BAKAR INUWA 29
Episode 29
……………GOVERNMENT HOUSE
Tattaunawar sa da dattijan ya bashi ƙwarin gwiwa sosai. Dan yaji matuƙar daɗin shawarwarinsu. Da wuri yau ya shigo gida, dan haka yana ɗan watsa ruwa ya fito falon upstairs ɗin domin yin wani ɗan aiki. Da kansa ya buɗe fridge ya ɗauka fresh furarsa da Anne bata gajiya da aiko masa duk bayan kwana biyu. Da ga can gefen falon kujerune guda biyu dake gab da wawakeken glass ɗin dake tamkar matsayin window, sai dai shi zaka iya fita ta cikinsa zuwa barandar upstairs ɗin, daga nan cikin falon kuma zaka iya hango kai kawon kowa dake a ƙatuwar harabar gidan. table ne tsakkiyarsu, sai fitila doguwa dake tsaye wadda zaka iya amfani da ita idan baka buƙatar hasken falon da yawa. Zama yay da bismilla kafin ya buɗe furansa da kilishi dake a cikin kwali. Daga haka ya kunna apple lap-top ɗinsa ya fara aiki a nutse cike da ƙwarewar iya sarrafa keyboard. Sosai ya shagala a aikin dake masa matuƙar dadi, dan tsare-tsarene da suka shafi ayyukan da zai ɗora cabinet ɗinsa a kai. Lokaci-lokaci yakan ciri kilishi ya kai bakinsa koya ɗan zuƙa fura.
Cak yatsunsa da ɗan sakewar fuskarsa suka dakata sakamakon jin kamar shashshekar kuka. Sai dai kuma bai ɗagoba har kusan sakanni talatin. Tabbatar da da gaske kuka ake a kusa da shi ya sakashi sake nutsuwa yana sauraren inda sautin ke fitowa, kafin ya ɗago da ƙyar tamkar an masa dole ya kai dubansa ga inda sautin kukan ke tashi.
Babu yalwataccen haske a falon, amma hakan bai hanashi hango Raudha dake zaune can steps na sauka downstairs ba, ba dukanta yake hangowa ba, iya kafaɗarta ne kawai zuwa kanta, saboda tana zaune ne a steps ɗin kusan tsakkiya ta masa ƙasa da yawa. Ɗauke idanunsa yay da ga kanta, ya maida ga agogon dake jikin lap-top nashi, ƙarfe ɗaya saura na dare. Cigaba yay da aikinsa tamkar abin bai damesa ba, sai dai acan ƙasan zuciyarsa kukan nata na sukarsa. Bai cika san kuka ba, musamman irin nata mara sauti sai jan ajiyar zuciya. Duk yanda yaso cigaba da aikin cikin shauƙin daya fara sai hakan ya gagaresa, dole ya ɗauke hannayensa ya gyara zamansa a kujerar tare da harɗe ƙafafunsa ɗaya kan ɗaya ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe ido yana cigaba da sauraren fitar sautin kukan nata mai haɗe da jan ajiyar zuciya.
Tun yana lissafa sakanni ya koma mintuna, har takaisa ga kusan mintuna talatin babu alamar zatai shiru. Takaicin tsayar masa da aiki ya sakashi jan siririn tsaki ya buɗe idanunsa. A ɗan harzuƙe ya miƙe zuwa makunnar wutar falon ya dannasu baki ɗaya. Warr haske ya gauraye ko'ina.
A matuƙar tsorace Raudha tai saurin miƙewa tare da juyowa. Gabanta yay matuƙar faɗuwa saboda tozali da tai da shugaban ƙasa Ramadhan tsaye jikin ƙarfen benen hannayensa duk biyu zube cikin 3quarter wandonsa. Fuskarsa kicin-kicin yana watsa mata wani irin kallo da batasan a wane aji zata fassarashi ba.
Saurin maida kanta ƙasa tai da ga barin kallonsa, yayinda ruɗanin da kunyar kayan dake a jikinta suka hadu suka dabaibayeta, ta naɗe duka hannayenta a ƙirjinta tana shafa damtsen hannunta dan son bawa jikinta kariya. Kayan barci ne masu santsi da taushi baby pink color. Wando iyakarsa gwiwar ta, hakama rigar mai kamar best sai dai hanunta nada faɗi, ba wata babba bace, dan ta mata ɗas a jiki tamkar saida aka gwadata akayita, sai gashin kanta dake ɗaure a tsakkiya da ribbon yana reto. Raudha tanada gashi mai ƙyau, duk da kuwa bawai yanada tsaho kalar da za'a ce masa irin na indiya ko turawa ba. Sai dai a cikin mutane irinmu dole ne a kirata mai baiwar gashi musamman a yanzu da ya samu gyara na musamman da kulawa wajen Feena a gidan aunty hannah lokacin training ɗin da akai mata, sai ya kara ƙyau da zama abin kallo dalilin halittarta nada alaƙa da jinin larabawa, dan kafin auren bata taɓa sakama kanta relexer ɗin ba.
