BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Nan ta samu ta kara bin gashin girarta ta gyara shi tsaf,

Jan baki ta dauka ta dan shafa kadan kalar pink domin koda Agaishat nada duhun fata lebenta kalar pink ne na kasan na saman ne mai duhu hakan ya saka na kasan kawI take sakawa jan bakin hakan sai ya bada kala.

Tana kokarin zirara kwali a idannuwanta ta ji dirar motoci,

A hankali ta mike ta leka ta windows, 

Ya Allah, shi ne abinda ta iya furtawa ta saki labulen ta koma wajen gyaran kanta ,

Su Wardugu ne, motoci ne laye farare kar, du sun sha shada ruwan Baka, color din ya wani irin fito da shi, ya kafa hular da……

Tunaninta ne ya katse lokacin da Ayya ta turo dakin,

Hannunta dauke da wani Lafayar ta karaso , 

Ayya ta ce” tashi ki saka kayanki su Wardugu sun zo daukarmu

Mikewa ta yi ta karbi lafayar mai mahaukacin kyau da wani tsare tsare mai ruwan turkudin ta je ta ciro yar doguwar riga mai gajeran hannu fara kar a kayanta ta dawo ta saka rigar ba wani bars a ciki, 

Ayya ta mike da Lafayar ta shiga nada mata cikin nutsuwa har ta gama tana dubanta,

Hancinta ta ja ta ce”ki karanta lahaula wala kuwata illa billah ki shafa a jikinki da li.ilafi, masha Allah kin yi kyau Yata,

Agaishat ta saki murmushin jin dadi ta ce” Ayana na gode????,

Ayya kam binta take da kallo inda Agaishat ta juya ta dauki takalmi da yar jaka wace ta ado ce kawai domin ko wayar babu batama san inda ta yarda wayar ba, 

Nan ta shafa humura da turaren feshe na hamata sosai ta shashafa sannan ta karasa kusan Ayya tana duban irin yanda Ayya ke kallonta 

Fitar dakin ta kashe da Ac suka rankaya kasa , 

Tun daga sama gabanta ya buga, domin Walyn ce hakimce ta hade cikin shadar baka itama ta yi wani irin kyau tamkar sarauniyar mekka,

An zuba zinari an coge da dogon takalmi da jaka , tana danna watsetsiyar iPhone dinta tana sakin dan murmushi da alama chating take kuma yana birgeta,

Da sauri ta kawar da kanta daga dubanta domin ta dago ta watsa mata kallon da ta rasa na kyama ne ko na raini ne take mata a kulun idan sun hadu?,

A hankali ta dube shi kanta a kasa ta ce” ina kwana Ya Wardugu,

Amsawa ya yi da “Lafiya, 

Kawai, aman kuma kyam kallonta yake, lafayar ta yi mata kyau da yawa, gashi dan jaraba harda gayar yan daurin aure yake yawo maza masu farauta kuwa! 

Fuskarsa ya gimtse ya mike ya fice gaba kafin du suke biyo bayansa, 

Ja ya yi ya dan tsaya inda Walyn ta zarce wajen motar da suka shigo shi da ita, da dan mayafinta sai isa take bazawa ta shige motar ta hakimce abinta,

Ayya ce ta karaso kusa da shi, nan ya samu damar kara dubanta murya kasa kasa da yaren tubanci ya ce” yanzu Ayya fisabililahi a haka zata je wajen daurin auren? Gidan bikin da ya tara shegun masu jar fatan nan?

Ayya ta zaro ido tana dubansa kafin ta tafa hannayenta ta ce”””””

              Barka da safiya

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣2️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga ALKALAMIN yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,

………….kar ku bari a baku labari…………………….

Ayya ta tafa hannayenta ta ce” ni ban ga aibun shigar yarinyata ba,! 

Gaba ta yi taki tsayawa maganar ta yi tsayima inda Wardugu da mamaki ya dan rike habarsa yana girmama irin son da Ayya ke yiwa yarinyarnan , dan kuwa idan ba a kanta ba , bai ga abinda zai fada ba Ayya ta musa masa,

Kansa ya kada yana hangen inda aka bude masu, motar dake gaban tasa nan suka shige bayan su duka,

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya hanzarta ya tafi wajen tasa da Walyn ya shiga shima,

Tafia suke inda Walyn ta narke masa kan kudin jakarta sun mata kadan shi kuwa ba tsayawa zai yi bank ta ciri kudi ba,

Yana dubanta da kulawa ya ce” menene marar dadin da ya hada ki da Agaishat ne da bakya amsa salamarta?

