BAK’A CE Page 61 to 70

Karasa fitar da ita daga motar ya yi ta hanyar kara kamo hannun nata,
Rawa rawa kafafuwanta ke yi, hakan ya sa ya bi cinyoyinta da kallo, dan kuwa lafayar dake jikinta bai hana cinyarta kadawa ba sakamakon rawar da kafafuwanta ke yi, dubansa ne ya kai kan yarensa, ya ga suraj kyam na kallonta, wani uban harara ya zabga masa wanda ya saka shi juyawa gaba dayansa lokaci guda,
Ayya ya ga bata wajen, wato ta shigewarta wajen matan , dan haka ya kara kusanta kusancin dake tsakaninsu ya rage murya ya ce” ki daina haka mana, ki daina rawa rawar nan, domin ba iya kafarki da cinyarki ke motsi ba????,
Agaishat kam da ido take binsa tamkar ta ga sabuwar halita, inanta ke motsi? Ya Allah, da sauri ta kara jan mayafinta ta gyara rufar lafayarta kafin ta mika hannu ta dauki jakar Ayyarta da ya ajiye nan dan gyara mata lafaya ta hada da tata kanta na duban kasa ta shiga neman ta inda zata raba ta bar wajen domin gaba daya idannuwanta basa nuna mata hanyar bi , du ya cika wajen,
Tsayuwa ta yi gabansa hakan ya bata damar tsayuwa daidai kirjinsa domin ya fita tsayi, ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta dago da fuskarta ta dube shi ido cikin ido, gabanta ne ya kara faduwa , wasu hawaye take ji suna kokarin zubo mata domin ji take sam jikinta tamkar ba laka, da kyar ta iya shagwabe fuskarta kamar koda yaushe idan zata yi magana ta ce” zan je wajen Alhinayett,
Wardugu ya yi murmushin da bai yi niya ba ya dan kauce ta raba gefensa ta shiga tafia mutanen na kadawa tamkar wace ke yi da gangan ,
Idannuwansa ya kara lunshewa sannan ya juya da kafarsa suka rankaya da jama.arsa suka koma waje,
A jikinsa yake jin Walyn na binsa da kallo, , niyarsa yana fitowa ya je itama ya sanyota, sai dai ya tarar wajen angwaye sun karaso an fara haramar daurin aure gashi kuma shi ke zama kusa da mahaifin Alhinayett din,
Hakan ya sa ya bada kys din motar ya bada umarnin a sanyota domin sosau waje ya dauki harama,
Captain Ashiru ne ya karasa wajen motar ya bude ya sanar mata abinda Wardugu ya ce,
Idannuwanta da sukai ja na bacin rai da tashin hankali kawai ta iya budewa ta watsa masa kafin ta mika hannunta ta ciro kys din motar ta fito ta shiga gidan gaba ta tayar da motar ta fita da ita ta yi tafiarta
Bata zame ko.ina ba sai gidan aminiyarta, tana shiga hankali tashe ta je ta zauna saman kujera,
Dubanta take tana tambayarta lafia?
Walyn ta ce” menene tsakaninsa da ita? Wacece ita?
………………gidan biki………….
