BAK’A CE Page 61 to 70

Innalilahi kawai yake maimaitawa domin ya jima da daina jin me take fada da idannuwansa ruf a rufe suke,
Da kyar ya iya mikewa ya shiga dan takawa a hankali , bai ce da ita ufan ba ya bude kofar nata ya fice a dakin yana mai dan dafe kansa,
Maganarsa ya tsinta inda yake cewa” Ayya, a facebook ne na ga sanarwar auren Alhinayett, abinda ya sa muka zo kennan, dan girman Allah Ayya ki duba maganata , ki zauna ki nazarceta, zaki ga iya gaskiyata kennan, Ayya ba zan yi maki karya ba, ba zan iya wannan gangancin ba????????
Bai iya tsayawa a falon ba ya zarce zai fita, nan ya taka wayarta dake yade hakan ya saka ya duka ya dauka idannuwansa na kara rikidewa da tsabar masifa a cikinsu,
Da kallon tsoro, da kuma mamaki Ayya ta raka shi, kafin take juyowa da sauri wajen Mu.azam tana mai tarababin abinda ya fada kan Wardugu, ya salam! Shi ne abinda ta iya furtawa, sai kuma abubuwa suka shiga dawo mata daki daki,
Tana kallo Mu.azam ya mike ya bi bayan Wardugu, tana son tsayar da shi aman tunanin lamarin ya saka harshenta yin nauyi,
Da sauri ya karasa inda yake tsaye ya mika hannu ya taba kafadarsa,
Da sauri Wardugu ya juyo jin an taba shi,
Wani irin kakausan kallo ya jefawa Mu.azam , kallo mai nunin zan iya kasaraka, kafin ya furzar da wata iska ya maida dubansa wajen yarensa da suke tare hakan ya saka suka matsa suka basu wuri domin sun biyo Mu.azam ne kar ya karasa wajen ogansu
Kansa ya dafe , muryarsa a dan dage sannan cike da tashin hankali ya ce” dan me sai ita? Me yasa zaka ringa kokarin sakata kuka? Ka san ya na jure wanda ta yi ta yi min a lokacin da ka wulakanta ta? Ya zaka biyo mini ita nan ka kara sakata kuka?
*Ka CUCE NI*, me yasa Mu.azam? Me ya sa? Me na yi maka ka huce a kanta? Ya aka yi ka min haka? *Ban cancanci haka ba*, wayo wayo wayo Allahna…….! WARDUGU ya karashe yana mai dukan hanayensa a kansa da karfinsa,
Mu.azam ya dan ja baya, ransa bace da yannayin nan ya ce” danme ba zaka fuskanci lamarin ba? *Agaishat* *KADARA* ce! Nauyin baki, tsoro! Zai saka ka yin aikin dana sani, domin idan ni na kawar da kai ga tarin ni.imarta wani ba zai iya ba!
Wardugu ya harzuka ya cakumi wuyan rigarsa cikin karaji ya ce” ni zaka fadawa maganar banza maganar ni.imarta? Ni kake nufi ina tsoron mace ko me? Na taba fada maka wata magana a kanta ne?
Mu.azam da ya rike hannunsa da kyar yana so ya sakar masa wuya aman ya kasa suka ji muryar Ayya tana tafa hannu,
Hankalinta tashe ta karaso wajen su ta saka hannunta bibiyu ta kama jan hannun wardugu da iya karfinta,
Da kyar ya cika hannun kafin rai bace ta nuna masa hanyar fita ta ce” jeka gidanka! Tafi ka bani waje!
