn take sauke ajiyar zuciya, aman a zuciyarta ta yi waje ta ajiye irin shiga zuciyar da *Bak’ar* yarinyar ta yi a wajen uwar mijinta da mijin nata kansa, zata so sannin asalin yarinyar duda ta ga a inda aka daukota aman bata san meye dalilin daukotan ba!
Ba wardugu ya bar gidan ba sai wajen magariba, ba komai ba kuwa ya hana shi tafia sai dan kar ta tashi ta shiga wani aikin, yana zaune ya hade rai tamkar hadarin gabas komai sai dai a kawo mata rabonta har sai da ya tashi tafia ya saka ta yi kiran Ayyanta a gabansa kafin ya fice ya bar gidan,
Alhinayett kam tunda ya fada mata aure nan da wata guda jikinta ya yi sanyi, bai ce da ita komai ba sai dai ya dubeta ya yi mata murmushi , ita kuwa du tsoro ne ya gama kasheta a zaunen da take, abin ya zo mata da gagawa, ita tsoronta Allah tsoronta auren soja!
Dare ne ya tsala, a lokacin da bayi ke hutawa shi kam juyi yake saman makeken bed dinsa,
A bukace yake da ainahin matarsa, sai dai ya jima rabonsa da ya wani kai mata kansa, idan ta zo halas idan bata zo ba sai dai ya yi ta juyi abinsa har safiya ta yi,
Kamar daga sama ya fara jiyo kamshinta,
Lamo ya yi bai nuna zalama ba har ta karaso gareshi,
Jikinsa ta shige ta shiga kokarin sarafa shi,
Ya jima kafin yake bata amsa inda sai da suka hau sama ya mike dan saka abinda ya tsiro mata da shi tun bayan dawowarta gida, ya daina yarda ya zuba mata wani abinda ya fito daga jikinsa, danma tsaro yakan aiki da abinda zai tare masa tana jintana gani,
Mikewa ta yi tana dubansa jiki sanyaye ta ce” Wardugu, me yasa kake haka ne? Danme kake anfani da irin wannan abin bayan da matarka ta sunna kake tarawa?
Dubanta ya yi tsaf kafi yake turata baya ta fada saman bed din,
Kafin ya bi bayanta ya ce” kamar yanda kika kawo kanki a yau, haka zan yi yanda na ga yana gyara ni, ko ba komai hankalina kwonce ba sau ya rikide ya fara zama gudan jinina a markade shi ba kafin mai rikewa ta zo !
????♀ ba zan iya fadin sunnaye gatsai ba????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Share this
[ad_2]