BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 51 to 60

Tsare su Hatimi ta yi da ido kafin a hankali ta dawo da dubanta wajen Anna,

Murya na rawa ta ce” *Allatchi?*, ina kika shiga kika barmu cikin tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya? 

Anna ta tsareta da idon itama, 

Gukunni ya riko hannunta ya ce” Allatchi, kin san irin tashin hankalin da na shiga dalilin dawowa daga wajen aiki da na yi na tarar da anmanki da *Herde* tsakar gida suna kuka wai baki motarki aka ganni a kofar gida aman ke baki dawo ba kuma wayarki bata shiga? Ina kika je? 

Anna ta sada idannuwanta kafin a hankali ta ce” ban san da me ya juyar da hankalina ba, wanda tunda na baiwa gida baya ban san takamaiman abinda ya faru da ni ba sai nan da kwana goma na dawo hayacina, hasalima ban san *zaman da na yi da shi na shekara da shekaru ko da aure muka yi shi ko kuwa zaman haka muka yi?* , gashi harda y’aya suma sun fara haihuwa,

Zabura Gukunni ya yi ya mike tsaye, nan da nan jikinsa ya dauki rawar bacin rai da tashin hankali, murya bace ya ce” waye? Dan gidan waye? Wanene ubansa da kuma shi din kansa? Ko wanene ina mai tabatar maki da sai dai a yi daya cikin ni da shi, sai na rufe shi rufewar da ba zai fito ba sai dai a fitar da shi!, koda ya ki fitowa yaransa zan rufe sai ya bayanar da kansa! Sai na nuna masa danyen kai koda ubanshi sarki ne! 

Anna dake zaune ta dago da kanta da sauri gabanta na faduwa, muryarta na rawa ta ce” yaranshi? Ko yarana? Abanna, bai damu da yaren ba dan ya yi rayuwarsa ne ta hanyar siyar da su, wato yana karbar sadakin yarana a tafi da su shikennan , ba sai ua damu da yaranba zai damu dan an rufe su? Aa ba za.a taba mini yaranna ba dan ina son su! 

Ta karashe tana mai fashewa da kuka ta ce” mun yi rayuwa cikin dajin Timiya, 

*Algabitt* ya kasance dodo , kura, fitina a rayuwarmu ni da yaranna, 

*Algabit?* Hatimi ta tambaya tana mai son karin bayani kan waye hakan? Dan ta manta, bata taba kawowa a ranta ba, 

Anna ta dubeta da kyau ta ce” Algabitt wanda Muka kade da Mota ni da Herde daga karshe Abanna ya dauke shi aiki a gida,

Hatimima mikewar ta yi a tsorace tana fitar da idannuwanta baki daya tana kallon Anna,

Anna ta dago kanta ta shiga kora masu dukan abubuwan da kwakwaluwarta ke iya tinnawa, 

Mahaifiyarta kawai mutuwar tsaye ta yi, dan abin ya mugun daketa, wai Algabitt? Yaron da ta dauka tamkar dan gida? Eh lale aikinsa baiwa fulawowi ruwa, aman tunda ta ga y’ayanta na son lamarinsa ta yarge masa shiga falonsu, a zauna da shi a sha dariya, bale da ya fada masu shi maraya ne shikennan suka kara yarda da shi duda wani lokacin mahaifin su Anna na fadin yaron nan yanada wani kallo irin na munafukai, sai ta yi daria ta jinjina hannunta tana fadin sai alkalina, kai fa ka saka na aminta da mu dauko yaronnan, sai yanzu da muka shaku da shi kai kuwa ka fara hango wani abin? 

Bayan Anna ta yi shiru da labarinta Hatimi ta duka inda take zaune ta jata jikinta irin rarashi,

Gukunni kuwa sai wani irin numfashi yake fitarwa na bacin rai, bai ko kalli inda su Gaishata suke ba, dan shi kama suke masa da yaron, sai yanzu ya tina yaron, kam, lale haduwarsa da wannan bakin macijin za.a sha mamaki, 

Hatimi ta dago tana share hawayenta ta ce” Gukunni, ka yi hakuri, yanzun ya dace mu yi murnar ganninta, na tabata asiri yayi mata, mu yi fatan da aure ya rayu da ita , mu rungumi jikokinmu, na san Herde sai ta fi kowa murnar yarannan , ta kwashi yayan wasuma bare na yar uwarta wace suka shaku ? Ai ni da zaka amince minma da ba zamu wani yi shara.a da wannan yaro ba, idan har ya sanar mana gaskiyar da aure ya rayu da ita? Ya sawake mata salim alim ya je, duniya ce, sannan mai duka na madakata, ya je ya yi abinda yake so idan tunaninka kai din wani shege ne a duniya toh tabasa akoy wanda ya dameka ya shanye, ba zan yi shara.a da shi ba, bai isa ba, cuta ya gama cutata , sai dai na gode Allah da tun kasa bata rufe mani idannu ba Allah ya bayanar min da ita, 