Kokawa yake da zuciyarsa da idanunsa da ga barin kalonta amma ya kasa, damin kuwa ALLAH ya azurtata da abinda yake matuƙar so ga diya mace. Tun Ramadhan na yaro yana matuƙar son gashi, dan yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙara shaƙuwarsa da Anne cikin ƙanƙanin lokaci a wancan lokacin. Anne nada gashi sosai, haka zai zauna yayta jagwalgwala mata shi wai yana mata kitso ko tsifa. Har ya shiga secondary school bai daina zaman taya Anne tsifar kai ba dan kawai ya samu damar wasa da shi........
“In... Ina yini”.
Raudha ta katse shi da ga shagalar kallonta. Komai baice mata ba, sai dai ya janye idanun nasa a kanta. Bata taɓa jin ya amsa mata gaisuwa ba, dan haka yanzu da bai amsa ɗin ba bata damuba ta fara hawowa steps ɗin cike da tsoro da kunya da nufin komawa ɗakinta. Tazo gab da shi zata gitta a bazata taji saukar muryarsa cikin kunnenta babu zato.
“Mike damunki?”.
Duk da ahankali yay maganar bata hanata jin tasirinta cikin zuciya da ɓargon jikinta ba. Kanta dake ƙasa ta girgiza masa, cikin ƙoƙarin danne kukan dake taso mata tace, “Babu komai”.
Komai bai sake ce mata ba, sai ma raɓawa da yay ta gabanta ya koma inda ya baro. Bata cigaba da tafiyar ba har sai da yakai zaune da kusan minti biyu.
Sum-sum ta nufi hanyar bedroom ɗinta batare data yarda ta dubesa ba hawaye na rige-rigen sake sakko mata saman kumatu. Daga inda yake zaune, ƙwayar idonsa ta bita da kallo harta shige. Idanun ya maida ya lumshe tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya ya lafe jikin kujerar yana kokawar danne abinda ke taso masa….
★★★
Tun daga wannan ranar Raudha da shugaban ƙasa basu sake haɗuwa ba. Sai dai kamar kwankin baya, takanji shigarsa da fitarsa gida. Dan takan jima batai barci ba. Takai ko dare ya raba bai shigoba sai taji shigowar tasa.
A haka suka kuma shanye satin ya zam satinau uku da aure da kuma shiga gida gwamnatin. A safiyar juma'a kusan 12pm na rana sai ga su Aunty Hannah a bazata harda Hajiyar birni sun kawo mata ziyara. Harga ALLAH taji matuƙar daɗi da yin farin ciki, duk da tsananin tsoron al'amuran aunty Hannah a yanzun. Sun samu tarba ta mutuntawa a gareta dama ma'aikatan gidan. Dan Mama Tambaya ce tsaye kan komai har sai da taga kuku ya wadata gabansu da abinci na musamman da abin sha. Bakin Hajiyar birni har kunne tanata zuba santi yau gata a fadar shugaban ƙasar NAYA. Kuma jikarta ke amsa sunan matar gidan, ƴarta matar vice president, kai wannan daɗi ya mata yawa. Ta kama Raudha ta rungume tanata saka mata albarka ko damuwa da ramar datai babu wanda yayi.
Raudha taji daɗin ganin Yasmin da yayunta su Fatisa. Har su fatisan ke faɗa mata aunty Halima zata wuce da su gidanta a Bina su koma makaranta. Hakan ya mata daɗi, dan dama bata son zaman su Fatisa a Bingo hannun su Hajiyar birni gudun kar a saka rayuwarsu a garari kodan rawar kansu, saboda mummynsu bata da wani ƙarfin iko akan komai. Babu abinda zaman nasu zai amfana musu sai ƙara lalacewa duk da taga kamar sun ɗan nutsu yanzu tun sakin da Abbansu yayama Mummy.
Batai ƙasa a gwiwa ba wajen roƙon Hajiyar Birni a bar mata Yasmin anan. Babu wanda yace mata komai akan hakan, sai ma hajiya mama data wani taɓe baki da hararta.