Rigar kakinsa ya ja ya cire baki daya ya yi masa sauran ta cikin kawai , ya juya ya nufi wajen motocin dake parke du sun yi cirko cirko suna sauraron fadan cike da taoron su shiga abin ya juye kansu,
Zuwansa ya saka aka bude masa ya shige suka tayar suka dauki hanya,
Kansa kawai ya jinginar ya lumshe idannuwansa kafin ya shiga hasasota a idannuwansa, ya Rab shi ne abinda ya iya furtawa ya kule bakinsa yana saurare har suka karasa gidansa ,
Ficewa ya yi ba tare da yace da su su ci kansu ba ya shige part dinsa ,
Walyn ce kwonce saman doguwar kujerar dakin daya kwalin kwal wace aka canza kayan dakin da kallolin aka saka masu ruwan zeba da dan ratsin fali aka saka kujerar zoguwa ta yi kwana ita daya mai wani irin zubi irin kujerun gidan sarakai, gannin idoma zai nuna maka da an kashe kudi a kanta, domin da ka kaleta zaka ga tamkar tana gayatarka ne zama samanta
Ido ya tsura mata ta saamu baci abinta, hankalinta kwonce abinta, ta sha yar karamar rigarta ta baci baka mai shara shara ta daure gashin kanta waje guda ta yi shar da ita ,
Da ita ya yi tafia ta wajen sati biyu,
Zagaye kujerar ya yi ya nufi dakinsa na baci yana faman neman bayi ya watsa ruwa mai sanyi ko zai ji zuciyarsa ta rage nauyi,
Bayan ya fito a wanka wayarsa ya tarar tana ringin,
Wajenta ya nufa ya dauka ya amsa kiran Alhinayett ce, sauraronta ya yi ta gama maganar kafin yace” kin ga ki raba ni Alhinayett, idan ni ina uban gidansa a wajen aiki ke uban gidanki ne a rayuwar aure, kar ki yarda ki ringa fada min laifinsa domin idan ina yawan yi masa magana tsanarki zai yi, ke wai ke din ba mace bane ba? Dole sai kin masa katsalandan a abubuwan da ya tsara maku na rayuwa? Haka kawai yara kananu kuna saka mutane yawan magana da tashin hankali? Ohk yanzu da kika kirani kika fada mani so kike in kiraye shi in tirsasa masa saka turkudi a ranar da za.a yi masa murnar aurensa na sojoji ni babansa ko? Kawai dan kina buzuwa shikenan zaki sako shi a gaba dan wulakanci ranar sojoji ki saka shi ya nada rawani kamar sarkin wani gari ko wani tsohon baruma? Yaki ba zai saka ba, nace ba zai saka ba!
Ya karashe da dan karaji,
Alhinayett da ta rafka tagumi tana tarababi da fadin ikon Allah wa ya tabo shi a ranta, ta zaro ido ta ce” Toh, ikon Allah
Wardugu ya ce” ni ne toh din ko? Ni ne toh din?
Ai kuwa kitt ta kashe kiran tana zazaro ido ta kai dubanta wajen matar abansu ta saki wani murmushi mai kama da ba.a dace ba,
Haka ya bi wayar da kallo kafin ya yi kwafa ya ajiye wayar
Har zai karasa kusan bed ya kai dubansa kan wayarta samsung da ta farfashe,
Juyowa ya yi ransa a jagule ya jujuya wayar,
Abin cire sim ya dauka a gaban sif dinsa ya ciro sim din wayar kwaya daya na airtel ya bude wayarsa iPhone 11 ya saka layin a ciki ya kunna wayar ya ajiye nan kafin ya zarce wajen bed din ya kwonta ya lumshe idannuwansa,
Kansa yake ji na sara masa sosai, dan haka ya yi adu.ar baci da fatan Allah ya sa ya samu bacin ya lumshe idannuwansa bayan ya kashe fitilar dakin
Ayya kam sosai abin ya daketa, ta yi mamaki, sannan ta tausaya masa, anya kuwa? Anya ta taba gannin abinda ya yiwa irin wannan son da idannuwansa ke rufewa idan tana waje ? Jikinsa fuskarsa, da act dinsa baki daya ke nuna kariya ga abin? Ita kam ta shiga wani yannayi, ta yaya? Yaushema ya yi aure?
Gannin damuwa na neman hadasa mata ciwon kai ya saka bayan su Mu.azam sun tafi hotel domin wannan karon a hotel suka sauka ta haye sama wajen Agaishat, nan ta tarar da ita ta yi baci hannunta dafe da goshinta,
A hankali ta zauna gefenta ta sauke mata hannun dan kar ya sage sannan ta tofa mata adu.o.in tsari ta ja mata rigarta ta rufe mata inda ya bude a jikinta ta mike ta tafi ta ja mata kofa tana tausaya mata , ko me ya dawo da ita daga wajen sabgar auren?
Tanaa shiga dakinta ba kwonciya ta yi ba, alwallah ta daura ta raba dare saman salaya tna mai neman zabin Allah da kawar da du wata fitina…………
Wannan kennan
Ranar daurin Aure
Tun karfe biyar Ayya ta tayar da Agaishat ta barta ta kimtsa inda itama ta koma dakinta ta karasa shiryawa,
Wanka ne ta darza sosai domin bakonta ya zo mata tsakiyar dare,
Tana fitowa ta saka auduga da pant, sannan ta zauna a yar kujerar turaren wutarta ta yi turare mai sanyayan kamshi sosai har gashin kanta,
Tana gamawa ta mike ta mayar da komai wajensa sannan ta daura tawul a jikinta ta zauna gaban coiffeuse dinta,
Cikin nutsuwa take kimtsa kanta, hodar ruwa mai duhu duhu irin fatar jikinta ta dan shafa yar madaidaiciya wace ta kara haska mata fuskarta da wani sirri,