BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 51 to 60

Ka kasance mai zama da mutun da zuciya daya, na yi imanin koda wani ya zo rayuwarka dan ya cutar da kai Allah zai kare ka????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Mu.azam ya rintse ido dan harga Allah baya son yannayin wardugu na fushi, shi walahi tsoronsa yake, 

Tausasa murya ya yi ya ce” Wardugu nine fa? Ni ne Mu.azam, 

Idan kaine Mu.azam sai aka yi yaya? Ko an fada maka dan kai ne Mu.azam shikennan ka san ko ni wanene? Harma ka san abinda yake raina ko me? 

Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa, a hankali ya ce” ka yafe mini, 

Wardugu ya daki table din gabansa da hannunsa ya nuna wayar ya ce” dan ka san kana cikin halin rashin lafia ka yi min wannan gangancin?

Mu.azam baka da huja, hujarka bata da wani ma.ana, ya zaka saki yarinyar da na je na karbo amanar aurenta wajen iyayenta a gabanka wai kan wata banzar hujarka ni Wardugu ina son ta?,

Mu.azam ya yi shiru yana duban wayar,

Wardugu ya dan rage ihun bacin ran aman muryarsa a kausashe ya ce” dan kana da wace kake so ka wulakanta mini ita? 

Mu.azam ya kwararo ido da mamaki, 

Wardugu bai barshi ya ce wani abu ba ya ci gaba” Mu.azam ka san irin halin da na tsinci kaina na irin kukan da ta ringa gumzawa a kanka?

 Bakai min adalci ba, baka rike min amana ba, kai ka isa ka yi hukunci ne? Kan zaton da kake?a abinda ka yi hasashe? Ko akoy wanda zai fito yace na taba fada masa ina son ta ?

Mu.azam ya talafe habarsa da hannunsa na dama yana yiwa Khadija alama da kar ta leko wayar, (????),

Wardugu ya juya ya juyo ya tsare shi da jajayen idannuwansa ya ce”

Yau koda hakan ne, koda ace wai na taba soyaya da ita bama maganar ana tunanin ina sonta ba, Mu.azam aure? Aure abin wasa ne? Da ace ita ta fito maka da hanyoyin da suka girgizaka , da ace ita ta nuna maka kiyaya da idan ka saketa da hujar bata sonka ba zaka iya zama da ita ba hankalina zai dauka, aman Mu.azam ka saka mini ita ta yi ta kuka? Wanda yau kwana hudu tunda na ajiyeta ban koma ba dan ban san shin ta daina kukan rashinka ba ko bata daina ba? Ni kadai nake da alhakin sakata kuka, daga lokacin da na karbo amanarta wajen mahaifiyarta ta zama abin karewana ta gaske,

Ba zan lamunta ba, ba zan iya kawar da kaina daga du wani wanda zai sakata zubar da hawaye ba!

Yana kai karshe ya datse kiran ya zauna yana saka hannunsa cikin sumar kansa,

Marahut dake daf da kofar office din, kasancewar murya dage Wardugu ya yi magana da Mu.azam ba abinda bai ji ba,

Ido ya kurawa kofar, kafin yakr kada kai ya juya ba tare da ya shiga daukar wayarsa ba, dan ya tabata idan ya shiga a haka zasu kara hawa sama ne, dan ransa a bace, kansa ya girgiza yana adu.ar Allah ya shiryi wardugu da zuciya, kuma abu gashi zahiri sai ya take sai ya ji jiki ya lalubi mutun.

Yau kwananta daya a gidan Ayya,

Tunda ta je wajen mahaifiyarta ta kora mata bayani , uwar ta buga ta buga suka ga basu da hanyar bi da ta wuce su je wajen mahaifiyarsa dan sun tabata itace kawai ke zabga masa mari ya sada kai, ta tankwasa shi ya yi koda baya so,

Ayya ta sha mamakin ganninsu, sai dai da ta ji abinda ke tafe da su, domin mahaifiyar Walyn nunawa ta yi ta zo da gaskiya dan a gaban Ayya har marin Walyn ta yi tana fadin irin gangancin da ta yi na zubar da ciki, da kukanta daa komai take rokar Ayya ta ji kanta ta kama mata, harda fadin yayan zamani ne ka haife su baka haifi halinsu ba,