Tsai ta yi da shagwabarta ta dan tsura masa ido kafin ta dan hade yannayin farin cikinta ta ce” Wacece haka?

Wardugu ya juyo da kansa saman fuskarta da kyau, wacece? Taf, shi ya ayanna a ransa kafin yake gimtse fuska dan kar ta yi kokarin kawo masa raini da safiyar nan,

Walyn ta hadiye tashin balagar fitsararta ta ce” to aman Heart ka ga ai kai kadai ta gaisar, bayan kuma ni na girmeta, kuma ni ta tarar a zaune ko? Haka take min yarinyar ban san me take jin kanta da shi ba idan ta ganni ba zata girmamani yanda ya dace ba sai dai a wani dake ta min magana, ni shi yasa bana shiga sabgarta ko daya ! 

Wardugu kam tunda ya kawar da kansa bai kara ce da ita komai ba, shiru ya yi inda ya kai dubansa kan Wayarsa da sim din Agaishat ke ciki,

Wannan number tun jiya take kira da tura messages, messages sakarkarun messages, messages masu ban haushi,

A hankali ya bude wanda ya shigo yanzu ya karanta kamar haka ” haba targui, tau ashak din naki ne ya motsa tun jiya an ki a kula ni? Ni kam zan yi maza na kawo kudin gaisuwa gida a san da zamana ko za.a yi maganarmu, bafa na son wasa da zuciya Targui, 

Murmushi ya saki wanda ba zaka gane manufarsa ba kafin yake ajiye wayar yana kallon sun karaso sun parke ana jira daga gare shi,

Duban Walyn ya yi , da yatsarsa ya yi mata nuni da ta tsaya kar ta fita, sannan ya fita a kotar

Yana fita du suka nufo wajensa suka shiga kakare shi daga maroka da masu son su gaisa kai harma da masu harin rayuwarsa, su kam a shirye suke, tabas shadoji ne a jikinsu aman kasan rigarsu ba wanda bashida bindiga yar karama wace a koni lokaci suna iya cirota idan bukatar hakan ta tashi,

Tsayuwa ya yi ya kali gabas da yama, kudu da arewa, can ya yafito kanin Alhinayett dan saurayi sannan ya yi masu nuni da su barshi ya karaso,

Musabaha suka yi kafin ya ce” ina so a bude hanya a shiga da mahaifiyata,

Ai kuwa da sauri ya matsa dan zuwa ya bude hanyar sannan a bude kofar shiga da motar,

Wajen motar ya karasa wajen direba ya bude ya masa umarnin fita, 

Yana fita shi kuwa ya msye gurbin direban sannan ya tayar da motar a hankali ya fitar da ita daga layin motocin ya shiga tukata cikin nutsuwa har cikin gidan su Alhinayett inda sojoji masu kaki dake wajen du suka kame masa wasu kuwa suka rufe motar dan bata tsaro har ya dangana da wajen da zasu fito sannan ya fita ya zagaya ya budewa Ayya gefen da take,

Jakar hannunta ya karba ya kamo hannunta na dama ya taimaka mata ta fito cikin nutsuwa sannan ya kai dubansa kan Agaishat dake ta son ta bude gefenta ya ki buduwa bata san sai da kys din hannunsa kowani bangare na motar ke iya buduwa ba,

Hannunsa ya mika mata fari kal fafada da shi inda ya dan leka dan ta gane nufinsa,

Hannun ta bi da kallo, kafin take dago nata dake rawa rawa a hankali ta dora saman nasa ta yunkura ta sako kafarta daya mai dauke da takalmi mai dan matsakaicin tsayi kafa ciki na fata aman an yi masa adon fari kar, zamo kafar da ta yi ya saka lafayar ta dan dage har kaurinta a waje,

Ita dai bata san ya aka yi ba, sai gani ta yi ya saki hannunta ya saka hannayensa biyu ya ja lafayar ta sauka ta rufe wajen da ya fito, sannan ya dago da fuskarsa suka hada ido cikin ido ,

Idannuwansa ya wani irin lumshewa a hankali, ya rage masu girma sosai , hakan ya sa samansu suka kumburo kamar mai jin baci kafin yake saka hannunsa ya ja rufar kan ta rufe gashin kanta da kyau domin kadan ya dan fito da siririn yan kunayenta masu tsayi da suka kara kawata kwaliyar,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button