BAK’A CE Page 51 to 60

Dukansu suka mike suka je bangaren sauke bakin alfarma aka basu dakunna wanda matar sarki ta nuna masu kowa dadaya, aman Anna ta kiya kan su hade suka,
Hakan kuwa aka yi dan haka sai aka shigo da sauran gadajen dan dakunnan akoy girma aka yi masu shinfidun alfarma inda suka shiga gaba dayansu,
Sai a lokacin Hatimi ta zo wajen su Agaishat dake tare waje guda ta zauna tana kallonsu,
A hankali ta ringa rungumarsu tana tausaya masu, zuka zukan yan mata ya wannan aman a cikin duhun kai, suturun jikinsuma abin tausayi wai a nan sun wanku ne? , ko.ina yar uwar tasu take ita? Shiga halin kaka naka yi har ka cire da ka mika kyauta, karshe a zo a aure shi bada izini ko saninka ba sai komai ya wakana a sanar da kai,
Kai bata tunanin akoy kotun da zata iya yi mata shari.a da Algabitt a nan gidan duniya.
*NIAMEY*
Jakar hannunsa ya yar a nan ya shige dakansa yana yatsina fuska dan kyankyamin wajen yake,
Samu ya yi ya buda wajen tufafinsa ya ciro kaya masu tsafta
Yana kokarin rufewa ta shigo dakin, yauma dai cikin kwaliyar take duda bata san da zuwansa ba,
Walyn kam akoy kama jiki, akoy kanshi, akoy iya kwaliya,
Karasa shigowa ta yi tana duban hannunsa da mamaki, wasu kayan ne ya dauka, ina zai je kuma? Shida yanzu shigowarsa har zai juya?
Da sauri ta idasa kusa da shi tana mika hannu wajen kayan ta ce” Wardugu, ina zaka je? Dan Allah yanzu fa ka dawo, daga ina kake haka wajen sati uku? Kuma ka dawo yanzu ka kuma fita?
Bai tsaya sauraronta ba ya goce kar ta karbi kayan ya rabata zai fice
Hankalinta ne ya kara tashi, ta san waye mijinta wajen harkar mu.amalarsa da matarsa(aurataya), aman yanzu har tsayin wannan lokacin bai wani nemeta ba?
Da sauri ta je ta bayansa ta rungume shi, hannunsa ta kamo ta dora saman rigarta wajen mararta ta ce” baka tambayi ajiyarka ba zaka tafi? Baka damu da cikinka dake jikina ba?
Wardugu ya janye hannunsa ya juyo yana kallonta tun daga kanta har kasa, idannuwansa ya dan bude kafin ya ce” kudin account din ki sun yi kasa ne?
Wani abu ta ji marar dadi a ranta, tabas tana yawan yi masa biyaya idan tana son kudi, aman ita yanzu bama kudin ya kawota ba, gannin baya gida ne ya fara daga mata hankali,
A hankali ta kai hannunta bayan zip dinta ta zuge shi har kasa, ta ja rigar ta cire ta shiga nufo shi tana mai kokarin jan ra.ayinsa,
Bai wani kawar da kai ba, sai da ya kureta da kallon tsaf kafin ya saki wani murmushi irin na ka raina abu ya juya ya fice a dakin ya barta nan tsaye tamkar mutun mutuni,
Ido ta kwalalo da matsanancin mamaki ta kwala wani ihu kafin tace” walahi ban yarda ba, kai ka ga haka ka tsalake? Kawai ka tare da wata yar iskar, walahi sai na bika na gani,
Wardugu na jan dankareriyar motarsa ya fice Walynma ta fito da tata ko dan kwali babu saman kanta tsabar neman fitina da jayowa kai fitina ta shiga bin bayansa a hankali inda ya ganta ta miroir tunda danja ta tsayar da shi,
Murmushi ya saki mai tsada kafin ya ciro wayarsa ya nemo lambar Basma a cikin whatsupp dinsa ya danna mata kira
Ka na rana, in sha Allah za.a samu na dare
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣1️⃣
Hanya ya canza ya dauki ta gidan minister,
Kiran da ya yi mata daya kwal ta daga ya fada mata yana anguwarsu kishi ya kama shi yana muradin ruwa,
Abinka da yan gayu, dama a wanke take a lume cikin katuwar kujerar falonsu, tana jin haka ta mike da gudu ta haye sama ta feshe jikinta da turare ta ajiye wayarta ta sauko kicin ta dauki faranti fari ta dora goran ruwan Awa, ta kuma kiran saurayinta da zai zo zance cewar kar ya zo ta fita!
