BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 51 to 60

Kafinma Agaishat ta dawo da wayar karan dankareren babur din nan nasa ya isar da zuwansa gidan,

Wani irin juyawa Walyn ta yi wajen kofar gabanta na faduwa da wani irin sauti da cikinta ya bada, Wardugu ne a gidan warhaka?

Ai bata san lokacin da ta cire dogon takalmin nata ta jefar nan bayan kujerar Ayya ta yi sauri ta karasa saman cafet ta zauna ba saman kujera ba,

Ayya dake binta da kallo ta dago sukai ido hudu, wata kunya ta ji ta kamata, tunda suke bata taba zama a kasa Ayya ta zauna a sama a matsayinta na wace ta girmeta bale a je ga maganar sirikarta, zama take duwaiwanta da nata ba abinda ya shafeta aman yanzu da ta ji motsin Wardugu ta zo da gudu ta zauna a kasa,

Murmushi Ayya ta yi tana waiwayawa dan jin tafiar Agaishat wato ta dauko wayar,

Tana saukowa shi kuwa yana shigowa, 

Matatakalar ba a saitin kofar shigowar take ba aman dan fitina idannuwansa suka hasko masa ita ta cikin bakin gilashin da ya saka,

Kara kicin kicin ya yi da fuska ya maido dubansa wajen Ayya wace itama ta hade fuska inda Agaishat ta juya da gudu ta koma dan saka hijab

Harga Allah bai ga Walyn ba, domin tunaninsa ba zai taba kawo masa wai Walyn na zaune a gidansu ba, sannan Walyn a kasa a zaune? Bai kawowa ransa haka ba, dan haka ya karasa kujerar dake facing din Ayya ya zauna yana kallon Fuskar Ayya, a ransa ya ayyana bata huce ba dai,

Murmushi ya yi kafin ya ce” Maman Wardugu barka da yama,

Ayya ta zabga masa harara kafin ta ce” ni zaka gaisar da gilash?

Cire gilash din ya yi wanda ya saka ta ga idannuwansa sun yi ja, ko na meye oho?

Wardugu na cirewa ya ce” ina son Ayyana ????????

Ayya ta yatsina baki tana duban Walyn, hakan da ta yi ya saka shi duban inda take kallo,

Zoben hannunta na zinari ya toni ko wacece domin shi ya sayi zoben,,

Juyar da kansa ya yi tamkar bai gane wacece ba, kamarma bai ga wanda ke zaune ba,

Ayya ta girgiza kanta dan sarai ta san ya gane ko waye aman ya wani basar,

Ayya ta ce” kai, mace na karkashinka aman bata gidanka tsayin wannan lokacin baka bibiyi inda take ba? Kana da lafia kuwa Wardugu?

Wardugu ya kaleta irin kallon nan na tsai, murmushi ya yi ,

Ayya ta ce” wani ahu ta yi maka ne?

Wardugu ya girgiza kai bai yi magana ba,

Ayya ta ce” Wardugu ka min magana mana ko kurma ka zama?

Wardugu ya yi murmushi dan kuwa ko ba komai yanda ta masa magana haka ya ji dadi, dan haka ya ce” wace matata?

Ayya ta kale shi inda Walyn ta dago da sauri itama tana dubansa, 

Ayya ta hade fuska ta ce” ka dauki matarka ku koma gidanku , koma me ta yi ka yi hakuri , 

Wardugu ya dago da sauri ya ce” Ayya?

Ayya ta hade fuska ta kawar da kanta ta ce” na ce ka yi hakuri.

Wardugu ya dan matso bakin kujerar,

Hannunsa mai dauke da zoben azurfa ya dago a hankali ya shafo kansa zuwa sajensa,, ya yi haka sau wajen biyu kafin yake dan dagowa ya kalli Ayya, itama shi take kallo sannan da idannuwanta ta nuna masa da ya bi umarninta,

Wani murmushi mai ciwo ya sakar mata kafin yake dan muzgutawa ya koma cikin kujerar ya zauna , 

Ayya ta dubi wajen Walyn dake zaune ta ce” ki tashi ki koma dakinki, ki kiyaye dukan abinda mahaifiyarki ta fada

Mikewa ta yi zurbat ta dan sosa kanta tana duban Ayya, aman batai masa gargadin kar ya mata wani abin ko ya daina fushin da yake da ita ba,

Sai dai ba halin ta kawo maganar domin ko a fuskar Ayyan bata ga fuska ba,

Dan haka ta samu ta raba Ayya ta fice da sauri ta shiga motarta ta nufi gidanta.

