BAK’A CE Page 51 to 60

Dif Ayya ta yi da tambayoyinta tana duban Wardugu, saki? Abinda kunnayenta suka jiyo mata kennan?
A hankali ta kankace idannuwanta tana duban Wardugu zatai magana kennan ta ji Agaishat ta ce” Ayya wai ya sake ni, Ayya ban san laifin da na yi masa ba,
Ayya ta kallo wardugu ta ce” Saki,? Aka yiwa y’ata? Shin ciwon nasa haukata shi yayi kafin a gane har na dauki y’a na bashi ? Mahaukaci ne da riga?
Wardugu ya dago yana duban Ayya da auna yannayinta, daga muryarta ya fara dauko cewa Ayya ta fara hawa, wato tana harhada dukan abinda gareta na tashin hankali wanda yayi imanin zata saki a yanzu yanzu,
Ajiyar zuciya ya saki ya ce” da hankalinsa
Ayya ta zabura ta mike tsaye, idannuwanta ta karasa kankancewa ta nuno wardugu da dan karamin yatsarta ta ce” ni? Ni zaku yiwa wulakanci? Ni zaku tozarta? Ni zaku watsawa kasa a ido? Ni zaku tonawa asiri? Ni zan dauki yarinya na baku ko wata batai ba ku sako mini bayan ba kangarariya na baku ba kuma ba hujajen buhu na baku ba? Ba nakasashiya na baku ba kuma ba neman kai nake da ita ba na dauka na baku ba? Gaskiyar Aghali, a lokacin da ya zo min bankwana nake fada masa maganar kun tafi neman aurwn yarinyata yace da ni haba Ayya, ai da ni zan ce ina so, na yi mata dukan abinda za.a yiwa yar gata na aureta a kaita gidana na kula maki da yarinya, aman yanzu kika baiwa abokin Wardugu kin tabata zai rike maki y’a?
Wardugu ya dago kansa da sauri, dan tunda ta fara maganar kansa ke sade, bai yi niya ba, bai so tanka Ayya ko daya ba, dan an bata mata tanada damar yin fada ta yi abinda take so, shine mai laifi dan shi ya uzurata , ya lalabata har ta aminta da a je a dauro auren, ya so yin shiru ta kare kansa, shi kuwa tasu shi da Mu.azam ne, Takunsu na gogagu ne, zasu goga ! Sai dai ji yayi bakinsa ya ce” Haka yace kennan?
Ayya ta ce” Ubanka yace Wardugu, nace Uban nan naka yace! Ba gashi ba ya nuna halin ba.a je ko.ina ba? Sai na yi shara.a da shi! Ba zan barku ba ku duka! Wato an baku y’ar a saukin kudi ko? Baku yi tade tadensu na buzaye ba kun samu abin a bagas ko?
Agaishat dake kallon Ayya, ta ce” Ayya, dan Allah a bashi hakuri ya mayar da ni , walahi ba zan kara yi masa koma mene yace na yi masa ba,
Ayya ta juyo da mamaki ta rike habarta ta yi tsai tana kallon Agaishat inda dakin ya dauki wani dan shiru, can ta ce” kina ji? Ki tashi, ki je dakinki ki cire mini wannan rigar ki yi mini wanka ki wanke ruwan gidan wannan banzan, ki yi sallah ki kwonta ki yi baci tun kafin na yi baja baja da ke a gidannan! Ka ji rashin sannin ciwon kai? Namijin zaki turani lalabo shi? To ko ku haka kuka a tadanku na buzaye na soke maki hakan a rayuwarki na haramta maki hakan! Walahi walahi walahi ni Ayya in dai na rike ki ko na kwana daya ne karya ne ki kuma waiwayar wani Mu.zzam koda shi daya kwal ya rage a duniya! Agaishat bace min da ganni kafin na maki marin da zai kufumta maki kunne!
Da sauri ta mike tana karkarwa ta shiga taka matatakalar benen ta haye da gudu ta nufi dakinta tana waiwayen Ayya dake tsaye sai da ta bacewa ganninta ta juyo wajen wardugu,
Takowa ta yi har gabansa ta tsaya ta ce” in sha Allah na dauki alwashin sai ta zama abin hangensa daga nesa, sai ya yi dan daman bai sakar min y’a ba, ubankuma bai isa ba bale ku (wato Marahut), wasan kuke so bugawa da ni ko? Ni zaku kawowa wargi a wannan lamarin ko? Na gode , aman ka fada masa gidana da gaishe da ni sun haramta a gare shi! Yarinyata nada gatanta, in da hakinta kuma ban yafe ba!