Gukunni ya juya yana kallon su Agaishat , ya juya wajen su sarki dake zaune sun yi zuru suma, 

Da kai Sarki ya jinjina masa irin nuni da ya yi hakuri, ya tausasa zuciyarsa,

Dan yatsansa karami ya dantsa a bakinsa kafin ya kada kai ya nufi wajen su Agaishat da suka tsurewa nufo sun da ya yi,

Yana zuwa ya duka ya dauki Yarima Boy dake kuka ya juya ya fice a falon da shi,

Murmushi Hatimi ta yi tana duban su ta ce” zai huce, ko dan dan jaririn wannan fushinsa ba zai yi tsayi ba, dan yana son yara kamar me, burinsa ya samu dan jika , 

Sarki ya sauke ajiyar zuciya, ya kuma kiran uwar gidansa domin ba a gabanta akai komai ba,

Tana zuwa ya umarceta da ta baiwa baki wajen hutawa,

Dukansu suka mike suka je bangaren sauke bakin alfarma aka basu dakunna wanda matar sarki ta nuna masu kowa dadaya, aman Anna ta kiya kan su hade suka,

Hakan kuwa aka yi dan haka sai aka shigo da sauran gadajen dan dakunnan akoy girma aka yi masu shinfidun alfarma inda suka shiga gaba dayansu,

Sai a lokacin Hatimi ta zo wajen su Agaishat dake tare waje guda ta zauna tana kallonsu,

A hankali ta ringa rungumarsu tana tausaya masu, zuka zukan yan mata ya wannan aman a cikin duhun kai, suturun jikinsuma abin tausayi wai a nan sun wanku ne? , ko.ina yar uwar tasu take ita? Shiga halin kaka naka yi har ka cire da ka mika kyauta, karshe a zo a aure shi bada izini ko saninka ba sai komai ya wakana a sanar da kai, 

Kai bata tunanin akoy kotun da zata iya yi mata shari.a da Algabitt a nan gidan duniya.

                   *NIAMEY*

Jakar hannunsa ya yar a nan ya shige dakansa yana yatsina fuska dan kyankyamin wajen yake,

Samu ya yi ya buda wajen tufafinsa ya ciro kaya masu tsafta 

Yana kokarin rufewa ta shigo dakin, yauma dai cikin kwaliyar take duda bata san da zuwansa ba,

Walyn kam akoy kama jiki, akoy kanshi, akoy iya kwaliya,

Karasa shigowa ta yi tana duban hannunsa da mamaki, wasu kayan ne ya dauka, ina zai je kuma? Shida yanzu shigowarsa har zai juya? 

Da sauri ta idasa kusa da shi tana mika hannu wajen kayan ta ce” Wardugu, ina zaka je? Dan Allah yanzu fa ka dawo, daga ina kake haka wajen sati uku? Kuma ka dawo yanzu ka kuma fita? 

Bai tsaya sauraronta ba ya goce kar ta karbi kayan ya rabata zai fice

Hankalinta ne ya kara tashi, ta san waye mijinta wajen harkar mu.amalarsa da matarsa(aurataya), aman yanzu har tsayin wannan lokacin bai wani nemeta ba?

Da sauri ta je ta bayansa ta rungume shi, hannunsa ta kamo ta dora saman rigarta wajen mararta ta ce” baka tambayi ajiyarka ba zaka tafi? Baka damu da cikinka dake jikina ba?

Wardugu ya janye hannunsa ya juyo yana kallonta tun daga kanta har kasa, idannuwansa ya dan bude kafin ya ce” kudin account din ki sun yi kasa ne? 

Wani abu ta ji marar dadi a ranta, tabas tana yawan yi masa biyaya idan tana son kudi, aman ita yanzu bama kudin ya kawota ba, gannin baya gida ne ya fara daga mata hankali,

A hankali ta kai hannunta bayan zip dinta ta zuge shi har kasa, ta ja rigar ta cire ta shiga nufo shi tana mai kokarin jan ra.ayinsa,

Bai wani kawar da kai ba, sai da ya kureta da kallon tsaf kafin ya saki wani murmushi irin na ka raina abu ya juya ya fice a dakin ya barta nan tsaye tamkar mutun mutuni,

Ido ta kwalalo da matsanancin mamaki ta kwala wani ihu kafin tace” walahi ban yarda ba, kai ka ga haka ka tsalake? Kawai ka tare da wata yar iskar, walahi sai na bika na gani,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button