BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Ayya ta gala mata harara ta kawar da kai irin ta shakan nan bama zata bata amsa ba, dan haka sukai mata salama ta bi su da adu.a suka fice a motar Alhinayett din.

Tafe suke suna dan hira inda wakar guitar ke tashi kadan kadan a motar suna bin mawakin Buzun mai sunna Bombino bisa wakarsa ta *Arakkham nah*,

Wayarta ce ta dauki kara dan haka ta samu waje ta dan tsaya,

Tana dagawa ta ji yana cikin kayaniya dan haka bai tsaya sun yi wata doguwar gaisuwa ba ya isar mata da sakon inda zata tardo shi yanzu yanzu ,

Da to ta amsa ta datse kiran tana duban Agaishat ta ce” Wardugu ne, yace mu tarda shi shagon nan na siyar da kaya yanzu ko lafia?

Agaishat ta tsura mata ido bata ce da ita komai ba har ta tada motar ta dauki hanya, Agaishat kam na so tace da ita dan Allah ta ajiyeta ta je ta dawo sai dai ta san bama zata saurare ta ba , dab gaja ta tsurawa hanya ido,

Ita ba komai ke rikitata ba sai irin yanda gabanta ke faduwa idan ta hadu da shi, ko dan ya cika fada ne? Wani lokacin yana da saukin kai, aman yawancin lokutan ya cika fada da daure fuska, ita kuma tsoron hakan take.,

Sun jima suna tafia kafin ta tsaya kofar tankamemen shagon kayan dakin,

Baki da hanci Agaishat ta saki tana duban wajen da suka tsaya,

Alhinayett ce ta fara fita a motar ,

Gannin Agaishat bata fito ba ta leka dan gannin abinda ya hanata fitowa,

Agaishat kamar an mintsineta ta juyo wajen Alhinayett ta ce” ke gala, ko dai mun bace da wajen ne? Na ji kin ce yana gudan siyar da gadaje , ke kuwa na ga kin kawo mu wannan waje dake shige da manyan ma.aikata?

Alhinayett ta bushe da dariya ta ce” Agaishat yanzu wannan ne ma.aikatar? Ba na ce da ke ba idan har kin ga waje ki ringa karantawa kar ki yarda ki nuna wani kauyanci ba? 

Agaishat ta shafe gaban goshinta ta ce” hm, ke dai bari, yo ni ta karantawana nake? Wajen gadaje kayan katako an saka su a wannan waje an kilace? Lale du abu idan ya kasance yana da daraja zaka ga an kilace shi, 

Alhinayett ta zagaya ta bude mata motar tana fadin malama fito kar ya kagauta ya yi mana abinda ba shi ba, mu je mu fito mu yi tafiarmu

Tana fitowa ta gimtse dariar da take yi ta kama kanta ta bi bayan Alhinayett,

Sai da suka je wajen wani madubi da mutun da tsaye ya saka dan injin caje mutun din nan ya caje su kafin suke shiga cikin boutik din,

Gaskiya ne, idan har ba kai din dan gayun bane, toh fa ka san wajen, in ba haka ba kana shiga kana iya faduwa fan kallo,

Wannan shi ake kira murmushin amarya, kukan iyaye kennan, 

Tafdi, haduwa, karshen haduwa, tsari, kaya ne na manya,

Saman luntsumemiyar kujera suka hango shi zaune da mai wajen baki daya, 

Yau kam shada ce jikinsa mai ruwan maroon , an yi masa tazarce kawai, ba.ai mata adon komai jikinta ba sai kace karamar shada, abinka da an wanku an jiku sai ta yi bada wani samfari a jikin nasa, ga wata hula da ya kafa yar daidai da kan nasa da ra kuma hau da kayan jikinsa, 

Kai wardugu mai kyau ne,

Hira suke da mutumen, da alama ba yau ya fara zuwa wajen ba, koma sun san juna ,

 Yau baki dayansa annuri yake fitarwa, inda suka tsinci muryar Elhajin na fadin” Oga, ai sai ka fada min gaskiya kawai zaka gwangwaje ne, kai zaka dauki amarya haka? Gaskiya Oga kana ja,

Wardugu ya yi murmushi yana girgiza kai, daidai sun karaso ya ce” aminiyata ke aure ba ni ba, Alhinayett fada masa ko ya bani lafia,

Yana ganninsu ya juya wajen yaronsa ya ce” kai Idrissa, zo kakabe kujerun nan maza, ai ko yanzu aka ciro su a leda sai an goge domin hajiyoyin ne da kansu,

Alhinayett kawai ta yi murmushi tana duban wajen da za.a goge masu wai, wajen sai daukan ido yake a hakama, aman dan da mai ajin suke tare sai suka caje inda suke har aka zo aka goge masu wajen zaman suka zauna,