Shi dai Wardugu kansa na kallon kasa, shi ganima yake da sauki tunda bata kai ga kifa masa mariba, sannan a haramtawar tata banda shi, dan haka ya sada kai sai da ta kare fadanta ta juya ta haye sama ya samu wuf ya fice a gidan,
A wannan dare kwana Ayya ta yi tana fada tana kai kawo tsakannin dakinta da na Agaishat tana duba lafiarta da banka mata harara danma karta yarda ta kuma kawo mata shirmen wai a lalaba shi, yo Allah ta tuba ko ita dake tsohuwa ta wani bi namiji a yanzu bare y’arta yarinya mai jini a hanci son kowa kin wanda ya rasa? In sha Allah zata kulata ta gama idarta tsaf sai su san abin yi, fatanta Allah ya sa bata dauko ciki ba dan a yanda take cikennan kar a je sai da ya kumsa mata ciki ya saketa (wato dai du a tunaninsu wani abu ya shiga tsakannin Agaishat da Mu.azam…..)
Wardugu kuwa na shiga gidansa ya tarar da gidan shiru kamar koda yaushe,
Bai wani damu da neman gannin matarsa ba ya nufi bangarensa,
Yana shiga ya tarar da farar takarda an ajiye ya dauka ya karanta, mai aikinsa ce ta yi masa salama da fadin ba zata iya ba madame ta koreta ta mata alkawarin in dai ta zauna mata a gida zata soketa da wuka!
Murmushi yayi ya yarda takardar nan ya shiga dakin da kyau, falon ya danyi kura abinka da fararan kaya nan ya yarda jakarsa ya nufi wajen wayar dake dakin ya daga ya shiga latsa numbobi…..
Tafiar awa gudu suka yi kafin su karasa garin Agadez capital de l.aïr
Hilux din sarki ce ke jiransu da direba, suna sauka direba ya dauko su inda kamshin turaransu ya cika motar
…………………comment comment.comment
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣0️⃣
Motar na saka hancinta cikin gidan *Hatimi* ta rike hannun mijinta gam,
Shima din a zaunen kawai yake aman du gani yake ba.a sauri an kasa karasawa,
Anna dake tsaye a falon sarki dan baki daya can ya dugunzuma su sai kallon kofa take tana kai kawo ,
Turo kofar da aka yi ne ya saka ta tasayawa cak tana kallo ,
Direban ya fara shigowa kafin *Gukunni* sai *Hatimi*,
Dan tsai suka yi kafin Hatimi ta daga kafa da sauri sauri jikinta na bari ta karasa wajen Anna da kafafuwanta suka kasa dagawa daga tsayuwar ,
Tana zuwa rungumeta a jikinta inda Gukunnima ya karaso kafafuwansa na hardewa ya hadasu su duka ya rungume,
Ido kawai ta lumshe wanda jin nauyinta ya yi yawa ya saka Hatimi sasauta rikon da tai mata tana talafeta tana faman kufce mata dan ta yi nauyi da yawa,
Da kyar suka samu suka talafota, Anna ta suma
Nan fa hankali ya tashi sai ihun a fitar da mota a tafi asibiti suke suna talafe da ita a jikinsu,
Sarki je ya karaso da ruwa da sauri aka shafa mata
Wani irin numfashi ta ja kafin take buda idannuwanta a rikice irin farkawar sumarnan da mutun ke yi.
Ganninta jikin mahaifinta , wanda yake da dan gemu kadan fari wato furfura sai girarsa da ta fara farin itama, sai hannun mahaifiyarta fa dake jimke da nata ta dan daga a hankali ta ga hannun ya dan fara yakushewa irin na tsufan nan,
Kuka ta fashe da shi tana kara shigewa jikinsu, ji take tamkar idan ta sake su zasu bace a gabanta ne, dan haka ta ririke su tana kallonsu tana kara shigewa jikinsu
Sun jima a wannan yannayi, inda yayanta ke zaune can gefe , kukan yarima jariri ne ya fargar da su inda Anna sai a lokacin ta tuna da y’ayanta,
Dan sasauta rikon ta yi masu gannin ana dan waiwayawa inda yaran nata suke zazaune suna fama mimika Yarima boy sunna jijiga shi a tsakaninsu,