Dan nesa da gidan ya tsaya, domin a kofar gidan gwomnatin yaransa ne ke gadi suna baiwa gidan tsaro,
Yana nan zaune yana hangen Motar Walyn sannan ya dan dago ya hangota ta fito daga gidan nasu,
Cancandi inji ni, yarinyar fa ta gama haduwa, farin ne? Tana da shi, kyan ne? Ta gaje shi, tsarin halitar ne? Ta ninka Walyn sau biyu, yarinya Shuwa Arab, gashinta ta yi kwaliya da shi ta sake shi, taku take da dogon takalminta dan kara jan ra.ayinsa, inda ya kawar da kansa daga dubanta , wani uban tsaki ya jawa kansa, wani haushin kansa ya ji a lokacin da zuciyarsa ta raya masa wani lamari a kan wada ba zai so zuciyarsa ta falasa shi ba, zuciyarsa ce ta hasko masa gudunta na dazu da rigar dake jikinta Blue mai ruwan samaniya, zuciyarsa ta fada cewa” ta zarce misali,
Idannuwansa ya rintse daidai nan ya ji tana buga masa glas din mota,
Cire lock din ya yi dan haka ta bude ta taka ta shiga
Tana shiga ta juyo da ruwan da iya kwarkwasar da ta san tana tafia da duban samari ta yi masa salama,
Dubanta ya yi irin na tsaf din nan kafin yake karbar ruwan ya yi mata nuni da tana iya tafia,
Ido ta zaro kafi ta shagwabe fuska ta ce” haba abincin ruhina, daga zuwa sai ka kore ni?
Wardugu ya hade fuska ya ce” fitarmin a mota na ce!
Da sauri ta kama marfin motar ta dira daga motar tana kallonsa ya watsa mata wani kallon kyama ya yi ribos ya nufi hotel dan ba zai iya kwana a gidan ba ya yi masa dati,
Walyn kam kamar mahaukaciya ta tada motar tana zabga gudun sai ta kamo shi , ta yiwa yarinyar kuma kallon tsaf tana kwafa kan zata dawo gareta
Yana tsayawa da mota ya fito, ta fito da sauri ko rufe motar batai ba ta tunkaro shi
Sai dai kafin ta karaso yannayin fuskarsa ya saka ta rage saurin da take,
A haka ya shiga cikin Hotel din inda take binsa da sasarfa
Du daki daya kwana daya jika dari uku ne , ky ya karba ya juya ya je wajen accenseur ya shiga,
Tana tsaye har ta ga wajen da ya tsaya ya nuna ya dawo ta danna itama ta shiga ya daga da ita,
Yana budewa ta sako kafarta guda wajen ta ji an yi sama da ita sannan an rufe bakinta,
Wutsil wutsil take har ya shiga dakin ya direta saman kujera,
Kafarsa guda ya dora gefen kujerar yana dubanta kafin ya ce” ke, kin raina ni ko?
Fashewa ta yi da kuka , tana kuka ta ce” yanzu wardugu amanata kake ci? Budurwa ka yi? Wannan yarinyar dake yawo itace ta dauke min hankalinka har sati uku? Wardugu cikinka nake dauke da shi fa? Wardugu kai fa batube ne, ka san ko a al.adunmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta haihu kamar uku ko hudu, yanzu Wardugu ko cikin na fari bai fito a jikina ba ka fara zuwa wajen budurwa ka yi zamanka ka manta da ni du irin kiran da na yi ta yi maka?
Sai da ta kare magangannunta ya ce” auren zobe na yi da ke?
Ni ka daina fadin maganar auren zobe, ba wani auren zobe, ai mu ba auren zobe ya kawo mana wannan ba, al.adunmu suka hana.
Adini ne? Ya fada yana kara tsareta da ido,
Walahi ba adini bane aman muna rike da su da karfin gaske, kuma ko Ayya ba zata bari ka taka su ba, ta fada tana son kauce dubansa dan ba zata iya ba,
Wardugu ya yi murmushi ya nunota da yatsarsa manuniya ya ce” Baki da kunya Walyn, Ayyata kike nufi? Wace kika raina,
Walyn ta ce ” ni ban raina Ayya ba, ba zan taba iya rainata ba.