BAK’A CE Page 61 to 70

Hannu ne, kokarin kai hannun ake cikin dadaudan sqet dinta wanda ko karamin wando babu a ciki, wato dai malan shigo………..
Domin karin bayani ka tumtubi +22791466605
Labaru masu zuwa in sha Allah
*AURE….YAKIN MATA NE*
*KAMARTA BATA DA NIYAR CUTARWA*
DAGA ALKALAMIN *SAJIDA* YAR MUTAN NIGER MARUBUCIYAR
*DUK KARYAR KADA*,
*YAR MAHAUKACIYA*
*DAGA TAFIA DAUKAR SOJA*
*BANI DA ZABI*
*NEMAN NA KAINA*
*BAK’A……*
Fan’s barka da sallahna????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣8️⃣
Asalamu alaikum
*Allah ya kawo mu wata mai albarka, banban wata mai tare da lada ,wata mai cinye zunubi, RAMADAN, ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA TARE DA WASILA DA FARILLAH A ALJANAR FIRDAUS Allah ka jikan magabatan mu, ka sa sun huta, idan tamu ta zo ka sa mu cika da imani ka sa mu tarda alkhairi ???????????????????????????????????????? Ya Allah, muna rokon ka, ka shirye mu, ka inta mu, ya ubangiji ka yafe mana zunubanmu, Allah ka hane mu saba maka,Ya Allah ka dora mu a hanyar bautarka, ka karbi ibadunmu, Ya Allah ka sa mu bayansa lafia ka maimaita mana, ni sajida ina mai yi mana fatan Alkhairi da fatan Allah ya kai.mu rai da lafia bayan sallah*
Algabitt ya dago da dubansa ya sauke kan Gaishata dake wani irin numfarfashi gabanta na faduwa tana duban mahaifin nata,
Algabitt ya kauda kansa yana bin mutanen dake zaune daya bayan daya da ido,
Kansa ya girgiza kafin ya kai dubansa wajen sarki ya ya buda bakinsa zai yi magana sarki ya mike tsaye ya ce” ya isa, kar ka fadi komai,
Muryar uwar gidansa ne ta ce ” sarkina, talakawa na zaune suna jiran hukunci,
Amaryarsa ce ta gyara zama ta saki murmushi ta ce” sarkina, muna masu neman alfarmar a yi hukunci yanda aka saba yiwa sauran talakawa,
Gaishata dake bin su da kallo su duka biyu ta maido dubanta wajen Sarki da ya tsurawa matan nasa ido cike da takaici,
Gaishata ta share hawayenta ta sada kanta kasa,
Sarki ya koma ya zauna yana duban dogarai dake muzurai , sun so su tsawatarwa da matan sarki sai dai gannin matan sarkin ne tsoro ya hana su su yi masu magana domin ba wanda yake da hurumin yin magana idan sarki da kansa na shari.a duda kauye ne, idan baya nan akoy mai wakiltarsa ,
Hade rai ya yi ya ce” du wanda ya kara buda baki ya yi magana a wajen nan zai karbi hukunci komai kusancinsa da Sarki!
Idan Dogarai suka ga abin tsawatarwa basu tsawatarba zasu fuskanci fuahina!
Ji kake suna fadin” tuba muke sarkin talakawa,
Sarki ya maida hankalinsa wajen Algabittt ya ce” tabas ka kasance mutun mai son kansa, ka yi rayuwa bisa umarnin zuciyarka, tabas munada muradin jin bukatar wace aka fi cuta duda ta bada amanar yarta ta wakilce ta, dan haka zamu iya sauraron zuwanta ko maganarta a waya,
Magana yake hankalinsa ba a kwonce ba domin tunda Gaishata ta sada kanta bata dago ba,
Mikewa ya yi ya danna kira kan number Gukunni ,
Bayani ya kora masa na komai cikin nutsuwa , yana gamawa Gukunni ya tarda matarsa da y’arsa, cikin hikima ta manya ya zayane masu komai wanda ya saka Anna fashewa da wani irin kuka har tana dukewa tana dafe cikinta da dukan hannayenta,
Mahaifiyarta dake kuka itama tana duban jikokin nata da suka dora hannayensu saman kansu sun kasa magana tsabar shiga firgici da tashin hankalin jin wai su din ashema ga ta hanyar da aka same su duniya ta kawar da kanta wajen mijinta dake zaune sai zufa yake ta rintse idannuwanta zafafan hawaye suka zubo mata ta bude murya ta ce” na haifi Allacthi ta hanya mai kyau wace Allah ya nufe ni,
Ban bi kowa ba, haka mahaifinta ya kasance mai kiyaye wannan lamari,
Wannan kadara ce mai girma wace ta girmi tunanina,
Tabas na zama wawa a wannan lamari,
Shin wa zan kaiwa kuka a nan gidan duniya?
