BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Kakarsu tana cikin koya masu wanka na yayan gayu da suka jiku a cikin gayu, 

An koya masu mota, su ke zuwa alimentation siyayar kayan kicin da na frij, suna koyan su cake da sauransu, 

Anna ta murje, ta murje ta faso, Anna bata magana daya biyu ba tare da ta jefa turanci wato inglish a ciki ba domin makarantar da ta yi ana koya masu yaran ne duka biyu a tare,

Rayuwarta na da ya dawo, ta dawo cikakiyar yar birni mai wayayen kai da iya tafiar da rayuwarta a nitse ba da hayaniya ba,

Takan shiga damuwar rashin labarin Agaishat, sai dai hankalinta na kwonciya idan ta tuna ai ta bada aurenta tana dakin mijinta kuma ko ba dade ko ba jima zata neme su fatanta dai Allah ya sa tana cikin rayuwa mai nagarta a gidanta,

Sai maganar Algabitt da suke jiran bilowarsa dan abinda ya tsaye masu a rai ya sakar masu y’a !

             Timiya,

Sarki ya kada , ya raya, yana so ta janye maganarta aman fir ta rikice masa kan walahi ita magana daya ce tana so a fitar mata da hakinta a matsayinta na yar gari wace take da inci a kan wanda ya cuta mata,

Ya so su yi lamarin a sirri aman ta kiya ita kawai a yi masu shari.a da Algabitt dake rufe a matsayin mai dauke da laifi mai girma a gidan sarki,

Garin ba wanda bai san halin da ake ciki ba dan haka kananun magangannu ke yawo cewar za.a ga idan sarki zai hukunta sirikinsa bisa laifin da ya yi, idannuwa dai a kansa wanda hakan ya saka dole ya fitar da shari.ar fada,

Komai na son sirri, abinda ya yi ta nanatawa Gaishata dake kukan wannan lamari,

           Gigirigin kennan ranar fadin gaskiya,

Tare wajen yake dankam, cike da jama.a, an taru an cika an yi makil abinka da kauye kowa ya zo ya ga kwaf,

Sarki zaune ya hakimce da rawaninsa na turkudi, gefe da gefensa du dogarai ne da yaran gidan sarki, 

Sarkin bulala tsaye yana dan kadata lokaci zuwa lokaci,

Gefe guda matan sarki ne laye cikin shiga ta alfarma kowace na isa da kanta a matsayin na matar mai garin timiya,

Gaishatama zaune take ta sha turkudinta mai kala biyu blue da maroon an yi mata dinkin zamani ta rufa da katon mayafi hannayenta dauke da warwarayen zinari , ba yara a wajen domin ko yayansu a gida a aka bar su ,

Dayan gefen kuwa Algabiittt ne ke zaune shima yana ta kale kale alamomin rashin gaskiya sun bayana a tare da shi,

Gayaran murya sarki ya yi kafin ya ce” kamar yanda Timiya yake karamin gari mai dauke da sarki ni Ibrahim Asadeek, timiya ta kasance garin da talakanta ke da inci, muna zakulo du wanda ke tayar da zaune tsaye mu hukunta shi bisa tsarin adini,

Dogarai sai amsa shi suke kafin ya ci gaba da fadin” a yau , mun zauna a wannan waje dan tuhumar Malan agabitt kan manyan laifuka da muke tuhumarsa da su wa.inda matar da yake zaune da ita ta shigar da karar tun kafin ta bar gari , yanzu da bata nan bisa madadinta ga y’arta wato gimbiya gaishata , muna masu umartar Algabiit da ya bayana mana haduwarsa da mahaifiyar yayansa, dalilin da ya saka ya yi rayuwar wulakanci da ita….

