BAK’A CE Page 61 to 70

Ya kanuna da basu samu miji ba zasu samu a irin wannan rayuwa ta yanzu? Idan Agaishana ta ji haka, ya zata dauka? Ya mijin dake aurenta zai dauka?
Gukunni ya lumshe idannuwansa ya mike ya samu ya dagata ya dubi mai aikinta ya yi mata umarnin maza a dauko sultan,
Bai bata amsa ba sai jan hannunta da ya yi suka nufi wajen jirgi inda ha baki bude aka raka su da kallo , da yawan mutanen da fadin ko dai Uban Agaisha ne? Wato Bak’A?
Nan ya tsaya jira har sarki ya fito suka kara gaisawa ya bashi takardar da Wardugu ya kawo dauke da wasikar da bai karanta ba,
Juyawa ya yi ya basu waje shi da matarsa su yi salama kafin suke dagawa,
Wajen yama tuni sun dawo garin niamey inda mai tuka shi ya ja su har gidan su,
Suna zuwa ya saka ta fice shi kuwa yana rike da Sultan dake dan wasansa na jarirai ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya daga idannuwansa sama yana kallon sararin samaniya,
Takardar nan ya bude ya duba,
Number waya ne kawai tsararu masu bin juna sai sunnan da ya zirawa ido da mamakin gannin sunnan , shin sunna ne ya zo daya haka ko kuwa shi din ne?
Wato jan gwarzon nan, yaro mai hazaka, yaron da yake ji fa shi dan aiki na yawan hada su, yaron da idan yana kallon abubuwan da ya yi a duniya har wani tsam yake ji da jin wani yannayi na shauki da jinjina masa da gannin girmansa tamkar wani datijo, yaro karami mai watsa taron yan daba, wato *WARDUGU BATUBE DAN MARAHUT*
MA.ASALAM
???????????? *BAK’A CE*
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
7️⃣0️⃣
Barkan mu da sallah jama.a,
*KUTKALE*
*Aure yakin mata ne*
*Kamarta bata da niyar cutarwa*
Kar ku bari a baku labari…..
Mikewa ta yi tsaye, nan doguwar rigar da ta saka wace ta bi jikinta ta sauka kasa ta kara ainahin fitar da surar jikinta da wani tsararen kyau mai fizga,
Lafayar ta dauko da niyar sakawa sai dai me, tana dubawa da kyau ta ga ai wannan ta ranar dinern da aka shirya ce,
Juyowa ta yi wajen Alhinayet dake zaune cikin shigar turkudi riga da zani sannan ta yaye kanta da shi ta fiti fit Buzuwarta ta ce” Alhi, dan Allah ki saka a kaini gida na dauko Lafayata, wannan ta gobe ce na dauko ashe,
Alhinayet ta ce ” Ohk ki je wajen Salisu motar a hannunsa dan tun jiya colonel ya hana na kuma fita da ita ,
Agaishat ta amsa inda ta dauki Abayarta ja mai adon baki baki a jiki mai mabalai ta saka sannan ta yane kanta da mayafin abayar,
Kai Agaishat fa ta gama haduwa, dogon hancin nan nata ya zo har kusan bakinta mai dan girma kadan, gashin girarta kuwa ta caje shi ta daidaita shi ya yi tsaf da shi ya bada kala, tsarin fuskarta kyauta ce daga Allah, gashi kuma ya hadu da nutsuwar yannayi,
Cikin nutsuwa take takawa har ta samu fitowa inda ta hange shi domin an saka fitilu ko.ina,
Tana zuwa da muradinta ya mike ya tafi wajen motar suka shiga ya jata sai gidan Ayya, wato mahaifiyar ogansu,
Suna shiga gidan Agaishat ta ga motoci har shida,
Biyar din kalarsu daya, sannan ga sojoji tsatsaye du sun hade fuska tamkar an zage su,
Tsayar da ita aka yi sai da aka cajeta dan kuwa ogansu na ciki ko wa bai isa ya shiga kansa tsaye ba,
Ji ta yi kafafuwanta na rawa, dan ba alamar sasauci a fuskokin su, dan haka a hankali ta samu ta raba ta haye inda ta fura kofar falon ta shiga da salama murya a dan dage kadan dan mutanen dake ciki su ji ta,
Salamar ce ta katse, a daidai lokacin da idannuwanta sukai mata arba da su,
Da Farko dai Wardugu ne da kakin soja sai dai botiraan rigar a bale inda rigar shi ta ciki fara kar ta samu damar bayana kanta da pecto dinsa,
Kafarsa daya kan daya ya dora, yana danna waya aman salamarta ya saka shi dago kansa da sauri tare da bugawar zuciyar da ta saka shi lumshe dara daran idannuwansa,
Gefe kuwa mijinta ne, uhum ba mijinta ba, tsohon mijinta, wato Mu.azam, docter Mu.azam ne zaune sanye da costume bakake da cravate dinsa ya daure cif da shi, duda kansa a aske kwal aman bai hanna bayanar kyansa ba,
Sai Ayya dake zaune cikin lafayarta , daga kasa kuwa Khadija ce ta duka da alama neman gafara take,
Idannuwanta ta lumshe, ta kara,lumshewa, dukan wata jarumta da take tunanin tana da ne take gayatowa , sai dai ina, gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa wanda hakan ya yi sanadiyar sakin dankareriyar samsung dinta kasa inda ta bada Pats screen ya mutu????♀,
Dubanta ta kai wajen wayar , ta yi azamar dukawa dan dauka, sai dai gaba daya ta shiga raruma tana saki, ta kasa daukan!
