Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 27

BAYAN KWANKI BIYU

Yau kwankin shugaban ƙasa da amaryarsa biyu kenan a gidan gwamnati, sai dai tunda suka shigo gidan babu wanda yaga ɗan uwansa. Dama Raudha bata saka a ka ba, sai dai duk sanda za’a nunasa a television takanji wani iri a ranta tamkar mai ganin laifinsa. A gefe kuma tana yaba iya tsara adonsa da kyawun haiba da ALLAH ya bashi. Shi mutum ne da ko yaya yasa sutura ko badan kwalliya ba saita nuna kanta a jikinsa, koda bamai muhimmanci bace da rashin tsada. Abu mafi ɗaukar hankalinta shine ƴar tsagar kan girarsa dake nuna tamkar irin ta gayun zamani, tunaninta ya tsayane kawai akan ya bada wanzami yay masa hakane saboda gayu. Bama ita ba, mafi yawan mutane haka suke fassara tsagar dake kwance da wani salon style tamkar an tsara bisa girarsa ta dama.

 

Da ace tanada dama da saita masa tambaya akan tsagar. Ba komai yake mata daɗi ba a gidan, musamman abinci da kaɗaici suna sukar ranta. Sam girkin su kuku baya mata ɗan ɗanɗano a baki, ga kewar momynsu da ƴan uwanta musamman Yasmin da suka shaƙu matuƙa. Kai har ƴan hutawa kewarsu takeyi sosai. Sai kwaɗayin karatunta na islamiyya. A tarewar tasu sau uku tai baƙi manyan mata masu ji da kansu da zasu iya haifarta har jika da ita ma, wai matan gwamnoni ne sunzo gaisheta. Sai wasu kuma matan manyan ƙasar ne ƴan siyasa.

 

Ita dai nata gaisuwane a garesu da godiya. Dan duk da ƙarancin shekarun Raudha nasihar sayyadi Abubakar ta jima da maidata mai halin manya. Tanada nutsuwa da zuciya, ga miskilancin tsiya. shiyyasa takeda takatsantsan akan abubuwa masu muhimmanci. Ba komai takema garaje da rawar kai ba har saita nutsu ta fahimcesa. Hirarsu Aunty Hannah na taka rawar gani wajen bude mata ido da sanya ido ga duk wanda zai raɓeta a yanzun. Dan zuciyarta ta kasa yarda da kowa da komai na gidan. Kullum kuma cikin yin nazarin ta yaya zata kuɓutar da shugaban ƙasa take.

A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa yayi matukar zama busy ne. Sam baya samun kansa yanda ya kamata a kwana biyun nan da fara shigarsa office. Wani abu daya faru randa ya fara zuwa office ya sakashi fara binciken wani abu akan jerin sunayen cabinet ɗinsa da suka tattauna akan zai naɗa. Sai dai kuma yana gabatar da su ga mashawartan nasa wasu a cikin manyan jam’iyyasa sukayo masa ca akan akwai tsarin da sukebi wajen naɗa cabinet na shugaban ƙasa. Shi kuma a take zuciyar maza ta motsa yace bai yarda ya hau kujerar dan ya zama a ƙarƙashin mulkin mallakar wasu ba, dolene a barsa da zaɓinsa ya samu abokan aikin da zai sauke nauyin talakawan ƙasa. Ja’inja ta ɓarke sosai a tsakaninsa da su wannan shine ya ƙara ɗauke hankalinsa ga Raudha har ma da su Gimbiya Su’adah data cika tai fam da tunanin ɗan nata na can na rugurguzar amarci da holewa a gidan gwamnti ya manta da su.

Tayi kiransa har sau uku amma bai daga ba. Daga karshe kuma tama bar samunsa kuma bai biyota ba. Abun nan ya sake harzuƙa mata zuciya dajin tsanar Raudha. Sai dai UBANGIJI shine kawai masanin gaibu akan abinda zuciya ke hasashe babu tabbaci. Abinda gimbiya Su’adah bata sani ba shine shugaban ƙasa baima da lokacin kansa. Dan cikin kwana biyu kawai su Alhaji Yaro glass sun gama hargitsa shi, harya fara hange da saka inuwar mulki a jerin BAƘAR INUWA ce kawai ga wanda ya tsinci kansa a cikinta. Wayar da duk family contacts nasa ke ciki a gida yake barinta, hakan yasa taketa kira ba’a ɗaga ba bakuma a bita ba. Daga karshe ta mutu saboda karancin caji. Shugaban ƙasa bai luraba kuma sai yau da kewar su Anne ta ishesa yaga ya dace ya kira.

A gefe kuma yana buƙatar yin magana da kakansa akan wannan rikicin nasu na fidda sunayen cabinet ɗin dake faruwa tsakaninsa da ƴan jam’iyya. Dan bai tunkaresa da zancen bane a tunanin zai iya shi kaɗai, yanzu ko yana buƙatar shawarar sa. Sai da yay ma wayar caji kafin ya kunnata, da saƙon gimbiya Su’adah ya fara cin karo. Yay ɗan tsamm kafin ya buɗe ya duba. Tun a layuka ukun farko na saƙon zuciyarsa ta tsarga da abinda ya ta rubuto, ya ɗan dafe kai yana rumtse idanunsa da cije baki, sai kuma ya buɗe idanun ya ƙarasa karantawa. Missed calls ɗin nata ya duba, kafin ya ajiye wayar yana jan numfashi da ƙyar.

