BAK’A CE Page 61 to 70

Ido Sarki ya kwalalo gannin Gukunni,
Mutane kuwa kallon mutun da baki haka a cikin jirgi suke, daman bakima na shiga?
Wajen sarkin ya nufa inda Algabitt ya kusan zubewa kusa da dogarin dake tsare da shi,
Ai kuwa juyawa ya yi da jiyar baiwa wandonsa iska sai dai an tare ko.ina,
Hayaniyar a sake shi ta ja hankalin Gukunni waje sa, dan haka ya saki hannun sarki da suka gaisa ya nufi wajensa yana dubansa da kyau
Yana zuwa ya tsaya gabansa inda Algabity ya zama wani cirit a gabansa,
Gukunni ya girgiza kansa, a fili ya ce” wai a gaban halita irinka kana haka ina ga ka je gaban wanda ya halice ka? Tabas ba sauran abinda zan yi shari.a a nan,
Yana gama fada ya koma wajen sarki ya ja hannunsa gefe,
Cikin nutsuwa ya ce” ina gaishata ne?
Sarki ya sada kansa kafin ya ce” tana cikin wani hali, ba yanda ban yi da ita kan a yi shari.arnan a sirince aman ta kada kai ita sai an yita a fada, hakan ya hadasa mata tashin hankali,
Kansa ya girgiza idannuwansa da sukai ja ya ce” ka san me? Shi du abinda Allah ya hanna, ma.aiki ya kawo mana mu yi aiki da shi,
Shi tsananta bincike ba kyau,
Yanzu wa gari ya waya?
Sarki ya kada kai yana duban gefe da yannayin damuwa,
Gukunni ya ce” zan so ka bani ita mu je gida, idan har kana ra.ayin hakan, zan so ta je ta huta, zamu so mu hada su su duka mu yi magana da su, zan so su saurari gargadi da nasiha ta zaman da zasu yi na rayuwa,
Tanas duniya ta ci gaba aman banda wajen mata,
Wannan bakin fentin na iya hana su sukuni cikin mata yan uwansu,
Zan so ka yi min wannan alfarma,
Sarki ya gyada kansa ya ce” tabas mata suna girma aman suna cin kasa, a yanzu haka har na so soke maganar abokan zaman nata suka takalota,
Dan haka yin hakanma ba laifi bane, nima ina kan duba wani lamari na nan , zan yi shawara da tsofafi magabata in sha Allah, a taya mu da adu.a Allah ya sa abinda za.a shiga alkhairi ne
Gukunni ya amsa shi cike da farin cikin zai bashi Gaishatar da zuciya guda,
Juyawa suka yi dan shiga ciki Gukunni ya ce” ita dai dayar har yanzu ba labarinta ko?
Sarki ya ce” aa, da wasika da wanda take hannunsa ya kawo, bara na dauko wasikar ni ai na sha.afa abubuwa sun shige mini,
Juyawa ya yi cikin gidansa inda Gukunni ya karasa wajen Gaishata ya duka,
Hannunsa ya saka ya dago habarta, kir idannuwanta abude suke sannan a soye,
Sauke idannuwanta da ta yi saman fuskar kakanta ta ji bakinta ya bude, murya na rawa ta rike hannunsa ta ce” ashe mu shagu ne ba aure Algabitt ya rayu da mu? Ya zamu yi rayuwa a cikin wannan lamari? Ya zan rayu cikin kishiyoyi da kauye a haka?
Ya kanuna da basu samu miji ba zasu samu a irin wannan rayuwa ta yanzu? Idan Agaishana ta ji haka, ya zata dauka? Ya mijin dake aurenta zai dauka?
Gukunni ya lumshe idannuwansa ya mike ya samu ya dagata ya dubi mai aikinta ya yi mata umarnin maza a dauko sultan,
Bai bata amsa ba sai jan hannunta da ya yi suka nufi wajen jirgi inda ha baki bude aka raka su da kallo , da yawan mutanen da fadin ko dai Uban Agaisha ne? Wato Bak’A?
Nan ya tsaya jira har sarki ya fito suka kara gaisawa ya bashi takardar da Wardugu ya kawo dauke da wasikar da bai karanta ba,
Juyawa ya yi ya basu waje shi da matarsa su yi salama kafin suke dagawa,
Wajen yama tuni sun dawo garin niamey inda mai tuka shi ya ja su har gidan su,
Suna zuwa ya saka ta fice shi kuwa yana rike da Sultan dake dan wasansa na jarirai ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya daga idannuwansa sama yana kallon sararin samaniya,
Takardar nan ya bude ya duba,
Number waya ne kawai tsararu masu bin juna sai sunnan da ya zirawa ido da mamakin gannin sunnan , shin sunna ne ya zo daya haka ko kuwa shi din ne?