Yau du abinda za.a yiwa wannan bawa in dai ba dawo da shekaru baya za.a yi ba a dawowa da y’ata martabarta bana tunanin zan ji zuciyata wasai,
Yau ko yikuwa na cakawa wannan mutun ban goge komai ba,
Idan rufe shi aka yi ma ba.a dawo baya ba,
Wai wai wai ni Herde wai rayuwa Hamdulilah, Allah na gode maka,
Gukunni, dan Allah ka yi kiran wannan yaron ka fada masa ni nace dan Allah ya saki wannan mutumin da ba zan so maimaita sunansa ba,
Ya bar shi, *wata shari.ar sai a lahira*,
Tana fada tana ta share hawayenta ne tana kula da irin yanda Anna ta dafe zuciya tana gumurzun kuka,
Wajenta ta nufa dan ta lura Gukunni sauraronta kawai yake,
Kama Anna ta yi ta kwontar da ita ta dubi Mariama,
Hade fuska ta yi danma kar su daga mata hankali ta ce” ke maza je ki yi kiran docter Aliyu, maza ya zo ina jiransa,
Maida dubanta ta yi wajen Gukunni ta ce” ba zai ga bayan farin cikin gidanna ba, ba zan yarda wani katon gardin dan kauye saka baki a rayuwar da ta doso ni mai tsananin haske,
Zan so na ga jarumtar ka a wannan lamari Gukunni? Zan so na ga dauriyarka, ka kama mani kar na rasa y’ata, sannan ka fadawa Ibrahim Asadeek cewa idan ya ga zama da Gaishata wani damuwa ne, ya dawo min da ita da yaronta,
Gukunni dake zaune yana dubansu ya mike ya fice a gidan ,
Zuwa ya yi aeroport neman jirgin da zai kai shi agadez domin mai tuka nasa jirgin yana hutu ba zai so takura shi ba,
Sai dai ina ba jirgin agadez kwata kwata a ranar, dan haka da kansa ya tuka mota zuwa gidan yaron nasa soja kuma matukin jirgi ya je masa ya fada masa bukatarsa inda ya baiwa matarsa hakuri cewar idan har sun kwana hali ne ya kama babu niyar hakan!
Abinka da manya masu garin, haka suka zarce inda ya yi kira ya nemi alfarmar zai tashi da jirgi tafiar gagawa abinda ya shafi familynsa domin koda kana da jirginka ba kyau tashi lokacin da ka yi niya sai an baka izini
Basu wani sauka a Agadez ba, tafia suka yi mai dan tsayi sai garin timiya inda ya yi ta shawagi dan samu wajen sauka wajen da ba rere da kuma duwatsu, sannan wajen da idan zai tashi zai samu dan hanyar tafia kafin ya cira,
Da kyar dai , da kyar ya samu wajen da ya nuna masa zai iya sauka, inda yara tuni suka fito baki bude sunna kallon wannan abu mai kara mai ficewa can sama yau yana yin kasa kasa cikin gari, hakan ya saka wasu firgita da tsoron fadowa zai yi ya kashe su,
Inda wannan lamari ya ja hankalin mutanen fada da suka ki watsewa du suka dugunzuma zuwa gannin abinda ke faruwa kuma,
Dole sarki ne zai je gaba , dan haka ya mike ya kai dubansa wajen Gaishata dake yanda take ya juya da sauri ya tafi dan duba lamarin kauyensa inda yake tafe yana ayyana dole ya ajiye sarauta , shi kam ya kai wajen da ya ji takaicin kasancewarsa sarki,
Suna samun tsayawa Gukunni ya mike ya fito domin ya bude masa kofa inda shi kuwa ya zauna ciki yana gyare gyare da duba idan komai lafia dokin wajen ba wajen saukar jirgi bane