“Oh saboda ita kaɗai kuka haɗa uwa da ita? Yanzu Raudha har idonki yayi buɗewar raba ɗayan biyu tsakanin Yasmin da su Noor?”.
Kai Raudha tai saurin girgizawa, “Lah a'a wlhy Hajiya mama ba haka bane, dama so nake naji idan za'a barmin Yasmin ɗin sai nace itama Noor a bani tunda Asim shi namiji ne”.
Hajiya Mama zata sake magana aunty Hannah ta katsesu. “To inaga mubar maganar haka sai munje gida ma tattauna. Sai itama Asabe a kirata idan ta amince”.
Badan Hajiya mama taso ba tai shiru. Daga haka suka cigaba da hirarsu har lokacin salla yay Raudha ta kaisu ɗakinta dan suyi. Wasun su sunyi alwala wasu na ƙoƙarin yi Asim yace mata zai ƙara shan lemo. Da to ta amsa masa tana ɗan murmushi. Taja siririn gyalen jallabiyar jikinta ta yana ta fito domin ɗauka masa.
Yau ne karon farko da tun zuwanta gidan ta nufi hanyar kitchen, badan ta tabbatar nan ɗinne kitchen ɗin ba. Sai dan taga tanan kuku ya dinga fito musu da abinci ɗazun. Tana ƙoƙarin ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar dake a rufe taji kamar ana magana a hankali, kuma kamar muryar Aunty Hannah data fito a ɗaki tun shigarsu tana amsa waya. Nutsuwa tai ta kasa kunnenta, sai ko tajiyo aunty Hannahr na faɗin,
“Waɗan nan sune kalolin abubuwan da yafi sha kenan?”.
Kuku ya amsa mata da faɗin, “Eh ranki ya daɗe. Amma kamar yanda na sanar miki har yanzu bai taɓa cin abincin gidan nan ba. Amma kullum akayo sharar sashensu nakanga alamar kwalayen anci nama musamman kilishi, sai kuma fura da naga yana shigo da ita da kansa duk bayan kwana biyu”.
“Fura kuma?”.
“Eh ranki ya daɗe”.
“Okay hakan ba matsala bane. Zamuji daga ina ake kawo masa furan da naman ba damuwa. Yanzu dai daga yau duk bayan sati za’a dinga kawo waɗannan kalolin drinks ɗin zuwa nauyin kowanne milk cikin cefanen gidan nan idan zakayo. Sai ka kula sosai wajen zubasu a iya fridge ɗin da yake mu’amula da shi. Maganar abinci kuma zan saka matarsa ta kula da shi akan cinsa dan muna buƙatar ya dingaci ɗin, dan muna buƙatar waɗan nan abubuwan su dinga tasiri a cikin jininsa a hankali yanda babu wani likita da zai iya fahimta da wuri sai dai a ɗauka diabetis ɗinsa ce”.
“Okay Ma baku da matsala da hakan, dan ɗazuma nayi magana da Aunty (forma first lady, ƙanwar mahaifiyarsa ce, uwa kenan take a wajensa, kuma tun yana ƙarami itake tsaye kan karatunsa saboda mahaifiyarsa ta rasu wajen haihuwarsa, a hanun mamarsu first lady ɗin ya tashi ma. Aikine dake buƙatar sirri, shiyyasa ta ɗorasa akai gudun kar aci amanarsu ko a samu matsala. A haka ma akwai abinda ya sani da ita aunty Hannah ɗin bata sanshi ba). Ta ƙaramin bayani sosai dama akansu ɗin da yanda zai dinga amfani da shi a abincin nasa musamman ma shayi. Amma na mata complain akan matarsa, tace babu damuwa itama koda taci”.
Ɗan jim Aunty Hannah tai, sai kuma ta ɗan ɗaga kafaɗa da taɓe baki alamar ko’a jikinta inhar burinta zai cika na ganin mijinta a kujerar shugaban ƙasa wataran. “Ba damuwa idan tacin itama kamar yanda first lady ɗin ta faɗa. Sai dai ka kula, ba kowanne ma’aikaci bane namu a cikin ku, sannan wanda suke namun ma da ga kai sai Tambaya kuka san sirrin aikin da kukeyi”.
“Okay Maa. I promise bazaku taɓa samun matsala daga gareni ba kuma kun sani, Aunty Bushira tamin komai a rayuwa, miye amfanina idan ban saka mata da buƙatarta ba.”
