BAK’A CE Page 51 to 60

Kansa ya girgiza ya sauke kafarsa ya tsaya gabanta ya ce” kin san me? Nifa da a tsarina babu maganar na auri macen da ta furtan kalmar so , gaskiya wayewata bata barina gannin matar nan a mace, kema kin shigeni da yawa ne
Kin gane, ina son mace mai aji , wace ta san kanta,
Walyn ta mike ta ce” ai koda ni na fara cewa ina sonka kaima daga baya kace kana so na,,
Wardugu walahi in dai ina raye ba kai ba wata mace a duniya sai ni,
Wardugu ya yi murmushi yana kallon yanda take girgiza ita ga marar kunya, kansa ya kada ya shiga cire rigarsa ya ce” je ki,
Walyn ta dube shi, ta je fa?
Wardugu da ya gama balewa ya juyo yana dubanta tana dubansa ya ce” ki tafi.
Walyn ta ce” aman ka san idan na fita yanzu za.a rufeni ne ko? Dan umarninka ne,
Wardugu ya daga kafada ya ce” eh ki je,
Ido ta shiga kikiftawa tana dubansa, matsowa ta yi tana dubansa ta ce” Wardugu, shin baka san ciwona bane? Ai ko albarkacin cikinka dake jikina sai ka sasauta mini,
Wardugu ya buga wayarsa dake hannunsa da kasa ya yi taku biyu ya shaketa ya kaita jikin bangon dakin ya hadeta ya firfito mata idannuwansa baki daya ya daga murya ya ce” bayan wanda kika zubar? Ke daba baki da hankali? Kina tunanin zan aureki na sakeki sakaka kina yawo tamkar tinkiya? Du motsinki, du abubuwan da kike ina sane da ke, wada ta nuna maki hanyar zubar da cikin tana rufe, ke da kika zubar ba sai na kara kwonciya da ke ba bale ki kara daukan cikin? Walyn kauce maki nake kina biyo ni a filin rashin mutunci? Kin manta waye ni? Halaya basa sakewa sai dai a sada kai dan kunya! Ke taraki nake, bana son ki ga ranar da zan dago ki, kike ikirarin aure? Toh bari ki ji ba.a yi ba ba za.a yi ba macen da zata dora min dokar ba zan kara aure ba tunda ba dokar Allah bace,
Zan dauki yan aiki mata a gidana daga gobe tunda ke baki san ana daga maki kafa ba, yan mata zan kula na ga me zaki yi? Walyn ikirarinki ki soke ki kashe ko? Ni da ke za.a ga ainahin asalin batube, zamu gwada sokewar!
Cikata ya yi ta zube wajen tamkar mataciya tana jan numfashi ya dauki ky din motarsa da carte dinsa ya fice a dakin ya yi tafiarsa
Wakyn kam suma ta yi na dan lokaci kafin take dawowa hayacinta,
Ta jima kwonce kafin take janyo numfashi ta zabura tana zaro ido tana neman inda yake, hannayenta biyu ta dora saman kanta , ya sani? Ya san na zubda cikin? Ya sani? Wayo na shiga uku,
Da kyar ta iya rarumar ky dinta tana dingisawa ta fito ta shiga motarta ta tayar tana tafe tana labe labe har ta karasa gidansu
Wardugu kam a nan cikin mota ya kwana idonsa biyu yana duban titi, da safe bayan ya dawo daga masalaci ya shiga motarsa ya tayar, kokarin harbata titi yake ya dan yi tsai ya afka tunani:
Tun yana can aka turo masa bayanin an maidota asibiti tana zubar da jini,
Doctern da ya dubata aka turawa wardugu numbersa, nan yake shaida masa maganin zubar da ciki ta sha,
A hankali Wardugu ya binkita ya gane da wa da wa ta yi mu.amala har aka gano masa wanda ta kaita da wanda ya siyar mata,
Su duka aka rufe ita kuwa ya yi murmushi cewar zata gaje kurenta, daga lokacin ne ma ya kara daukar niyar sai ya kara aure koda zata mutu, kuma ba zai saketa ba su je zuwa tunda har shi zata zubar da cikinsa dan wani shirme nata na kar ta haihu da wuri ya kara aure? Zai kula matan ya ga wanda zai hana shi!,
Kansa ya girgiza a zaune a motarnan, yaushema aka yi aurensa da Walyn? Yarinyar da ta nuna masa zata rayu da shi komai bakin halinsa? Ta shanye wulakancinsa? Yanzu ta zame masa fitinaniya? Shi kam baya ra.ayin sakinta, da zata gyara halayenta ma zai rayu da ita a haka, aman ba zai daina kudirinsa na aure ba.
