BAKAR INUWA 33

★Tun daga wannan ranar Raudha bata sake jin ɗuriyar Ramadhan ba tsahon kwana biyu, kota shirya abincin safe da Bilkisu ke tsaye kanta kullum yanda suka aje haka kuku ke kwashewa. Dama dai basa shirya lunch tunda sun san yana office. Na dare ma ba'a taɓawa haka ake kwashesa. Raudha bata sanin sanda yake fita balle shigowa.
Yana ɗan bata tausayi, dan ta fahimci sam bashi da lokacin kansa. Gaskiya mulki ba wani daɗi bane ba. Da wahalhalun cikinsa yafi daɗin yawa. Musamman ma irin na Ramadhan dake zagaye da maƙiyansa batare da ya sani ba.
Addu'a ta cigaba da masa, tare da maida hankalinta ga abubuwan da Bilkisu ta duƙufa koyar da ita, wanda take matuƙar jin daɗinsu har tanajin canji a al'amuranta. Duk da ba baƙinta bane, saboda kusan duk irinsu ne su aunty Hannah suka koyar da ita a wancan lokacin. Banbancin kawai tana maida hankali a waɗan nan saboda fahimtar lallai zaman gidan bazai yuwu mata ba sai ta zama mai buɗaɗɗen brain irin na manyan mata. Ba komai ya sata irin tunanin nan ba sai ziyarce-ziyarce da matan manyan mutane irin ƴan majalisu da gwamnoni ke kawo mata cikin gidan. Kallonsu kawai wajen iya tsara ado firgitata suke. Balle a magana da sauransu.
Bata taka kowanne irin mataki da yay kamanceceniya da nasu ba, sai suttura kawai a yanzu da zata iya fin wasu saka masu tsada ma saboda Anne tsayin daka ta tsaya ita da Hajiya Mariya wajen haɗa lefen Raudha da kayayyaki na alfarma saboda hangen irin hakan.
_★★★★__
A ɓangaren Ramadhan ayyuka ne sukai masa yawa sosai, dan a wannan gaɓar suna tsaka da tantance sunayen mutanen da ya kamata su sami mukamai. Sai dai a zahiri bazaka taɓa jin baki ko cewar shugaban ƙasar ba. Sai dai daga bakin mai magana da yawunsa ko mai magana da yawunsa akan yaɗa labarai.
A ɓangaren majalisa kuwa bayan zama da kaikawo akan jerin sunayen cabinet na shugaban ƙasa da aka fitar aka sake dawo da sunayen ofishin shugaban ƙasan. Yayinda shi kuma ya sake maida sunayen ga majalisa a rubuce kan a tantance daga dukiyar kowanne na jerin sunayen. Ma'ana duk suzo su bayyana abubuwan da suka mallaka, hukumar bincike da yaƙi dacin hanci da rashawa kuma ta tankaɗe ta rairaye ta ajiye duk wani documents nasu. Wanda ba'a yarda da nashi details ɗin ba a ajiye sunansa gefe guda baya cikin jerin wanda za'a bama muƙamin.
Tofa wannan magana data fito da ga kakakinsa mai tabbatar da yawun shugaban ƙasa ne ta tada hankalin manyan jam'iyya. Ba komai ya kawo hakan na kuwa sai sanin cewar a cikin waɗan nan mutanen musamman wanda sukai bayar akwai masu kashi a ɗuwawu da yawa. Dan haka Jam'iyya ta bada sanarwar taron gaggawa tare da gayyatar shugaban ƙasa.
Wannan ne karo na farko da jam'iyya ta gayyaci shugaban ƙasa a bayyane tun bayan hawansa kujerar mulki, dan duk bata kashin da akai akan sunayen cabinet da zaɓin speakers na majalisu a rubuce ne data hanyar zaman sirri. Lokacin da kakakin shugaban ƙasa ya isar da wannan takardar gayyata ga Ramadhan ɗagowa yay yana dubansa. Yay ɗan murmushi yana sake maida dubansa ga takardar batare da yace komai ba.
Chief of staffs ya sake risinar da kai cike da girmamawa yace, “Ranka ya daɗe, na riga na shirya saƙon maida musu akan bazaka samu damar zuwa ba, nasan zaman bai wuce akan binciken dukiyoyin sunayen cabinet ba. Gashi a ranar ma kanada tafiya zuwa ƙasar China”.
Ramadhan da har yanzu idanunsa ke kan takardar ya cigaba da nazarinta tamkar mai bita. Sai kuma ya ɗago yana duban cos a nutse, sai dai yanzu babu wannan murmushin na ɗazun. “Tunda zama ne a bayyane zanje, sai dai ka canja musu lokaci”.
“Amma....”