Shagali kawai ake, biki irin na buzaye, guitar ake ta kadawa inda du suka hakimce suna dan shiga rawa da dadaya maza da mata ana cashewa cikin nutsuwa , sai ruwan kudin da ake zuba masa domin fitacen mawakin nan ne Bombino.,
Maza kuwa tunda aka gama daurin aure suka tatara suka daga sai compagni baba inda suka je suka wuni.suna gashin shanun da suka yanka sai dai udan lokacin sallah ya yi a tashi a gabatar ga masu yi , a ci gaba da gashi , wasu na buga coss, wasu na game din buil, wasu na zukar shishar su, abin dai ya kankama domin kowa da gayarsa ne, haka Mu.azam ya saje da su dan kuwa ba wani abinda Wardugu ke nuna masa na bacib rai a gaban mutane normal yake amsa shi idan hakan ta kama har yama ta yi suka watse kowa ya nufi gida dan a shirya daukan amarya,
An kai amarya gidanta, yan matan amarya sun sha adonsu ba.a kama hannun yaro, an sha shagali a tsare a tafiye irin ta sojoji, tsari irin na sojoji,
Daga nan aka kwashe yan matan amaryar kowace aka shiga maida su gida, Agaishat ta zo shiga motar gugun yan matan wani soja da kaki yace da ita General yace a mayar da ita gida,
Tsai ta yi da dan alamar tsoro tana dubansa dan bai nuna mata shaidar hakan ba, sai da mijin Alhinayett ya fito da waya a kunensa yana amsawa ya karaso inda suke tsaye ya ce” in sha Allah sire,
Yana kashewa ya dubeta ya fada mata General ya sa a mayar da ita gida,
Wajen motar ta karasa ta shiga ya jata suka dauki hanyar gidan Ayya ba um ba umum tsakaninsu dan tukinsa kawai yake duda tarin tambayar dake cin ransa,
Ranar diner…………
*Chaina*
Garin da aka kawo Anna dan neman lafia tun daga lokacin da suka kaita asibiti docter ya tabatar masu da ta samu shanyewar barin jiki sanadiyar hawan jinninta da ya mugun tashi wanda take da shi da jimawa yanzu ya yi karfin da ya kaita haka, damuwa, faduwar gaba, fargaba, tashin hankali, da rike damuwa a cikin rai suka taru sukai mata ruf daya suka kwontar da Anna,
Likitan da ya dubata, shi ne ainahin wanda suka yi karatu da shi, wanda suka hadu lokacin da ta kawo fatimata jinyar yoyon fitsari, amininta, cike da mamakin itace haka? Ina ta shiga ya yi masu maganar su fita da ita, domin akoy halin hakan alhamdulilah sannan tana da bukatar nesa da kasar ko zata kwontar da hankalinta ta karbi magani yanda ya dace.
Toh Alhamdulilah za.a ce domin dai yanzu wajen sati uku kennan tana daukan magani da massage, da kulawar famillynta dake zagaye da ita, tana yakar kanta dan gannin bata saka su a damuwa ba, tana raha duda kasan zuciyarta na cike da kawar Agaisharta,
Sai abinda ke bata haushi irin yanda *Aminullah* damun mutane da kira da nacin ya take!
Zan iya cewa du wani mai tsoro a kusa ba zai iya shiga wajen ba,
Domin kuwa a yau ranar sojoji sun fito sun nuna su din su ne,
Kaki suka saka mai ruwan tsanwa da fari, baki dayansu,
Kowa ya karbe shi da tsarin halitarsa,
Sai hulunansu , sai wukake farare kar masu lankwasa,
……laye suke su….
Wayo hannuna????????????????????????????????
Hey readers more comment plz????????????????
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
Na
*SAJIDA*
7️⃣3️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
……..kar ku bari a baku labari…..
Laye suke tun daga bakin hall din har ciki suna jiran karasowar amarya da ango, inda mutane ke zauzaune gefe da gefe wato hagu da dama bisan kujerun karfe farare kar da aka dan daudaura masu wani dan kyale pink da fari a jikinsu sai yan table table a gabansu ,
Can gaba kuwa kujeru shida ne masu shige da kujerun falo na alfarma wa.inda aka tanada domin zaman ango da amarya da aminin ango da matarsa da kuma general da matarsa
Guitar kuwa sai tashi yake inda mutanen da suka riga suka zo suka nuna takardar gayatarsu aka barsu suka shiga suke dan rausaya daga zaune abinsu domin an hana kowa shiga rawa tukunnan
Kannen amarya da sukai anko da kawayensu cikin shadarsu bugagiya sai meko take kowace ka kala sai ka kara kala don sun hadu ba wani kwaramniya sun fito ba ta yarwa,
Haka akai motarsu hudu, sai motar amarya wace ke tare da Agaishat ,
Ta sha dinkinta da ta zaba, yau kam bata lulube gashin kanta ba daurin dan kwalin da akai mata daga gaba aka fitar da shi sosai sannan daga tsakiya daure shin da aka yi da dan karamin ribom sai aka fitar da shi gaba dayansa, hakan ya sa ya malalu a bayanta, ga rigar kanta yau mai wuyan Bateau ce wato irin wuyan nan na zamani mai tsayawa a kafada , sai yar siriryar sarka mai wani dan dutsi kwaya daya tal fari kar da yan kunayensa, sai farin takalmi da farar pos mai kyalkyali mai forme din heart, gashin idonta ta saka masa maskara hakan ya sa ya kara tsatsayawa ya kara yin duhu sosai, lebenta ta shafa masa jan baki ja mai dan haske kadan ba dayawa hakan ya kara fitar da kwaliyar tata dan daidai masha Allah wace ko a cikin duhu zaka iya gannin hasken fuskarta komin karancin hasken waje kuwa,