Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 25

Har cikin mota Anne ta kawota, tare da sake musu addu’a domin tuni ango shi ya shiga fadarsa. Amaryarsa kawai yake jira a kai masa.
Har suka iso a tafiyar da bata gaza mintuna a shirin ba saboda jiniya da aka sakama motocin yasa akaita basu hanya, wannan yasa suka iso cikin ƙanƙanin lokaci. Amarya dai bata buɗe ido ba yanzu ma. Sai dai kunnuwanta naji mata yanda ƴan rakiyar tata ke ta yaba wannan katafaren gida first class. Tsirarun ƴan uwanta kuwa da akazo dasu rikicewa sukai. Bataga laifinsu ba, dan masu shiga ƙasashen duniyar ma da kuɗin ƙugunsu sun yaba balle su.
Ita dai babu komai a ranta sai addu’oi, dan zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi musam da kalaman su aunty Hannah ke dawowa a cikinta tamkar bitar karatu, sai dai Alhmdllhi mafitar data samu a safiyar yau da matakin data ɗauka tana fatan zuwa yanzu an kauda matsalar farko da takema fargaba kafin masu zuwa. Kamar yanda Anne ta gargaɗeta da yin addu’a haka ta dingayi a duk takun da zatayi har suka iso ainahin cikin babban falon farko na gidan.
Gaban Raudha yay masifar faɗuwa. Tai azamar rumtse idanunta tana ambaton sunayen ALLAH masu tsarki, daga haka bata sake fahimtar komai ba har suka iso inda aka sanar mata falonta. Kamar yanda Hajiya Zuhrah da suka iske gidan suna jiransu ta ambata, ita da ƙanen Ramadhan biyu dake aure Mardiyya da Safina, sai wata cousin ɗin su Pa itama mace mai kirki hajiya Mariya, tun sanda za’ai rakkiyar shugaban ƙasa suka shigo tawaga akai masa rakkiya tare da su.
“Inaga mu barta iya nan kawai, shi mijin nata idan ya shigo da kansa sai ya kaita ɗakin da yaga ya dace su zauna ko?”.
Cewar Hajiya Mariya. A tare su hajiya mama suka nuna gamsuwa. Sai dai aunty Hannah ta taɓe baki dan tasan sun riga da sun zaɓa musu ɗakunan da zasu rayu ta hanyar saka ƙaramin symbol a saman ƙofar bedrooms ɗin ta ciki bisa shirinsu. Dan haka cikin kwantar da murya tai magana tana duban hajiya Mariya da murmushi. “Amma auntyna ayi amarya a falo? Kodai muyi haƙuri a kaita nata bedroom ɗin yazo ya sameta kamar kowacce amarya shima, koba komai zai tabbatar shima a yau ba shugaban ƙasar NAYA kawai yake ba, ango mai amarya fil a ledarta ne”.
Yanda ta ƙare maganr da ɗan shakiyanci ya sakasu sakin dariyar manya. Hajiya Mariya mace mai sauƙin kai da fahimta. tace, “Kumafa kin fini gskiya ƴar uwa, dan gara ya tabbatar da gaske muke yau muke son jika da izinin ALLAH”.
Nan ma dariyar suka sanya, tare da kama Raudha da kanta ke lulluɓe har yanzu, dan sam bama fahimtar zantukan nasu take ba ita kam. Har bedroom ɗin da suka zaɓa mata aka kaita, sai dai kuma an samu akasi ba wanda su aunty Hannah suka tanada dominta bane. Amma batace komaiba, ta barwa ranta zata dawo da kanta tasa Raudha komawa can ɗin cikin sauƙi.
Anan ma dai su Hajiya Mariya Nasiha suka sake mata mai ratsa jiki, kafin su tattara su fito suna mata sai da safe.
Sai a yanzu Raudha ta samu damar rushewa da kuka. Ta zame ta kwanta kan katafaren gadon da tasan ko bata kallaba ya haɗu harya gaji. Ji take inama ba’a haifeta tazo duniya ba, inama Abbansu bai saki momynsu ba har sukazo Bingo. Inama ranar batazo idi ba har ƙaddara ta sakata shiga hurumin Alhaji Hameed Harith Taura. Inama… Inama…. Inama. Sai dai bakin alkalami ya bushe, bushewa irin wadda idan akace sai an tausasashi karyewa kawai zaiyi yabar tawada dabin yatsun hannu.

Kuka taci sosai a wajen har kusan rabawar dare, Ba kuma tako ɗaga mayafin nata ba balle ta kalli wani abu daya shafi ɗakin kamar yanda bata kalli falon da gidan ba sanda zasu shigo, wani wahallen barci da zazzaɓi suka fara fisgarta, duk da kuwa kafin yau tasan tana da burin ganin fadar shugaban ƙasa tamkar kowane ɗan ƙasa. Har lokacin babu angon nata babu alamarsa, ta riga da ta fidda rai da shigowarsa, duk da dama bata sanya ran hakan ba tun farko. Tasan bata kai kodarajar ma’aikatan gidansu ba. Ya amshi aurentane kawai saboda halacci ga kakansa. Bazai sota ba, kamar yanda itama batajin son sa ko kaɗan a ranta. Sai dai tana tausayinsa matsayin shugaban ƙasarta dake cikin wani tarko mai wahalar sha’ani da nazari ga wanda baida yawan maida hankali akan abu. Harga ALLAH tana cikin razanin zantukan su Aunty Hannah har yanzu. Dan ko maganar aunty Hannah taji a kwanaki ukun nan ji take kamar ta saki gudawa a wando saboda razana da mamaki. Yanzu miya kamata tayi a wannan ranar da tasan shugaban ƙasa zai fara kwana a ɗakin da take da tabbacin an haɗa Poison da suka ambata cikin ac ɗin tunda bata da tabbacin saƙonta ya kai ga Bappi zuwa yanzun? Zata fito ta sanar masa ko zata jira taga idan saƙon nata yay nasarar kaiwa, ko yaya zatayi?. Wa zata tunkara da sauran batun ya bata shawara ne? Idan ta samu nasarar daƙile wannan ta poison ɗin ac?. Wane damar yunƙurine da ita a wannan dare na farko a gareta na shiga BAƘAR INUWA tare da shugaban ƙasarta?, idan tayi yinƙurin faɗa masa ya tuhumeta da a ina ta sani wace amsa zata bashi?, idan ta iya faɗa masa komai tanada tabbacin zai yarda ba turotan sukai ba kamar yanda su can yake a garesu zasuyi amfani da ita ne wajen cutar da shi. (“Ki daina yaudararsu, ki kuma tabbatar musu ke BAƘAR INUWA ce. Idan kikai wasa da gargaɗina ni zan zame miki BAƘAR INUWAr da sai kin gwammaci GARA RANA DA NI!) furucinsa a randa ta fara ganinsa a TK special hospital tare da kakansa, cikin halin ciwo take amma ya rumtse ido ya faɗa mata waɗan nan kalaman da tasan sune gaskiyar abinda ke a ransa. Inaga yanzu kuma da take cikin mugun ƙullin da bashi kaɗai ba, mutane da yawa ma idan suka ji bazasu fahimceta ba. Dan kuwa ba kowa ya gama yarda domin ALLAH ta bama dattijo Alhaji Hameed Taura garkuwa ba ranar idi, ciki kuwa harda mijinta, shugaban ƙasarta kuma a yanzun..
Da wannan tunanin barcin yay galaba a kanta………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button