BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Gaishata ta share hawayenta ta sada kanta kasa,

Sarki ya koma ya zauna yana duban dogarai dake muzurai , sun so su tsawatarwa da matan sarki sai dai gannin matan sarkin ne tsoro ya hana su su yi masu magana domin ba wanda yake da hurumin yin magana idan sarki da kansa na shari.a duda kauye ne, idan baya nan akoy mai wakiltarsa ,

Hade rai ya yi ya ce” du wanda ya kara buda baki ya yi magana a wajen nan zai karbi hukunci komai kusancinsa da Sarki!

Idan Dogarai suka ga abin tsawatarwa basu tsawatarba zasu fuskanci fuahina!

Ji kake suna fadin” tuba muke sarkin talakawa,

Sarki ya maida hankalinsa wajen Algabittt ya ce” tabas ka kasance mutun mai son kansa, ka yi rayuwa bisa umarnin zuciyarka, tabas munada muradin jin bukatar wace aka fi cuta duda ta bada amanar yarta ta wakilce ta, dan haka zamu iya sauraron zuwanta ko maganarta a waya, 

Magana yake hankalinsa ba a kwonce ba domin tunda Gaishata ta sada kanta bata dago ba, 

Mikewa ya yi ya danna kira kan number Gukunni ,

Bayani ya kora masa na komai cikin nutsuwa , yana gamawa Gukunni ya tarda matarsa da y’arsa, cikin hikima ta manya ya zayane masu komai wanda ya saka Anna fashewa da wani irin kuka har tana dukewa tana dafe cikinta da dukan hannayenta,

Mahaifiyarta dake kuka itama tana duban jikokin nata da suka dora hannayensu saman kansu sun kasa magana tsabar shiga firgici da tashin hankalin jin wai su din ashema ga ta hanyar da aka same su duniya ta kawar da kanta wajen mijinta dake zaune sai zufa yake ta rintse idannuwanta zafafan hawaye suka zubo mata ta bude murya ta ce” na haifi Allacthi ta hanya mai kyau wace Allah ya nufe ni, 

Ban bi kowa ba, haka mahaifinta ya kasance mai kiyaye wannan lamari, 

Wannan kadara ce mai girma wace ta girmi tunanina,

Tabas na zama wawa a wannan lamari,

Shin wa zan kaiwa kuka a nan gidan duniya?

Yau du abinda za.a yiwa wannan bawa in dai ba dawo da shekaru baya za.a yi ba a dawowa da y’ata martabarta bana tunanin zan ji zuciyata wasai,

Yau ko yikuwa na cakawa wannan mutun ban goge komai ba,

Idan rufe shi aka yi ma ba.a dawo baya ba,

Wai wai wai ni Herde wai rayuwa Hamdulilah, Allah na gode maka, 

Gukunni, dan Allah ka yi kiran wannan yaron ka fada masa ni nace dan Allah ya saki wannan mutumin da ba zan so maimaita sunansa ba,

Ya bar shi, *wata shari.ar sai a lahira*,

Tana fada tana ta share hawayenta ne tana kula da irin yanda Anna ta dafe zuciya tana gumurzun kuka,

Wajenta ta nufa dan ta lura Gukunni sauraronta kawai yake, 

Kama Anna ta yi ta kwontar da ita ta dubi Mariama,

Hade fuska ta yi danma kar su daga mata hankali ta ce” ke maza je ki yi kiran docter Aliyu, maza ya zo ina jiransa,

Maida dubanta ta yi wajen Gukunni ta ce” ba zai ga bayan farin cikin gidanna ba, ba zan yarda wani katon gardin dan kauye saka baki a rayuwar da ta doso ni mai tsananin haske,

Zan so na ga jarumtar ka a wannan lamari Gukunni? Zan so na ga dauriyarka, ka kama mani kar na rasa y’ata, sannan ka fadawa Ibrahim Asadeek cewa idan ya ga zama da Gaishata wani damuwa ne, ya dawo min da ita da yaronta,

Gukunni dake zaune yana dubansu ya mike ya fice a gidan ,

Zuwa ya yi aeroport neman jirgin da zai kai shi agadez domin mai tuka nasa jirgin yana hutu ba zai so takura shi ba,

Sai dai ina ba jirgin agadez kwata kwata a ranar, dan haka da kansa ya tuka mota zuwa gidan yaron nasa soja kuma matukin jirgi ya je masa ya fada masa bukatarsa inda ya baiwa matarsa hakuri cewar idan har sun kwana hali ne ya kama babu niyar hakan!