Hannu Ramadhan ya dagama Cos, dan haka ya haɗiye abinda yake son faɗa. COS baiso hakan ba ya jinjina kai kawai. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace har zuwa iya adadin daƙiƙun da zai iya ganawa da shugaban ƙasar ya cika ya fito.
Bayan fitar COS. Da wasu sakanni Ramadhan ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyinsa ya shiga danna-danne. Babu jimawa aka ɗaga kiran da yay. Cikin girmamawa ya fara gaisawa da Bappi, kafin ya zayyano masa batu akan takardar gayyata da jam’iyya tai masa.
Murmushi Bappi yay da ga can. Kafin yace, “Naji daɗi da kai tunanin zuwa ɗin, domin wannan shine kira na farko da jam’iyya tai maka a bayyane, duk zaman da kukai baya na sirri ne. Amma inaga a wannan gaɓar kar kai jayayya da su, duk umarnin da suka baka koda na janye batun bincike akan cabinet ɗinne kayi hakan”.
“Amma Bappi hakan ai tauye hakkin talakawa ne? Sannan zamu iya ɗaura ruɓaɓɓu a lulluɓe suzo suna ruguza mana tsari”.
“Zancenka yana kan hanya, sai dai ka sani Ramadhan bazai yuwu ka samu komai na ra’ayinka hundred percent ba, har sai ka nutsu ka fahimci mutanen man a to z. Dan zuwa yanzu zuciyata ta fara faɗamin akwai manufa a ɗoraka wannan mulkin musamman idan mukai la’akari da saƙon da muka samu daren ɗaurin aurenka da bincike ya kuma tabbatar mana da komai…”
Wani irin kakkauran numfashi Ramadhan yaja, sai kuma ya jinjina kansa cike da nutsuwarsa yace, “Babu damuwa Bappi duk yanda kace haka za’ayin”.
“Thanks you my dear, adai sake dagewa da addu’a, kar ai sakaci da ibadar ALLAH. Duk abinda yazo a nema zaɓin ALLAH, a kuma zartar dashi bisa gaskiya da amanar talakawa da tunawa da rantsuwar da akayi.”
“Insha ALLAH Bappi, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani”.
“Amin ya rabbi”. Daga haka suka ajiye kan wayoyin kusan lokaci guda. Yayinda kowannensu ya tsunduma a tunani ta ɓangarensa.
★★
Kamar yanda Bappi ya ƙara masa ƙwarin gwiwar amsa kiran jam'iyya a yau koda ya baro office kai tsaye falon da zasuyi zaman anan cikin fadarsa ya nufa. Su huɗu ne kawai. Party Chairman da wasu manyan masu faɗa aji a jam'iyyar su biyu. Cikin mutunta juna suka gaisa, domin dukansu sai dai a kirasu iyaye ga Ramadhan ɗin, ballema ta wani fanin duk suna tare da kakansa ne.
Kamar yanda Ramadhan yay hasashe akan maganar cabinet ne hakanne kuwa, dan haka bayan ya gama saurarensu bai wani ja maganar tayi tsayi ba ya nuna ya gamsu da abinda suka faɗa ɗin. Duk da acan ƙasan ransa wani irin ƙuna zuciyarsa ke masa da takaicinsu.
Tabbas sunji daɗin yanda yay musun, dan har fuskokinsu sai da suka nuna hakan, tare da yaba masa na bama jam'iyya girmanta a wannan karon. Daga haka suka cigaba da tattauna wasu abubuwa muhimmai bayan an bama ƴan jarida damar sanin wani abun. Basu tashi a zaman ba sai kusan ɗaya da rabi na dare. Dan haka a matuƙar gajiye Ramadhan ya ƙarasa cikin gidansa. Dole kuma ya dakata ya saurari COS na mintuna biyar kafin ya shige. COS kuma shima ya nufi nasa gida.
Kwanaki sun ɗan ƙara shuɗawa da adadinsu ya kai kusan goma sha, Ramadhan ya ziyarci ƙasar China na tsahon kwana huɗu ya dawo, an kumayi naɗin cabinet da yasaka wasu farin ciki wasu ɓacin rai. Babban farin cikin talakawa a zaɓin matasa da suka shigo tawagar sosai a wannan tsarin ma. Darajar shugaban ƙasa ta sake ɗaukaka a idanun matasa dama ƴan ƙasa, domin abubuwa na zuwa da ba'a taɓa gani ba a ƙasar NAYA. A gefe kuma ana cike da fargabar wasu a cikin cabinet ɗin, domin kuwa ansansu, sun riƙe wasu muƙaman an gani, inda ake yawan zarginsu da handama da baba kere wa dukiyar talaka. Wannan ya kawo ƴan kananun magana ga talakawa ga ma masana akan harkar mulki da siyasa tare da ƴan jam'iyyar hamayya da dama suke jiran ƙiris su hau suka. To komadai miye shi talaka ɗaukarsa a kullum shugaban ƙasa ne keda ikon mulki da zartarwa ga ƙasa, sai dai baisan zagaye yake da masu tilastawa da hanawa ba a zahiri da baɗini, takan kai ma wani lokaci shugaban ƙasa bai isa bayyana ra'ayin kansa ba koda yana buƙatar hakan.