To wa zaka aura? Ya yiwa kansa tambayar nan,
Basma? , ko cikin sauran yan matan? Ko zuwa kake ka samu wata yar liman ka aura?
Murmushi ya yi gannin du sai ture shawarwarin zuciyarsa ke yi, a fili ya furta” ke ki nutsu, *wada kike hange ba zai yiwu ba, domin ko ba ransa ta taba zama tasa*
(Toh Fa)
Sai wajen karfe goma na safe Ayya ta shiga dakin Agaishat,
Zaune ta sameta tana kallon waje guda,
Ayya ta karasa ta zauna kusa da ita,
Hannunta ta kamo tana dubanta , da dukan kulawa ta ce” Agaishat, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki barwa Allah kin ji? Bana tunnanin saka lamarinnan a rai zai saka ki ji sanyi, ki dauka lokacin mutuwar aurenki ne ya yi ba dan wani mugun halaya ko wani abin ba, ki roki Allah ya maye maki gurbinsa da wanda ya fi zama alkhairi , ki yafe min kin ji?
Agaishat ta matsa ta dora kanta a cinyar Ayya, murya na rawa ta ce” Ayya ba abinda kikai min, na tsorata sosai da jin wai ya sake ni, Ayya na yi tir da rashin ilimina, da zan samu na je makaranta da na ji dadi, dan bana son a sake maimaita min abinda akai min Ayya, ashe zaune nake gidan mutumen da ya sake ni? Kuma ya kasa dubana ya fada min ya sake ni? Me na yi da zafi haka? Wannan lamari ya girgizani Ayya,
Ayya ta lumshe ido tana shafa kan Agaishat ta ce” in sha Allah, da aljihuna, da lokacina zasu kare a kanki har sai kin samu ilimi, fatana ki yi hakuri , ki daina damuwa,
Agaishat ta kara kwontar da kanta tana jin wasu hawaye masu dumi na gangaro mata daga gurbin idannuwanta, ba zata so ta rayu kamar mahaifiyarta ba, ka zama tamkar abin wasan namiji? Ai matayenku ba takalmanku ba aka ce, abokan rayuwarku ne, idan dadi bai hadata da miji ba, ba zata so ta yi rayuwar wulakanci da shi ba.
Paris
Yau kwana na uku kennan Mu.azam baya gannin Wardugu ba kuma ya gannin Agaishat sun zo ganninsa sai Marahutt dake nan wanda shima yace zai juya a gobe tunda jikin da sauki,
Ya tambayi khadija sai dai gargadin likita ya saka bata ce masa komai ba, daga nan ya gane kawai Wardugu ya ga sakonsa.
Marahutt dake tsaye kan lamarin Mu.azam khadija ta fada masa komai, ya ji ba dadi sosai abinda Mu.azam din yayi, aman ya yi masa uzuri da jiran jin bayaninsa ta waya dan juyawa zai yi gida
Mu.azam ya birkicewa Khadija sai da ta bashi wayarsa , nan ya yi ta gwada kiran number Wardugu aman amsar daya ce ba zai same shi ba.
Abinda ba.a so din ne dan kuwa ya fara tada hankalinsa , dan ya kasa samun nutsuwa dalilin rasa Wardugu har kansa ya fara ciwo
Hakan ya daga hankalin su Marahutt dan haka ya shirya ya juya gida, wato niger
Direct office din Wardugu ya je, nan ya same shi yana cikin aiki,
Kamar yanda ya saba hawo shi kai tsaye , yanzun ma kai tsayan ya hau shi inda ya dana vidio call ya ajiye masa ya fice a office din,
Kaĺlon junna suke ,
A hankali Mu.azam ya ce” ka yafe mini War, ka yafe mini na roke ka,
Wardugu bai bashi amsa ba sai kallonshi da yake
Mu.azam ya ce” ya kake so na rayu da macen da ka fini son ta?
Wardugu ya mike tsaye yana dubansa kafin cikin karaji ya ce” *Ni na fada maka ina son ta?* *a ina muka taba yi da kai cewar ina son ta?*
????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣2️⃣