BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Da farko tsakiya suka saka mijin Alhinayett, daga baya ta bar wajen ta koma bayan su Alhinayett ya kasance su Wardugu da Alhinayett sun sakata tsakiya,

Yau Wardugunma bata iya gaisarwa ba, dan a dan rikice take , fama take su yi su shige, aman ganninta kusa da shi sai ta ji ta samu nutsuwa, ko ba komai ta san idan wani abin ya nufota da yardar Allah zai tare mata, kai ba ita ba, du wanda ke wajen bashi da dar! 

A hankali suke takawa, salon kidan ya canza, daga can gefe aka harba bindigar toka ta yi kara sannan aka saki kidan harbin bindiga wanda ya saka du jiki ya kwashi wani tsam,

Idannuwansa a kanta, du wani motsi nata , sannan hankalinsa du a tashe yake, sai dai a fuskarsa ba zaka taba fahimtar hakan ba domin ya hade fuskar tamau ba wani fara.a, hakama yaran nasa ba wani mai isashen sakewa dan kuwa kasancewa a wajen party ba zai hana ya ci ubanka ba idan ta kama! 

Yanda tsarin yake sai amarya da angonta sun zauna kafin kowani namiji da ya jero da mace ya rakata har wajen zamanta gefen hagu sannan ya koma gefen dama domin rawar guitar, (sai wanda ya san yanda ake yi zai fahimata????????????????????),

Amarya da ango na zama suka fara juyawa dan kai yan matan wajen zamansu,

Dan tsai ta yi a lokacin da ta fahimci yanda wajen zaman yake, haka ta juya jiki sabule zata je wajen zaman yan matan ta zauna ita daya,

Bai fi taku biyu da ta yi ba ta ji hannunta cikin nasa, ba zata iya rasa sannin hannunsa bane domin ta gama karantar yanda hannunta ke zama daram cikin nasa,, ta yannayin da jikinta ke nuna mata du idan ya yi irin wannan lamari ya saka ko dubansa bata yi ba ta karantawa zuciyarya shi din ne, a hankali ya kara kusanta kusancinsa da ita ya shiga bin takunta ba tare da ya kaleta ko ya ce da ita ufan ba har suka sauka suka nufi wajen zama,

Suna karasawa ya tsaya wajen kujerar da kanwar Alhinayett ke zaune, wace take facing dinsa ,

Kallonta kawai ya yi da idannuwansa ta mike a wajen ta koma wata inda ya kali yannayin kujerar kafin da hannunsa na hagu ya yi mata nuni da ta zauna,

Cikin nutsuwa ta dago idannuwanta da sukai mata nauyi , nan ta ga ikon Allah ashe du yawancin hankalin mutanen wajen na kansu, tun daga kan sojojin har yan matan wajen, uwa uba Farid da ta gani zaune shima ya yi zuru yana kallonsu,

Da sauri ta zauna tana dan zaro idannuwanta inda ya dan yi tsai , kafin ya rage tsayinsa wajen kunnenta ya ce” Na haramta maki motsawa a nan har sai an tashi! 

Du mai kallon su, zai yi tunanin maganar soyaya ake a wajen nan, zai yi tunanin an gama mutuwa a son juna ne, bai damu da kallon da ake binsa da shi ba, hasalima sai da ya dan kara tsayawa ya mike da kyau ya bi kowa da kallo hakan ya sa mutane suke kawar da dubansu daga kansa kafin yake nufar kujerarsa,

Walyn, Walyn, walyn, wani kakausan kallo take binsa da shi har ya gama du abinda yake ya dawo ya zauna a wajensa wato kusa da ita,

Bata dubi tarin mutanen wajen ba, bata yi la.akari da wajen ba bale ta ari kissa irin tamu ta mata ba, yana zama ta shiga magana kamar haka” Wardugu, wannan wani irin mulakanci ne? Meye hadinka da kaskantaciyar yarinyar da muka dauko daga kasurgumin jeji dan cireta daga kangin talauci? Meye daraja a bakar mace har da zaka dauki hannunka mai daraja ka rike nata? Wardugu menene tsakaninka da tsohuwar bazawarar da amininka ya aura ya saki dan ba zai iya zama da ita ba? Wardugu wacece ita a wajenka? Wardugu! 