Sosai ta nuna bacin ranta na irin halayan Walyn duka Ayya na kallonta,

Ayya bata da yanda zata yi, na farko dai ita ta yi imanin idan da zuciya biyu ne Allah zai iya masu, na biyu ko ba komai ta ji dadin ashe matar dan nata ta san bata kyautawa ? Duda bata nemeta ba sai a yanzu da take gannin ta masa madaukakin laifi? Na uku gaskiya ne, yayan yanzu sunna abubuwa ne gabam kansu, ba zata so a saki yar wani ba dan an saki tata bata ji dadi ba, a gaskiya sakin da akaiwa Agaishat ta ji shi har cikin ranta, dan haka ta amince ta zauna nan gidanta na dan lokaci har ta iya da lamarin Wardugu sai ta koma dakinta,

Duda ba haka suka so ba, sun so ne ta yi kiransa a lokacin ta bashi umarni, aman sai suka hakura dan matakin da suka taka na neman galaba kar ya kubuce masu,

Dalilin da ya saka Walyn ke zaune a gidan Ayya yau kwana biyu, inda take cikin dakin da yake na Mu.azam, domin dakin Wardugu daman Agaishat ta zaune shi ,

Tana zaune a gidan ne ba tare da shiga sabgar kowa ba, idan lokacin cin abinci ya yi mai aiki zata je ta fada mata, wani lokacin ta fito a ci da ita inda tana ci tana dana waya, wani lokacin kuwa tace bata ci sai sun gama ci ta zo ta diba ta ci,

Sai abinda ke bata mamaki irin yanda yarinyar nan yar kauye da suka dauko ta zama, duka dukama wani lokaci ta dauka a gidan? Aman cikin ikon Allah yarinyar ta wanku ta zama wata big girls irin yayan yan gayun nan, komanta irin na yan gayu ne, ita tambayace cike da cikinta, ba ita bace Mu.azam ya aura? To ina Mu.azam din? Duda tana yawan zama da doguwar riga da dan kwalinta a kanta, bata wani harkar samari dan Ayya na kilaceta wai ida take, sai karatu da aka daukar mata malamar makaranta dake zuwa tana koyar da ita sau biyu a wuni dan Agaishat dai ba komai take yi ba, ita kuwa malamar apbashin koyar da agaishat din yama fi na wanda ake biyanta a makaranta , dan haka ta rike damarta take aikinta da zuciya daya inda suke bi a hankali suna karatun su,

Ba abinda ke hada su , dan walyn bata taba zuwa ta tarar da Agaishat zaune ta nuna ta san da mutun a wajen ko ta yi kata salama ba, itama Agaishat ta gwada gaisheta sau uku aman Walyn bata amsawa dan haka sai ta kama kanta, domin wani yatsina fuska Walyn take idan ta ganta, wai yar kauye ta samu waje,

Zaune suke a fali, Ayya na saman kujera baba inda Agaishat ke zaune kasa da litafi a hannunta tana bitar hada sunna tana karantawa a hankali Ayya na gyara mata wajen gyarawa,

              Bayan sati biyu

Fitowa ta yi ta sha shada tana baza kamshi ta dan tsaya nesa da su Ayya kadan ta ce” Ayya, zan je wajen auren kawar tawa,

Ayya ta dago tana dubanta, ta so ta share ta tafin, sai dai fa tunanin yanzu fa a wuyanta take ya saka ta ce” bari na fadawa mijinki,

Wayarta ta saka Agaishat ta dauko mata domin wayar a kashe take wajen sati biyu kennan dan kara nunawa Wardugu tsananin fushin da take ciki,

 Agaishat ta mike yau kuma da yake ta san ba wani namijin dake shigo masu iya su ne, dogon wando ne jikinta mai dan santsi sannan daga kasa da irin igiyar nan ta daure kasan da shi, bai kamata ba aman ya bi shap din jikinta, sai fara kar din riga body wace bata da kwaliyar komai jikinta, sai dan kwali karami da ta yane gaban goshinta da shi , idan ka ganta kamar irin beautiful din balck americain din nan, ga kamshin turaran wankanta mai karawa fata santsi da take bazawa du idan ta gita,

Da ido Walyn ta bita kafin take yatsina fuska, kamar tace a barshi kar a yi kiransa dan bata so, ko da wasa bata shirya tarbansa a yanzu yanzu ba, ita gaba ta kaita rashin zuwansa gidan, da farko a dari dari take daga baya ta sake abinta take lamuranta hankali kwonce , ba abinda ta nema ta rasa, dan haka ta kwontar da hankalinta ta san dai ko ba jima zai nemeta tunda bai saketa ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button