A washe garin da akai naɗin cabinet bai fita office ba sakamakon hutawa na kwana biyu da likitansa ya buƙaci yayi, dan jininsa ya hau sama. Baiso zaman ba sam, sai dai babu yanda ya iya saboda Anne ta saka baki.
Hutune da basai ƙasa ta san zaije ba, domin zai ɗan iya zartar da wasu ayyuka muhimmai da ga cikin gidansa. A ranar yinin farko Raudha batasan wainar da ake toyawa ba, tunda rabon ma ita data gansa tun randa ya dawo China, shima ta fito ne da dare ɗaukar ruwa sakamakon ruwan fridge nata ya ƙare ta shafa'a bata saka an zuba ba sukai kiciɓus da shi a falo yana haurowa daga stairs ɗin fadarsa. Taɗan daburce a lokacin, dan bataso ya ganta da kayan barcin jikinta ba. Ta shiga masa sannu da zuwa aɗan daburce, dan ga kunyar kaya gata tsareta da yay da idanu. Kusan mintuna biyu suna a hakan kafin yay wucewarsa bedroom ɗinsa ita kuma ta saki ajiyar zuciya ta koma ɗaki da sassarfa, ruwan da bata ɗauka ba kenan. Daga ranar kuma basu sake haɗuwa ba sai dai ta gansa a television.
A ɓangaren su Basma kuwa washe garin daya dawo daga China duk suka koma gida saboda gimbiya Su'adah ta dawo, hakan sai ya saka Raudha a tsananin kewarsu da damuwa fiye da farko, dan tanajin daɗin zama da bilkisu da Basma ɗin. Su Lubnah kam tun randa ya maidasu sashen baƙi dama sai ta so ma suke ganinta, hakan ya kawo mata sauƙi sosai da cin zarafinsu.
Bayan tafiyarsu sai ta koma bata da abokin zama sai Mama ladi, tun bata sakin jiki da mama Ladin sosai harta fahimci ƙyawawan halayenta itama. Dan cikin hikima take ɗorata akan abubuwa masu muhimmanci da suka shafi aurenta da zamantakewar mutane fiye ma da yanda Bilkisu ke mata. Kuma Alhmdllhi tana fahimta sosai tare da ɗaura ɗamarar ɗaukar komai.
Kusan sha ɗaya na safe tana bedroom ɗinta Mama Ladi ta shigo bayan ta nema izini, dan tunda mama Ladi tazo gidan aikin mama tambaya ya koma iya falon ƙasa, dama aikinta kula da ɗakin Raudha da zama mai kusanci da ita fiye da kowa. Kawo mama ladi kuma ya nuna Raudha ta sake ta, hakan yama mama tambaya zafi, har takai ƙara wa iyayen gidanta su aunty Hannah. Amma sai suka lallasheta akan karta damu zasuyi wani abu.
“Mama akwai matsala ne?”.
Raudha dake duba littafi ta faɗa fuskarta a sake tana duban mama Ladi data shigo bayan ta bata izini.
Cikin girmamawa tace, “Ranki ya daɗe dama naga su Hajiya Anne ne gaba ɗayansu a gidan nan sai nake tunanin kamar dai babu lafiya”.
Sosai ƙirjin Raudha ya buga, a ɗan tsorace tace, “Suna ina?”.
“Basu shigo ta nan sashen ba. Ta can fadar shugaban ƙasa naga anbi dasu”.
Tunda suka shigo gidan gwamnati bayan wanda sukai mata rakkiya da kawo lefenta su Lubnah ne kawai suka taɓa zuwa gidan a kaf zuri’ar Taura, dan haka Raudha ta tabbatar lallai babu lafiya da gaske. Tun lokacin da yabi da ita ta fadarsa lokacin da zasuje Taura house bai sake ba, amma tsabar ruɗewa batasan ta fita kai tsaye zuwa can ba bayan ta zumbula hijjab har ƙasa da yay mata matuƙar ƙyau kasancewar yanda komai na jikinta ya sake canjawa a yanzu saboda canjin waje da abinci.
Tana kai ƙafarta step ɗin farko ta tsaya cak sakamakon riƙota da akai. Tsabar bugawa da ƙirjinta yayi batasan ta juyo gaba ɗayanta ba. Kasancewar yana gab da ita sai ta faɗa a jikinsa gaba ɗayanta.
“Ya ALLAH”.
Ta faɗa a rikice tana son jan jikinta baya………..✍