Shiru ya yi yana kifta ido ya ki yin magana,

Ajiyar zuciya Sarki ya sauke kafin ya ce” idan har mai laifin ya yi gardama, kadarorinsa na gida da gonarsa da ake yi masa noma za.a karbe sannan ya fuskanci hukunci mai tsanani,

Ido ya zaro yana duban Sarki, shi bashi da damuwar wai mutanen wajen su ji abinda ya aikata, shi damuwarsa hangen daya daga cikin wa.inda suka bashi kudaden su Mariama da ya yi, ya tabata idan sarki ya kore ahi daga Timiya ya kade, dan haka ya gyara rawanin kansa ya shiga bada labari kamar yanda Anna ta bada har zuwa ranar da zai tafi da ita inda ya ce” a ranar safiya na yi na koma wajen bokana, wanda yake anguwar Talagué pays ba, ina zuwa na karbo abubuwan da na bashi ajiya domin ni ke kai masa abubuwa shima yana neman kudi da ni, inda ya dora ni a hanyar da zan hadu da yar masu kudi,

Maganin cire ne, wanda hasalij kirana daga garin haihuwana wato tanut dan ina yawan ciren yayansu,

Dakatar da shi aka yi ta hanyar tambayar menene cire?

Dago da kansa ya yi ya ce” Cire, wani asiri ne da fulanin daji ke yi , wanda na gada wajen kakana na wajen mahaifiyata dan shi filo ne, cire asiri ne da idan aka yiwa mace take bin namiji , bata da wani ra.ayi nata sai nashi, 

Na hada da cire da asirin da bokan ya samo wajen wani bokansa dan dogon dutsi cewar idan na aikata idona idonta an kare zata bi ni ne du inda zan je, kuma ko me zan mata ba zata iya barina ba dan zatana jin tsoron zuciyata da bacin raina , sai dai kar na yarda ni da bakina na ambata mata sunnan garin su , ko sunnanta na asali, ko na yan uwanta, in dai ba ni na fada ba koma wa zai fada sai dai ya shiga tunani kamar ta san abin aman ta watsar daga baya dan zai tayar mata da hankali sosai

Na ci sa.a na cireta, muka fice a gidan daidai salar azahar muka dauki hanya da kudaden jakarta inda na yi wurgi da wayarta muka dauki yawon duniya,

Masalatai sun fi a kirga na je dan a aura mana aure, aman sai su ce koda bamu da kowa a duniya sai sun yi magana daga su sai ita, daya na amince sun fara maganar na ga sai wani tambayoyi yake yana faman tona asirina na bige shi da sadanta na dauketa muka kara shiga yawon duniya kafin daga baya na yada zango a nan,

Zufa ce ta shiga karyowa Gaishata, sarki kansa ji ya yi lumfashi na neman gagararsa,

Gaishat bata san lokacin da ta ce” kana nufin ba.a daura aurenka da matarka tsawon zaman da ka yi da ita harda hayayafa ba?????

           To fa

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          6️⃣8️⃣

             Asalamu alaikum

*Allah ya kawo mu wata mai albarka, banban wata mai tare da lada ,wata mai cinye zunubi, RAMADAN, ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA TARE DA WASILA DA FARILLAH A ALJANAR FIRDAUS Allah ka jikan magabatan mu, ka sa sun huta, idan tamu ta zo ka sa mu cika da imani ka sa mu tarda alkhairi ???????????????????????????????????????? Ya Allah, muna rokon ka, ka shirye mu, ka inta mu, ya ubangiji ka yafe mana zunubanmu, Allah ka hane mu saba maka,Ya Allah ka dora mu a hanyar bautarka, ka karbi ibadunmu, Ya Allah ka sa mu bayansa lafia ka maimaita mana, ni sajida ina mai yi mana fatan Alkhairi da fatan Allah ya kai.mu rai da lafia bayan sallah*

Algabitt ya dago da dubansa ya sauke kan Gaishata dake wani irin numfarfashi gabanta na faduwa tana duban mahaifin nata,

Algabitt ya kauda kansa yana bin mutanen dake zaune daya bayan daya da ido,

Kansa ya girgiza kafin ya kai dubansa wajen sarki ya ya buda bakinsa zai yi magana sarki ya mike tsaye ya ce” ya isa, kar ka fadi komai,

Muryar uwar gidansa ne ta ce ” sarkina, talakawa na zaune suna jiran hukunci,

Amaryarsa ce ta gyara zama ta saki murmushi ta ce” sarkina, muna masu neman alfarmar a yi hukunci yanda aka saba yiwa sauran talakawa,

Gaishata dake bin su da kallo su duka biyu ta maido dubanta wajen Sarki da ya tsurawa matan nasa ido cike da takaici,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button