BAK'A CE 1-END

BAK’A CE Page 61 to 70

Alhinayett ta karba ta ja hannun Agaishat har gaban Wardugu dake dan zantawa da Elhaj, duda ransa a bace aman yana amsa shi,

Suna zuwa Alhinayett ta ce” War?

Wardugu ya dubeta bai bata amsa ba,

Ta ce” ka yi hakuri, na tuba????????,

Idannuwansa ya dan lumshe ya bude a kansu,

Alhinayett ta turo Agaishat gabansa, irin sosai ta matso kusa da shi domin turota ta yi da biyu, ta ce” Agaishat, ki taya ni godiya wajensa, bani da bakin gode masa ki kama mani,

Agaishat ta zaro ido ta juyo da dubanta wajen Alhinayett , kafin take juyawa kusa da shi,

Kamshin turaransa ne ya saka ta fara jin wani irin dadi a ranta, 

Wardugu dake kallon kasa kasa ya shiga wani yannayi na jinta gashi gata, 

Agaishat ta shiga kame kame tana dan shafa gaban goshinta,

Dago idannuwansa ya yi ya zuba mata saman fuskarta, yanda take shafa fuskar tana dan waige , tana kuma kallon wajen da yake abin sai ya saka shi nishadi, irin ta daburce ne? Ai kuwa sai ya saki murmushin da ya nuna fararan hakoransa,

Yan wushiryarta ne suka bayana na sama wajen hakoranta biyu da suka dan yi kasa kamar na zoma sai dai basu fito sosai ba sun bada wani kala mai birgewa da tsari ne, suka bayanna, ta lumshe manyan idannuwanta ta bude ta ce” Mun Gode, Allah ya kara arziki, Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kaima masu yi maka domin Shi????????,

Bai iya amsata domin yakan zama wawa a duk lokacin da suka samu kusanci irin haka, shi ya sa ya daina yawan zuwa gidan Ayya, domin a gidan Ayya wani lokacin yana tarar da ita tana zuba tabara shi kuwa uwa wawa sai ya saki baki da ido yana rakata da kallo yana sakin murmushi ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀ 

                  Paris

Alhamdulilah, jiki ya yi kyau, a hankali har ya fara dan fita daga gidansa yana gannin gari ya koma,

Khadija dake fama da shi ta fara kosawa kan maganar aurensu aman abin mamaki ya nace aa, ba yanzu ba, shi ba zai iya auren da ba Wardugu ba, shi sai wardugu ya aminta zai iya auren ko wace mace!

Takan ji takaici da gannin bai san darajarta ba, sai ta nuna ta yi fushi , sai ta kasa ta dawo ko dan ya ci abinci dan idan bata nan baya ci! 

Kamar yau yana zaune yana kallon fulawowin tsakar gidansa,

Iska mai dadi na busa shi ya…..

???????????????? *BAK’A CE* ????????????????

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp

*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________

             

*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????

                            Na

                     *SAJIDA*

                          6️⃣6️⃣

Kai jama.a ni dai wollah Azumi????????????????

Iska mai dadi na busa shi yana mika hannunsa a kai a kao yana dan tsigo fulawar ya sinsina hat sai ta yi laushi sai ya zubar ya kuma tsinko wata,

Tsaye take bayansa tana dubansa, ta dan dauki lokaci kafin ta juya ta shige gidansa ta dauki wayarsa ta dana masa kira,

Ya jima, kai harma ta cire rai da zao daga domin ta kira ta kara bai daga ba , da kyar dai ya daga bai yi magana ba sai dan hayaniyar muryar Alhinayett bakinta ya kasa rufuwa dan murnar abin alkhairin da ta samu na aurenta,

Salama ta yi a hankali na wajen uku kafin yake amsawa shima,

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce” Wardugu Khadija ce,

Wardugu ya ce” na gane,

Khadija ta yi tsam ta ce” Wardugu kun san gaba ta fi kwana uku salar mutunma ba.a karba?

Wardugu ya ce” eh na sani,

Khadija ta cire wayar da mamaki a kunenta, kafin take maidawa ta ce” kun sani aman kuke yi?

Wardugu ya ce” ke din wa ya baki damar kirana ki min tambaya irin haka? Ni mace ne da zan tsaya gaba da wani? 

Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce” Dan Allah ka yi hakuri, baya jin maganar kowa idan ba taka ba, 

Me saurayin naki ya yi maki? Ya tambayeta kai tsaye,

Wata kunya ce ta kamata, kennan ya san halin da take ciki ko me? Ai tunda ya sani bara kawai ta fito a mutun, ta ce” Wardugu, ya ki maganar aurenmu, yana irgawa Agaishat ta fita a ida, wai shi sai ka yafe masa, dan Allah ka yi wani abu, idanma hada mu za.a yi a yi auren ni da ita in dai zaka yafe masa dan Allah ka yi,

Idannuwansa ya rintse, ya jima kafin ya bude ya furzar da wata iska ya ce” haka yake tunani ko tunanin ki ne?

Khadija ta ce” neman mafita nake,

Warsugu ya girgiza kai yana murmushi ya ce” ki iya da shi kin ji? 

Kit ya datse kiran,

Juyawa ya yi wajen da suke, ta daura mayafin a kugunta ta yi tsaye gaban katon madubin dake jikin bed din da Alhinayett ta zama tana juyi suna daria wai ga yanda Alhinayett zatana yi a dakinta ita daya gaban madubi, 

Dubansa ya kai wajen Elhaj ya ga yana tsaye shima yana dariar domin tana abin ne gwanin sha.awa,

Ji ya yi ransa ya baci da hakan, dan haka ya karasa wajensu ya ja ya tsaya ya gala mata hararar da ta sakata tsayawa bata shirya ba,

Hankalinsa ya mayar wajen elhajin ya ce” Elhaj sun gama ne?

Elhaj ya ce” sauran su kayan kyale kyalen falon Elhajinmu

Wardugu ya ce” ai su je kawai, sauran a duba tsarin kayanta a hada mata wa.inda zasu yi kyau,

Elhaj ya amsa da an gama ya juya wajen yaransa ya shiga basu umarnin yanda za.a shirya kayan a loda maza a kai adres din Alhinayett wasu cikinsu kuwa ya saka su karasa hada abubuwan da ba.a hada ba,

Alhinayett ta karasa kusan wardugu ta tsaya daf da shi, irin idan tana sin yi masa maganar siri ta ce” War, Mu kam mun yi kasuwa a nan fa,

Wardugu dake dubanta daman ya san magana take da shi, dan haka ya yi mata duban bai fahimta ba,

Alhinayett ta ce” Elhajin nan yana ciki fa,

Wardugu ya gimtse fuska yana dubanta dan ta fara gajiyar da shi sai wana masa magana take, ya ce” cikin ina wai?

Alhinayett ta ce” yaja son Agaishat mana,

Wani irin dago da idannuwansa ya yi ya sauke a kan fuskar Alhinayett dake murmushi tana dubansa irin ta yi da biyu dan ta ga reaction dinsa, aman da yake ya fita iya duniyanci sai ya yatsina fuska ya watsa hannayensa yana mai tausar zuciyarsa ya ce” shi zai iya jimawa da ita ko? Dan kam na gaji da yi mata aure ana sakota ,

Ido Alhinayett ta zari tana rufe bakinta da mamakin Wardugu, ta ce” Wardugu har sau nawa ta yi auren? Ai ko abokin ka da ya sake ta bai ganta a haske ba, sannan bai san ciwonta ba, na tabata du wanda ya dauki Agaishan ayya a yanzu zai yi mata rikon gold ne

Ido ya kankance yana dubanta ya ce” meye zai saka a yi mata rikon hakan? Yarintar? Ko kanantar? Kin san me ke rikita maza kuwa? Mace ginaniya, wace idan ta motsa zata motsa da shi ba yar jaririya ba, shima Elhajin Mubarack din nan nake yi masa duban baban yaro ashe dai yaro ne,

Ido ta kara zarowa tana dubansa yanda ya gama magangannun ya gimtse fuska yana kuma kallonta kafin yake juyawa ya ce” ta yafa mayafin nan a saman kanta, 

Tafiya ya yi Alhinayet na kallonsa baki sake, murmushi ta saki kafin take girgiza kanta , ta yiwa Agaishat dake kara kallon kaya magana suka kara gaba,

Ko a wajen gyaran jiki yau da aka fara jika jikin Alhinayett da turare haka ta kara kudin wajen Agaishat itama aka shiga yi mata sak irin gyaran amare, 

Tsume tsumen nan da ake basu kansa tana shanye abinta kai tsaye inda Alhinayett ke yi mata kallon ta san ko na meye tunda ta taba aure, hakan ya sa itama ta kama abin da karfi karfi gannin wace ta taba aure batai masa da wasa ita kuwa Agaishat na sha ne dan dadi yake yi mata, ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button