Da sauri Raudha taja da baya wani irin kuka na neman kufce mata, jitai bama zata iya ƙarasa ji ba, babu abinda kanta keyi sai sarawar tashin hankali. Bayan poison na ac bai ishesu ba sai sun haɗa da matakan ingiza ciwonsa, ya kamata tasan wane ciwo ne ke damunsa ma. Bata da tabbacin yunƙurin da tai akan matsalar ac ta karɓu, amma tana addu'a da fatan hakan dan tasan ta tura saƙonta inda da wahala a ɗaukesa shirme. Jin za'a buɗe ƙofar kitchen ɗin tai azamar rugawa karkashin ƙafar bene ta lafe har sai da aunty Hannah ta shige bedroom ɗinta na ƙasa da ta kaisu dan suyi alwala. dan bata kaisu upstairs ba sanin nan ɗin kamar sirrine na shugaban ƙasa.
Sai da tayi ɗan kukanta mamakin aunty Hannah da dalilinta na son aikata duk wannan abubuwan na ƙara kumeta. Dan a iya hasashenta tarasa minene alaƙar aunty Hannah da shugaban kasa da har take gaba-gaba wajen yin haɗin gwiwa da wasu domin kashesa. A gefe kuma zuciyarta na ƙara ninƙaya wajen tunanin zancen farko na sakama shugaban ƙasa poison a cikin ac. Ga wani zasu dinga basa a abinci da drinks? Kai mutanen nan sam basu da imani wlhy. Amma insha ALLAHU ALLAH bazai taɓa basu nasara ba. Zatai iya bakin ƙoƙarin ta na ganin burinsu bai cikaba akan shugaban ƙasa kodan kyakywar zuciyar kakanninsa.
★
Da ƙyar Raudha ta iya danne komai dake a ranta har lokacin tafiyar su yayi, shatara ta arziki ta haɗama kowannensu daga kayan lefenta. Dan sune kawai take takama da su a gidan matsayin nata. Hakama Mummy da Aunty Halima ta haɗa musu tasu tsarabar.
Ta rakasu har harabar gidan tana sharar hawaye. A dai-dai lokacin da motarsu ke fita a harabar farko na gidan motocin shugaban kasa da securitys nasa ke shigowa. Ko ba'a faɗa ba tasan shi ɗinne, dan haka tai shirin juyawa cikin gida tana ƙoƙarin amsa gaisuwar wasu a hadiman gidan da sai yanzu suka ganta.
Shugaban ƙasa Ramadhan da tun tsayuwar motar tasu idonsa ya ganta ya bita da kallo a kaikaice batare da waɗanda ke a wajen zasu iya gane hakan ba. Zuciyarsa ke masa wasuwasi da tambayar su waye ɗin waɗancan da har zata fito rakkiyarsu har harabar gida?. Rashin mai amsa masa hakan ya sashi ɗauke idonsa a ƙofar data shige ya maida ga agogon hanunsa. Ƙarfe huɗu na yamma da wasu mintuna. Ya dawo gidane saboda yana son su fita ita da shi zuwa Taura house gaishe da su Anne. Wannan lokacin kawai ne da shi, gobe idan ALLAH ya kaimu zai bar ƙasar wani taron shugabannin Africa da za'ai a ƙasar Nigeria.
Buɗe ƙofar ne ya saka Raudha dake kwance ɗagowa da sauri har gyalen kanta na zamewa ya faɗi, duk da shi ɗin ta tsammaci gani sai kuma duk ta ruɗe. Cikin in ina take masa barka da dawowa da gaishesa. Kamar kullum yauma bataji ya amsa ba, sai dai idonsa na kanta da har ya sata kasa kallonsa.
“Nanda mintuna talatin zamu fita can gidan gaishe su.”
Daga haka yaja jikinsa baya zai rufe ƙofar, dan dama tsaye yake a jikinta riƙe da handle ɗin. Yana gab da rufewa kuma sai ya sake buɗewa, da sauri ta ɗago sai suka haɗa ido. Cikin azama ta janye nata, yayinda shi kuma ya sake tsuke fuska da faɗin, “Karna sake ganin wannan gashin dokin a kanki ki ciresa”
Babu shiri ta sake ɗagowa, sai dai harya maida ƙofar ya rufe. Hannu ta kai bisa kanta ta damƙo jelar gashinta dake ɗaure da ribbon, a fili tace, “Gashin doki kuma?”. Tai maganar da ɗan waro idanu waje tana miƙewa zuwa gaban mirror. Ribbon ɗin ta zare gaba ɗaya, ta shiga kallon gashinta da tattaɓashi kamar yau ta fara ganin nasa itama, kai kace so take ta tantance na dokinne ko natan?. Ta ɗan girgiza kai tana sakin murmushi, dan harga ALLAH ma dariya ya bata. Yayta wani cin fuska ashe idonsa nakan gashinta. “Kajimun mutum, kawai daga ganin gashi sai kace masa na doki sa'idiniyya”. Ta sake faɗa a fili tana murmushi.