Tana fita Ayya ta maido hankalinta wajensa tana dubansa, ta sani sarai shirunnan da ya yi gwara ya yi magana, aman sai ta share, idan tana son tankwasa shi bata nuna wani tausayi ko tsoron zuciya, 

Rai ta hade ta ce” an yi maka laifi mai girma, ka yi hakuri , kar ka ci gaba da nuna mata wani abin, ka kwontar da hankalinka, dukan tsanani yana tare da sauki.

Idannuwansa ya lumshe ya kai dubansa wajen matatakalar Ayya, kansa ya juyo yana duban Ayya ya ce” alfarma faya nake nema a wajenki Ayyana,

Ayya dake dubansa ta ce” wace alfarma ce?

Idan na tashi neman aure , ina so tsakanina da ke ki sanya mani albarka, ba ruwanki da maganar wani al.adu da me za.a dube ki, Ayya bafa adini bane, dan na taka ba Allah zai kama ni ba, ba kuma wani zqi hana mini ci ko sha ba, ba wanda zai hana ni shiga inda nake so, hasalima koda za.a yi da ni sai dai a yi a boye, ki toshe kunnayenki na roke ki! 

Ayya ido kawai ta zuba masa, zata fi kowa murnar gannin wardugunta ya samu wani canji bangaren mata,

Ya kasance mai farin jinnin mata, suna likun masa a duk inda ya saka kafarsa, sai dai abin takaicin cikin matan nan wa.inda ya samu wani kusanci da su du sun saka ya ji dan damanma, har yanaiwa mata kallon zuma daga nesa, idan suka karaso gareka sun zama madaci,

Me ya rasa? Ya kasance namiji har namiji sai dai ya rasa macen mutunci,

Ya mace zata zubar da cikinka wai a zuwan ba zata haihu da wuri da kai ba dan tana maka tsananin son da ba zata so ka auri wata ba?

Ta iya zubar da gudan jininta, dan sunna dan tsaninin kishi ya zata dauki lamarin zaka auri wata?

Danma a haka wai tana shayinsa, du haukanta tama tsoron su hade daga ita sai shi idan ta yi masa laifi, aman lamarinta na saka Ayya a shakun jin wai wardugu zai dubi wata bare ya aureta,

Sai dai ina, ba zata shiga hakinsa ba , ba zata shiga ba, ya isa haka, harda laifinta irin yanda take tsawata masa idan ya dace ya hukuntata, ta samu damar da take sakawa ranta ita daya kwal ta ishe shi ko kowa ya rasa,

Ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da kanta, zatai ta adu.a, aman ko wacece zai aura zata hadu da fitinar matarsa sai dai idan ita dinma wata kwaron kanta ce!

           Gidan su Anna

Tunda suka sauka a gidan su Anna ba rajar banza da ba za.a yi baki ba, sun zo yi masu barkar gannin y’arsu,

Abin har mamaki yake baiwa su Gaishata, sai dai duba da irin mukami da datijantakar tsohon gidan ya tarawa kansa daraja,

Wani abu dake baiwa gaishata mamaki, shi ne irin kirarin da ake yiwa mahaifiyar Anna, 

Sai dai zaman da ta yi da ita na dan lokacin nan ya saka ta gane ba wai likawa aka yi ba, ta cancanci hakan ne,

Ita bata taba gannin mace irinta ba, a duniya duda tsufan da ya kamata ko me take, ko da wa take, mijin nan nata yana gaba da komai,

Wato wani irin kulawa, wani irin cancanna, wani irin salo da take bazawa a cikin gidan ba ruwanta da jikokinta ki yayanta ko wasu sirikai, ta iya tafia da mijinta a gaban kowa, kuma cikin ikon Allah du irin zafinsa idan ya kwashi zafi ya fice zatai murmushi ne idan ya je ya dawo ta bi bayansa zai fito kamar ba shi ba,

Har wani kirari take masa namijin mazaje ja gaban Hatimi aban Herde da Allatchi,

Zaka ga yana wani kayatancen murmushi,

Ko yanzu gaba ta saka Gaishata bayan ta gama lumdarta da turare, domin ita ke kula da harkar wankan jegonta koda yaushe tana daka tana lumdeta da shan zafin daki ta dubeta ta ce” ni kishiyoyinki nawa?

Gaishata ta ce” biyu,

Yara ne suma kamarki ko sun manyanta?

Gaishata ta ce” dayar na fita, dayar kuma ta manyanta,

Hatimi ta gyada kanta ta mike ta dauko wani kindirmo da ta dada ta zuba wani ruwan itace da ta dafa da kanta ta bata ta ce” ya mu.amalarki da su? Irin zumunta? 

Gaishata ta ce” a gaskiya bama fada kuma bama shiga harkar juna, 

Hatimi ta ce” me yasa bakwa shiga harkar juna? Kina nufin a cikin gida daya kuke aman ba ruwan kowa da kowa? Irin rayuwar idan wani na cikin wani hali ma ba ruwan dan uwansa da shi?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button