BAK’A CE Page 61 to 70

Sosai suka wuni cikin farin cikin da Wardugu ya saka su, suna dawowa suka tarar d Ayya a wajen hutunta tana zaune da jarida a hannunta,
Gannin su ya saka ta ajiye jaridar hannunta tana dubansu da yalwatacen murmushi a fuskarta dan yau an yi masu dilka sai sheki suke,
Suna zuwa Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat kadan ta duka har kasa kanta na kallon kasa ta ce” Ayya, ina rokon Allah subahanahu wata.ala ya kara rufa maki asiri ke da kika yi silar zuwan Wardugu duniya da mahaifinsa da dukan wani wanda ya shafe shi, ya Allah ya yi maku sakaya da gidan Aljana, Allah ya rabaku da kunyar duniya da ta kiyama, Allah ya…..sai ta yi shiru sanafiyar hawayen dake zubar mata ,
Ayya ta dafe kanta ta ce” ya salam, Ke Alhinayett tashi tashi maza goge hawayen ki, menene haka? Haka Mahaifin ki da da maman ki basu dade da fita a gidannan ba, ke idan bai yi maki haka ba , ni da kaina sai na ga bakinsa irin yanda kuke tare da zuciya daya? Maza daina wani kuka ba yayanki bane?
Alhinayett ta shiga share hawayenta tana duban Ayya,
Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana duban Agaishat da ta yi narai narai ta ce” kin ci abinci kuwa?
Agaishat ta daga kanta,
Alhinayett ta dungureta ta ce” ta sha solani dai, bata ci abinci ba,
Ayya ta dafe kai, ta ce” kin ga, frij cike yake da kalolin solani tunda na fadawa Wardugu ta mayar da solani abincinta ya kasance kafin ta gama da ta frij an kawo wasu an cika a frij, du wajen yarar gidannan ki ka duba zaki ga ledojinsu na yawo a ciki, tsorona ya saka mata ciwon ciki gata ba shan maganin zafi ba sai ina tsaye,
Ayya ta karasa tana dafe kanta,
Agaishat ta zauna gefen kujerar da take zaune ta dora kanta saman jikin Ayya ta dora hannunta wajen jaridar da ta ke karantawa ta ce” Ayya, wai mai siyar da kayan gadajen nan ya ce yana so na,
Ayya ta zaro ido tana dagata daga kwonciyar da ta yi kamar mage ta ce” ke kuwa ki ka ce da shi me?
Agaishat ta dubi Alhinayett ta ce” ni kalon sa na yi, kafin nake dan motsa bakina, na kada kaina sai kuma na yi gaba na bude motar Alhinayett na zauna na sada kaina, kin ga ban nuna zumudi ba, ban kuma yi masa rashin kunya ba, ko Alhin
Ayya ta yi murmushi tana duban Alhinayett ta ce” Alhinayett zauna mana,
Alhinayett ta zauna sosai, dan ta lura yau Ayya na yi da ita, ta sake mata fiye da kulun, dubanta ta kai wajen Agaishat ta ce” auta, dauko min faro,
Agaishat ta mike ta nufi ciki
Ayya ta dubi Alhinayett ta ce” Alhinayett, ki yafe ni kan wasu abubuwan da nake nuna maki kin ji? Kin san rayuwa, yau ko Wardugu na dan cikina dole na saka ido a mu.amalarsa da kowa bale mata, gashi a zamanin ku ake kawance mace da namiji, har ga Allah na sha saka shi gaba da fadan ya aure ki sai yace da ni kawarshi ce ba zancen soyaya tsakanin ku, hakan ke saka ni a halin tsoro , idan kika yi duba da tsakanin mace da namiji akoy shedan,
Alhinayett ta gyada kanta tana duban kasa ,
Ayya ta ce ” tun yaushe mahaifiyar ki ta rasu?