Abinka da manya masu garin, haka suka zarce inda ya yi kira ya nemi alfarmar zai tashi da jirgi tafiar gagawa abinda ya shafi familynsa domin koda kana da jirginka ba kyau tashi lokacin da ka yi niya sai an baka izini

 

Basu wani sauka a Agadez ba, tafia suka yi mai dan tsayi sai garin timiya inda ya yi ta shawagi dan samu wajen sauka wajen da ba rere da kuma duwatsu, sannan wajen da idan zai tashi zai samu dan hanyar tafia kafin ya cira,

Da kyar dai , da kyar ya samu wajen da ya nuna masa zai iya sauka, inda yara tuni suka fito baki bude sunna kallon wannan abu mai kara mai ficewa can sama yau yana yin kasa kasa cikin gari, hakan ya saka wasu firgita da tsoron fadowa zai yi ya kashe su, 

Inda wannan lamari ya ja hankalin mutanen fada da suka ki watsewa du suka dugunzuma zuwa gannin abinda ke faruwa kuma, 

Dole sarki ne zai je gaba , dan haka ya mike ya kai dubansa wajen Gaishata dake yanda take ya juya da sauri ya tafi dan duba lamarin kauyensa inda yake tafe yana ayyana dole ya ajiye sarauta , shi kam ya kai wajen da ya ji takaicin kasancewarsa sarki, 

Suna samun tsayawa Gukunni ya mike ya fito domin ya bude masa kofa inda shi kuwa ya zauna ciki yana gyare gyare da duba idan komai lafia dokin wajen ba wajen saukar jirgi bane 

Ido Sarki ya kwalalo gannin Gukunni, 

Mutane kuwa kallon mutun da baki haka a cikin jirgi suke, daman bakima na shiga? 

Wajen sarkin ya nufa inda Algabitt ya kusan zubewa kusa da dogarin dake tsare da shi,

Ai kuwa juyawa ya yi da jiyar baiwa wandonsa iska sai dai an tare ko.ina,

Hayaniyar a sake shi ta ja hankalin Gukunni waje sa, dan haka ya saki hannun sarki da suka gaisa ya nufi wajensa yana dubansa da kyau

Yana zuwa ya tsaya gabansa inda Algabity ya zama wani cirit a gabansa,

Gukunni ya girgiza kansa, a fili ya ce” wai a gaban halita irinka kana haka ina ga ka je gaban wanda ya halice ka? Tabas ba sauran abinda zan yi shari.a a nan, 

Yana gama fada ya koma wajen sarki ya ja hannunsa gefe,

Cikin nutsuwa ya ce” ina gaishata ne?

Sarki ya sada kansa kafin ya ce” tana cikin wani hali, ba yanda ban yi da ita kan a yi shari.arnan a sirince aman ta kada kai ita sai an yita a fada, hakan ya hadasa mata tashin hankali,

Kansa ya girgiza idannuwansa da sukai ja ya ce” ka san me? Shi du abinda Allah ya hanna, ma.aiki ya kawo mana mu yi aiki da shi,

Shi tsananta bincike ba kyau, 

Yanzu wa gari ya waya? 

Sarki ya kada kai yana duban gefe da yannayin damuwa,

Gukunni ya ce” zan so ka bani ita mu je gida, idan har kana ra.ayin hakan, zan so ta je ta huta, zamu so mu hada su su duka mu yi magana da su, zan so su saurari gargadi da nasiha ta zaman da zasu yi na rayuwa,

Tanas duniya ta ci gaba aman banda wajen mata,

Wannan bakin fentin na iya hana su sukuni cikin mata yan uwansu,

Zan so ka yi min wannan alfarma,

Sarki ya gyada kansa ya ce” tabas mata suna girma aman suna cin kasa, a yanzu haka har na so soke maganar abokan zaman nata suka takalota,

Dan haka yin hakanma ba laifi bane, nima ina kan duba wani lamari na nan , zan yi shawara da tsofafi magabata in sha Allah, a taya mu da adu.a Allah ya sa abinda za.a shiga alkhairi ne

Gukunni ya amsa shi cike da farin cikin zai bashi Gaishatar da zuciya guda,

Juyawa suka yi dan shiga ciki Gukunni ya ce” ita dai dayar har yanzu ba labarinta ko?

Sarki ya ce” aa, da wasika da wanda take hannunsa ya kawo, bara na dauko wasikar ni ai na sha.afa abubuwa sun shige mini,

Juyawa ya yi cikin gidansa inda Gukunni ya karasa wajen Gaishata ya duka,

Hannunsa ya saka ya dago habarta, kir idannuwanta abude suke sannan a soye,

Sauke idannuwanta da ta yi saman fuskar kakanta ta ji bakinta ya bude, murya na rawa ta rike hannunsa ta ce” ashe mu shagu ne ba aure Algabitt ya rayu da mu? Ya zamu yi rayuwa a cikin wannan lamari? Ya zan rayu cikin kishiyoyi da kauye a haka?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button