Dan haka ta mike ta tsalaka wayar ta juya da gudu gudu ta shiga hawan bene dan neman dakinta tana kokarin dane wani katoton kuka dake taso mata da karfin tsiya,
Ayya ce ta mike da sauri, inda ta ga gilmawarsa kawai, da karfinsa yake taka matatakalar yana nufar inda take inda idannuwansa suka rufe hankalinsa ya tashi,
Ayya ta ce” Wardugu,
Ina baya jinta, shima adu.a yake, fata yake na Allah ya sa ba kukan abinda yake tunani take yi ba,
Dakinta ya tura ya shiga,
Idannuwansa kyam saman kanta inda ya ga ta cire abayar jikinta sauran doguwar rigar nan ta cire dan kwali ta yar , ta kifa kanta saman abin bed, kuka take har tana jijiga,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi ne abinda ya iya furtawa kafin yake karasawa inda take,
Hannayensa ya saka wajen kafadunta ya dagota tsaye gaba dayanta,
Kokarin bude jikakun idannuwanta take , sannan zufa ta jike gashinta daga gaba tamkar ta watsa ruwa, fuskar nata ta jike jagab tana hakin kuka,
Bai bari ta karasa bude idannuwan nata ba ya janyota gaba dayanta cikin ni.imtacen jikinsa, wani irin riko ya yi mata gaba dayanta tamkar sabon babyn da baya so a kwace masa,
Kamshinsa, da wani irin bugawar da zuciyarsa ke yi wada tana iya ji a irin rikon da ya yi mata, da kuma bakon lamarin wai ita Agaishat kwonce a kirjin Wardugu, namiji daya ya daya, Wardugu zaki, wardugu guguwa lahaula wala kuwata, wani juuu ta ji wata juwa na neman debarta ita dake kwonce luf a saman kirjinsa, kukan ta nema ta rasa, hasalima mantawa ta yi ta yanda ake rera wakar kukan, sai wani ajiyar zuciya da take zaukewa mai dumin gaske saman kirjinsa dake bude,
Hannunsa dake rawa ya dago a hankali ya dora saman gashin kanta dake malale saman gadon bayanta ya dora ya dan ja hannunsa kasa sannan ya maido sama,
Tsayar da hannun ya yi yana kokarin bude idannuwansa da ya rufe ruf,
Muryarsa na rawan da bai taba yi ba, hannunsa na rawa ya ce” menene? Mu.azam ne?
Shiru ta yi bata iya bashi amsa ba, hasalima kokowa take da numfashinta domin yana buda baki maganarsa na watso mata kanshin turaran baki da yake anfani da shi mai kanshin banana
A hankali ya dora hancinsa saman goshinta, hakan ya baiwa bakinsa damar zuwa wajen jikakun idannuwanta,
Ji ta yi ya damki hannunta na dama da dan karfi kadan, sannan ya ce” *Son shi ki ke yi ko?*, *KUKAN SON TSOHON MIJINKI KI KE?*
masha Allah, Alhamdulilah, barkan mu da sallah yan uwa. ALLAH ya karba mana …..Amen
*TALLAH TALLAH TALLAH*,
*KUTKALE*
*PRISON KUTKALE*
Kwonce take inda aka gama jibgarta dan ta yiwa Eliz gardama, wani bacin wahala me ya kwasheta inda kamar daga sama ta ji ana lalubarta,,