Gaishe shi suka yi, 

Wardugu ya amsa da lfy, kamar yanda ya saba amsa gaisuwa a datse,

Duban Alhinayett ya yi, a kasan ransa kuwa ya ji kamar ya shige su da fada, wai ita ba zata daina yawo da yarinyar nan ba? Ba zata barta a gida ta yi zamanta ba? Han,

Katon albom aka kawo masu aka ajiye, 

Dubanta ta kai itama wajen Wardugun da yannayin tambaya,

Wardugu ya ce” ki bude ki zabi wa.inda sukai maki 

Kallon kur take masa bata kawar da fuskarta ba dan neman karin bayani ,

Mai shagon ne ya ce” hajia, ai idanma a nan basu yi maki ba sai na yi kira su turo mana sababi ki zaba cikin sati zaki ga kayanki,

Sai da ya gama magana tana dubansa kafin ta maido dubanta wajen Wardugu,

Fuska ya hade ya kawar da kansa,

Ajiye litafin ta yi ta katsa kusa da shi,

Murya ta rage ta ce” Wardugu, me kake nufi?

Wardugu ya ce” ban gane me nake nufi ba? Kayan daki zaki zaba Alhinayett mana, kin san minti nawa na yi a wajen nan ? Ina da taro fa ,

Alhinayett ta juyo da kallonta wajen Agaishat, gani ta yi ita kawai ta tsurawa wata agogo ido mai ruwan dawisu sai kyali take ta hadu karshe,

Dubanta ta maido wajensa, hannayenta ta hade waje guda ta ce” Warsugu, kennan zagin nawa da ake cewar na makale maka wai kawance dan dai na tsotsi abin hannunka ne zai tabata? Wardugu, kayan dakin ka rasa a inda zaka siya min sai a wannan tsadaden shagon da idan ba isa ka yi ba zaka saka kafarka bama koda dan kalo ne? Wardugu Abanna me zai ce? Wardugu wahalar ta isa haka, dan Allah ka rufa mani asiri ka bar maganar kayan nan ,

Wardugu ya zaro ido da mamaki, murya a kausashe ya ce” ni zaki rainawa wayo Alhinayett? Ni zaki fadawa irin magangannun nan? Ni?

Da sauri Agaishat ta juyo da dubanta wajensu, mikewa ta yi tsaye domin ta ga ya nuna Alhinayett da yatsa alamun ransa ya mugun baci, 

Muryarsa ta kuma ji ya ce” walahi yau da wata ce ta mani irin haka sai na dauke mata hakora kafin ta karasa maganar, an gaya maki ni sakarai ne mai daukan jita jitan mutane? Ko qn gaya maki idan ban yi magana da Aban ba zan yi gaban kaina? Malama da na kiraye ki ki zaba dan na san halayenku mata da shegen tsare tsare ana iya zabar maki ki ce basu yi maki ba! Ki zaba ku bace min da gani kuma idan na kara gannin wacen ba hijab sai na kade ku! 

Hawaye ne ke zubar mata a idannuwanta, wasu na korar wasu, rayuwa kennan, ita ta taba tunanin zata hau irin wannan gadon? Wajen Agaishat dake tsaye tana kikifta ido ta dawo da sauri ta dauki litafin ta mika mata ta ce” zabar min,

Agaishat ta dubeta ta canza harshe zuwa yaran buzanci ta ce” me kuma mukai masa da zai kade mu? Yaushe ne zai kade mun? Kuma muna cikin motar za.a iya kade mu daman? Kin ga Ayya amanata ta baki idan kika bari ya kade ni ke da ita ne.

Alhinayett ta ce” Agaishat kin manta yana jin yarenki ne?

Da sauri ta zaro ido, ran harga Allah ita ta manta da yana jin yarenta, dubanta ta waiga wajensa ta ga yana danna waya, da alama bai jita ba, dan haka ta sauke ajiyar zuciya ta ja Alhinayett suka kara matsawa tana duban har yanzu ta ki yin shiru,

Hannu ta dago tana dubanta ta ce” to wai kukan fa?

Alhinayett dake shasheka ta ce ” Agaishat, wai na zabi kaya fa yace? 

Agaishat ta ce” to menene?

Alhinayett ta ce” Agaishat, ba zaki gane ba,

A wajen nan kayan masu tsada ne na yayan gata, sun fi karfina, ni wa? Yar wa?

Agaishat ta yatsina bakinta wanda du idan ta yi sai dimple dinta ya loma, ta karbi litafin ta shiga dudubawa,

Hankalinta kwonce ta kallo tana ta santi a ranta, a fili ta ce” kin ga ni na rikice, karbi ki zaba, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button