Alhinayett ta dago da kanta tana duban Ayya, ya aka yi ta ji? Sai dai bata da amsa ta san tunda ta yi mata tambayar toh tana da labarin yanzu, dan haka ta ce” rasuwar mamana , wani soja ne ya kadeta, kuma sojan mahaifinsa ne baban mutun hakan ya saka suka rufe akama ki bin maganar,
Mafarin haduwana da Wardugu kennan, ba wancen labarin ba, domin na je na kai masa kukana, na fada masa komai hakan ya sa ya yi bincike, cikin ikon Allah ya tarbi abin da karfinsa inda ya samu baban Alkalin nan datijo mai sunna *Gukunni* ya zama lauyana a lokacin baban lauya ne da ake shayi , nan ya shige gaba suka hada karfi da karfe cikin ikon Allah suka kada shari.ar , dalilin da ya saka mahaifina ya cirewa Wardugu shamaki da cikin gidan mu, dalilin da ya saka na samu sa.ar zama abokiyar Wardugu, har ake mamakin irin kusancin mu da irin yanda muke hira da Wardugu, kuma duda haka sau biyu yana yi min dukan da ba zan taba mantawa ba , dayan kan karatuna da na so na yi wasa da shi, ya yi magana ya yi magana na kiya har Abana ya bashi damar ya yi maganina, a ranar sai da na kwana asibiti, na biyun da na fara samari masu hatsari, irin yaran nan yayan masu kudi dake hurewa yara kunne, suka so su saka ni a uku a lokacin yana Spain, ya yi min nasiha, ya gwada min ilar abin du na kasa fahimta sai da ya dakar min fata na suma sau biyu , tun daga shi na yi byby da samarinma baki daya sai yanzu Allah ya yi,
Ayya ta girgiza kai tana dubanta kafin ta yi murmushi, ta ce” daga yau ku daina zuwa gyaran jikin, in sha Allah zan karasa maki a gida,
Godiya Alhinayett ta yi ta yiwa Ayya har ta dakatar da ita,
Ayya ta hangi Agaishat tafe da faro ta ce” kin san menene, ina son Agaishat tamkar yar da na haifa a cikina Alhinayett, na yi sake aurenta da na tashi na baiwa yara haka , har ina tuhumar kaina da ni na haifa zan ko yi haka? Ina jin haushin kaina,
Alhinayett ta ce” Ayya, ba maganar sake, abinda Allah ya tsara sai ya kasance a kan bawansa, aure kuma ai lokaci ne , idan ya yi ko a halin yaya sai an yi shi idan kuwa lokacin mutuwarsa ya yo komai so sai an rabu, Agaishat na girmama girmanki a zuci da fili, bata taba nuna laifinki kan komai ba, koda ta san ta yi laifi takan yi murmushi ne tace Ayyana zata min fada, kuma ta je ta kasa barci, kin ga kuwa karara shakuwa ta iyaye ta bayana a lamarin,
Ayya zata yi magana ta karaso dan haka ta yi shiru, ko ba komai bata so ta san irin girman son da take mata dan karta sangarce mata, Agaishat duka duka bata fi 21 ba, har yanzu yarinya ce
Wardugu ne zaune da waya a hannunsa yana amsa kiran Elhaj Mubarack,
Elhaj Mubarak ya ce” Elhaj, nafa ga iri a wajenka,
Wardugu da ya dago zancen , ya gane inda ya nufa sarai, ya san me yake son fada masa , dan haka sai ya dantse lebensa na kasa yana sauraronsa,
Elhaj Mubarack ya ce” zan so a bani na kai gidana, wannan Hajia ce , sai Elhaj Mubarack,
Wardugu ya lumshe idannuwansa, bai san lokacin da ya ce” wai menene a tare da ita dake saka mutane bibiyarta ne?????????
Elhaj Mubarack ya yi wata dariya ta manya yana lumewa cikin kujerar falonsa inda matarsa ke gefe zaune tana zuba abinci tana jin abinda yake fada ya ce”……….
???????????????? *BAK’A CE* ????????????????
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER’S ASSO????* ____________________________________________
*Fad’akar da al’umma tare da nishad’antar da masoya shine fatanmu*????????????????
Na
*SAJIDA*
6️⃣7️⃣
Sai da ya gama murmushi ya shafa gemunsa ya kara kafin ya ce ” Elhaj, ai fure ce, zan so na yi mata yayafi,
Wardugu ya rintse idannuwansa, kansa ya kawar kafin yake ajiye wayar ba tare da ya kasheta ba,
Jikinsa ya matsa ya jinginar da jikin kujerar da yake kai, idannuwansa ya lumshe yana mai jin wani tukukin tashin hankali na taso masa daga zuciyarsa yana yin sama,
Idannuwansa ya rintse irin ruf din nan ya shiga kokowa da zuciyarsa, aman ina ya kasa ba zai iya ba!
Mikewa ya yi rai bace ya dauki kys din sa ya fito yana gannin garin ya yi duhu sosai ,
Motarsa ya shiga ya bale da gudun gaske ya yiwa gidan Ayya tsinke,