Wato jan gwarzon nan, yaro mai hazaka, yaron da yake ji fa shi dan aiki na yawan hada su, yaron da idan yana kallon abubuwan da ya yi a duniya har wani tsam yake ji da jin wani yannayi na shauki da jinjina masa da gannin girmansa tamkar wani datijo, yaro karami mai watsa taron yan daba, wato *WARDUGU BATUBE DAN MARAHUT*
MA.ASALAM
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
7️⃣1️⃣
*KUTKALE* (prison)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan Niger in sha Allah,
……..kar ku bari a baku labari……………
Wannan karron ma bata iya bashi amsa ba, ina ba zata iya budar bakinta ba, wani irin nauyi bakinta ya yi mata, sannan wani haushi take ji, *SO?* yo ita ba Mu.azam ba, ko waninsa bata tunanin zata kuma aminta ta so dan gudun idan ya wulakanta ta ta afka damuwa, dan haka sai ta dan motsa hannunta da ta fara jin zafin irin rikon da ya yi masa sannan ta bude idannuwanta a hankali ta dan janye goshinta daga wajen hancinsa sannan ta dago da dubanta a nitse ta sauke saman fuskarsa,
Kallon kasan ido yake yiwa du wani motsinta, hakan ya sa ya dan sasauta kusancin da ya saka a tsakanin su kafin yake bude idannuwansa gaba daya ya zuba cikin nata da kallon da ta tsare shi da shi,
Da sauri ta sada nata idon, domin idon Wardugu ya kada yay jajir, tsoro ne ya shiga dirar mata duda irin magangannun da ta fadawa kanta na ba zata kuma bari tana irin tsoron nan ko a gaban waye ba,
A hankali ta dan ja baya ta zauna saman bed din , ta sada kanta kasa,
Wani irin abu take ji, wata faduwar gaba da take ji da wani sanyi sanyi, sai uwa uba wani irin dadi da take ji na kulawa da damuwarta da Wardugu ya yi a daidai wannan lokacin,
Bayansa ta dago ta tsurawa ido , dogon namiji, namiji ingarma,
Hannunsa da ya dafe goshinsa ta kalla , wato damatsunan hannun , da sauri ta sada kanta domin sai da gabanta ya fadi, a zuciyarta take ayana shi wannan wani irin jiki ne da shi haka?
Wardugu kam kokarin saita kansa yake, gabba daya ransa ne yake ji a jagule, hankalinsa du a tashe dalilin kukan nan, shi kukan yake son sani na menene? Kuka? Ta zubar da hawayenta haka kawai? Bata san girman darajar hawaten ba? Sai ya waka ne? Ya ilahi,
Juyowa ya yi yana dubanta kafin yake daga kafarsa a hankali ya dangana shima da bakin bed din,
A dan tsorace ta dago dan gannin ya zauna kuma, kar ta ja ya daketa a banza kafin a amsheta wannan ai har ya sumar da ita, haba dole su suma idan yana dukansu yo wannan hannu haka?
Bana son yawan magana da tambayar mutun yana kyaleni. Wardugu ya fada hankali kwonce.
Dagowa ta yi inda bakinta ya shiga dan rawa rawa kafin ta ce” ina cike da tunani ne….
Wardugu ya tsura mata ido yana mai jin zuciyarsa na dokawa, a hankali ya ce” *Tunaninsa?*
Agaishat ta sauke ajiyar zuciya ta yatsina fuskarta , tunananinsa? Kanta ta girgiza ta ce” aa, ina yawan tunanin a yan kwanakin da na yi da shi, menene girman laifin da nayi masa da har ya kai shi mayar da ni karamar bazawara? Wani kure ne wannan na tafka masa da ya saka shi ahiga jikina sannan ya sake ni?
Da sauri Wardugu ya dago da idannuwansa ya sauke kanta, *SHIGA JIKINA* kalma mai ma.ana biyu, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ji ya yi kansa ya fara juya masa, duda yana da wani tunanin da wuya ta yi irin furucin nan a gabansa, aman wani lamarin ya rinjaye shi,