Yasan Maihaifiyarsu mutum ce mai saurin fushi, sannan tanada yanke hukunci akan abu batare data bincika ba. To amma a wannan gaɓar maganarta ta tabbatar masa da cewar tana da hujja, dan kuwa ko Anne idan bai manta ba a ranar ta turo masa wani guntun saƙo itama mai nuni da faɗa akan abinda yay ma yarinyar da shi tunma da aka kawota gidan bai ko ganta ba. Leɓensa na ƙasa ya tura cikin baki yana ɗan taunarsa kaɗan-kaɗan.

Tuni idanunsa da gaba ɗaya sun koɗe saboda rashin isashen barci da samun hutu suka sake rinewa da takaici. Mi yarinyarnan ke nufi da abinda tayi? Itace ta faɗa musu ya aikata wani abu da ita kenan? Maganar mahaifiyarsa ta wancan daren ta shiga dawo masa a cikin kai, sai dai kafin tunanin nasa yakai ko ina kira ya shigo a wayar. Tun kan ya ɗaga yasan Anne ce, dan ita da Pa da Bappi da Maa duk ya banbanta musu ringtone. Cikin furzar da fushinsa ya ɗaga yana kaiwa kunne. Daga can Anne ta ɗan sauke ajiyar zuciya, cikin damuwa tace, “A tunaninmu dawowa ka mulki ƙasar NAYA zai kusantamu da kai ne? Sai gashi yana sake nisantamu Ramadhan ”. Murmushi ya ɗanyi mai sauti, cikin tsokana yace, “Ba kune kuka jawo hakan ba Anne.” “Uhm hakama zakace dan gidanku”.

Murmushi ya sakeyi mai faɗi, ransa fal ƙaunar tsohuwar. “Am so sorry sweet Anne na, wasa nake miki”.
Itama murmushin tayi da ga can, har yana iya jiyo sautinsa. Ta cigaba da faɗin, “Shike nan ko waya ma ta gagara muyi da shugaban ƙasar NAYA, sai dai mu gansa a television”.
“Kuyi haƙuri Anne, ni kaina tausayin kaina nakeyi, babu komai a mulkin nan sai baƙar izaya. Wanda ke nesa damu ne suke hangenmu cikin wata ni’imtacciyar inuwa, amma wlhy Anne mulki BAƘAR INUWA ce kawai…”
“Asha Ramadhan! Asha. Karna sakejin hakan kaji, komai na rayuwa jarabawace kawai da rubutacciyar ƙaddara. Ka zama jarumi mai magana ɗaya kawai, sannan jajirtacce wajen tunawa da ɗunbin talakawan da suka dage rana da dare wajen ganin ka zama shugabansu. Ka kuma zama mai haƙuri da juriya kamar yanda na sanka kaji”.
Numfashi ya sauke mai nauyi, cikin ƴar nutsuwar da kalamanta suka bashi yace, “Inaha ALLAHU Anne nagode sosai ”.


“Babu damuwa. Ina Aminatu? Yanda kai wahalar ji itama tayi, har yanzu ban samu damar jin yaya jikinta ba haɗani da ita”.
Ɗan jimm yayi na alamar ɗaukewar numfashi, sai kuma ya shiga lalubo abinda zaice domin kare kansa. Sai dai ƙarya ba halinsa bace, dan haka harshemsa ya suɓuce wajen faɗin, “Tana ɗakinta”.
Kamar Anne zatace wani abu sai kuma ta share, sai kawai tace, “Daure ka haɗani da ita naji yaya take?”.


Baida wani zaɓin daya wuce bin umarninta. Dan haka ya amsa mata da cewar, “To Anne zan kira”.
Komai bata sake cewa ba ta katse kiran. Miƙewa yay cike da nutsuwarsa, ya ɗauka t-shirt mara nauyi baƙa ya sanya, tare da baƙin 3quarter na wando. Ya shigo gidane da wuri saboda burin yin barci, dan ko sallar magrib da isha’i ma a massalacin gidan yayi su. Slippers masu taushi baƙaƙe ya saka a ƙafarsa ya nufi ƙofa, sai kuma ya tsaya cak riƙe da handle ɗin ƙofar, dan haka kawai ya samu kansa da buƙatar sanya turaren da bai sakama jikin nasa ba, sai dai duk da haka yana ƙamshin sabulan wankansa, suma kayan suna nasu ƙamshin na kaya da yakan ajiye a Wadrobe, tun yana ƙaraminsa Anne ke masa haka, koda ya girma abin ya zame masa jiki koda yaushe zaka samu turaren kaya a Wadrobe ɗinsa.


Komawa yay da baya-baya yana ɓata fuska tamkar wanda akaima dole, ya sako turare kala biyu masu sanyin ƙamshi sannan ya fice. Duk wanda ya kallesa ya kalli yanayinsa dolene ya dangantashi da mutum mai girman kai, dan ko a tafiya abinda ke gabansa kawai yake kallo, sannan ba kowa bane yake ganin ya isa ya saka a sabgar rayuwarsa koda ta magana ce. Ko abokai sai ya gadama yake kula wasu. Ba kuma wai dan baya magana bane ko dariya, dan ko kusa baya kama da miskili. Mutum ne shi mai surutu a inda yaso ga kuma wanda yaso……….✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button