Maganar fitar da yace zasuyi zuwa Taura house ya sata maida ribbon ɗinta da sauri ta nufi hanyar toilet, dan ya kamata taɗan watsa ruwa. Harta shiga kuma sai ta fito dalilin qani tunani da yazo mata arai. Tare da tuna Mummynsu (Asabe) duk da kakarsu Inna ba cika son mahaifiyarsu tai ba a duk sanda zasuje wajenta ko ita wani abu ya kama zataje wajenta koda tare da su Larai ne sai ta sayi wani abun takai mata. Tun tana mata irin wannan ƙyautar tana rainawa da kiransa neman suna har kowama ya fahimci hakan yana daga cikin kyawawan halin Asaben duk da kuwa take tujararriya. Raudha tai murmushi dajin ƙara son mahaifiyar tasu a cikin ranta. (Haka rayuwa take, duk mugun halin bawa sai ka samesa da wani ƙyaƙyƙyawan halin tare da shi koda baida yawa. Hakama duk ƙyaƙyƙyawan halin mutum sai ka samesa da mummuna. ALLAH ya bamu ikon yin ƙyawawan halaye da ƴaƴanmu zasuyi koyi).
A cikin sauran kuɗin data rage ta ɗauka wasu ta fita. Duk da zuciyarta ta gama raya mata daina yarda da duk ma'aikatan gidan hakan bai hanata fita neman mama tambaya ba. Cikin sa'a ma sai ta sameta a falon farko zaune tana kallo. Da sauri ta miƙe ta nufota tana faɗin, “Ranki ya daɗe in buƙatar ganina kike ai basai kin sakkoba, sai ki kirani ta telephone kawai”.
Komai Raudha batace ba sai ɗan murmushi datai mata da miƙa mata kuɗin hanunta. “Mama zan iya samun kilishi mai ƙyau nan da mintuna sha biyar?”.
“Insha ALLAHU ranki ya daɗe zaki samu, dan kuwa sana'ar yarona ne, kum anan yake gab damu ba nisa”.
“Yauwa to Alhmdllhi, gashi yaymin kashi kamar.....” ta ɗanyi jimm tana hasahenshen yawan manyan gidansu Ramadhan ɗin. “Yauwa bakwai. Sai kuma wannan idan za'a samu goro mai ƙyau shima a siyamin”.
Mama tambaya ta amsa tana faɗin, “Insha ALLAHU duk za'a samu ranki ya daɗe”.
Har cikin rai Raudha taji daɗin hakan, ta jiya cikin da sauri. Maimakon ta shiga wankan sai ta buɗe akwatinan lefenta. Duk da tasan sune suka haɗo hakan bai hanata zaɓo turaruka masu ƙyau da daɗin ƙamshi kala biyu ba. Ko ba'a faɗaba tasan zasuyi tsada matuƙa. Ta ajiyesu saman mirror sannan ta koma wajen kayan khumrah ɗinta dake cikin ɗan show glass tana kallo. Taja kusan sakan talatin kafin ta far ɗaukarsu tana dubawa. Aunty Halima ce tai matasu dukansu, Haɗi ne na musamman da ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* ƙamshinsu kawai ya isa sanar da mai shaƙa an kashe ingantattune kuma nagartattu. masu ƙyau da daɗin kamshi ta ɗiba kala uku-uku, sai dai kowanne da kalar kamshinsa, sai turaren wuta kala biyu shima ta ɗiba kashi-kashi duk ta ajiye. Ganin kamar lokaci ya ɗan ja ya sata saurin faɗawa bayi, a gurguje ta gyara jikinta ta fito. Tana cikin shiryawa taji ɗan ƙarar bell ɗin dake tabbatar da ana jiranta a ƙasa. Hijjab tasa ta fita dan tana ƙyautata zaton mama tambaya ce. Ilai kuwa itace da ledoji riƙi-riƙi. Raudha ta amsa tana mata godiya tare da ajiye mata kuɗin data fito da su a hannu. Godiya mama tambaya taitayi duk da ba wasu masu yawa bane............✍