Ta karashe tana mai dan daga murya da wawatsa hannayenta wanda duka na kusa da su na jin abubuwan da take fada da irin dibar albarkar da take tafkawa inda na nesa da su ke hangen Walyn na yuwa Wardugu fada , domin kuwa geste dinta kamar uwa na yiwa yaronta fada ce, irin zazafan fadan nan ma kuwa,

Dubansa ya dago ya dora saman kanta, hauka? Shirme? Aa Raini! Kai tsaye, ido cikin ido, ba wani gargadar murya, ba wani kawar da fuska, ko tausasa harshe Wardugu ya ce” kina son ki san ko wacece ita? Ita din *ORRONUR* dina ce…….

Dankari,

Kaka kara kaka

Ku samo ma.anar ORRonur sai na baku wani page????

Walyn? Walyn! Wardugu! 

                        Agaishat

More comment bilahi????????????????????

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          7️⃣3️⃣

*KUTKALE* (PRISON)

*AURE YAKIN MATA NE*

*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*

daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,

……..kar ku bari a baku labari…..

Laye suke tun daga bakin hall din har ciki suna jiran karasowar amarya da ango, inda mutane ke zauzaune gefe da gefe wato hagu da dama bisan kujerun karfe farare kar da aka dan daudaura masu wani dan kyale pink da fari a jikinsu sai yan table table a gabansu ,

Can gaba kuwa kujeru shida ne masu shige da kujerun falo na alfarma wa.inda aka tanada domin zaman ango da amarya da aminin ango da matarsa da kuma general da matarsa

Guitar kuwa sai tashi yake inda mutanen da suka riga suka zo suka nuna takardar gayatarsu aka barsu suka shiga suke dan rausaya daga zaune abinsu domin an hana kowa shiga rawa tukunnan

Kannen amarya da sukai anko da kawayensu cikin shadarsu bugagiya sai meko take kowace ka kala sai ka kara kala don sun hadu ba wani kwaramniya sun fito ba ta yarwa,

Haka akai motarsu hudu, sai motar amarya wace ke tare da Agaishat ,

Ta sha dinkinta da ta zaba, yau kam bata lulube gashin kanta ba daurin dan kwalin da akai mata daga gaba aka fitar da shi sosai sannan daga tsakiya daure shin da aka yi da dan karamin ribom sai aka fitar da shi gaba dayansa, hakan ya sa ya malalu a bayanta, ga rigar kanta yau mai wuyan Bateau ce wato irin wuyan nan na zamani mai tsayawa a kafada , sai yar siriryar sarka mai wani dan dutsi kwaya daya tal fari kar da yan kunayensa, sai farin takalmi da farar pos mai kyalkyali mai forme din heart, gashin idonta ta saka masa maskara hakan ya sa ya kara tsatsayawa ya kara yin duhu sosai, lebenta ta shafa masa jan baki ja mai dan haske kadan ba dayawa hakan ya kara fitar da kwaliyar tata dan daidai masha Allah wace ko a cikin duhu zaka iya gannin hasken fuskarta komin karancin hasken waje kuwa,

Kusa take da amarya wace ta sha nadin Lafaya fara kar aka zuba mata sarkar gold dinta da awarwaraye sai takalmi mai dan tudu itama mai ruwa sarkar wato zeba zeba hannunta bata rike da komai dan zai zame mata kaya, 

Su biyu ne kawai a cikin katuwar motar da irinta kwaya biyu ce , dayar basu san ko su waye a ciki ba, aman baki daya motocin bakake ne wuluk har madubansu baka gannin na ciki ko daga gaba inda direba daya rak ke jan su cikin ayarin motocin,

A lokacin da suka karaso nan yan matan suka shiga fitowa inda Kanwar Alhinayet ta kara jadada masu tsarin shigar, dan kuwa sai amarya da ango sun fara shiga gaba, sannan General da matarsa, sannan aminin ango da matarsa, sai su kawayen amarya kowace da dan bouquet dinta na flower dan karami sai ta layu da soja daya wa.inda suke cikin yan tafiar makusanta da ango ne sosai manyan mutane ne suma daga colonel sai captain su shida ne wato harda Agaishat nada daya su bi bayan Amaryar da angon a haka su ratsa ta tsakiyar sojojin dake tsaye suka hada kawunnan wukaken nan na hannayensu sukai masu runfa da su, gldaga can gefe kuwa da yan yara biyu yayan buzaye dake watsa wani kyalkyali kyalkyali ga du wanda ya zo shigewa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button