Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 36

Ta faɗa a nutse cikin sanyin muryarta data sanyaya sakamakon ciwon da takeji na ɗan taso mata musamman ƙafafunta, tunda tazo gidan batai period ba. dama yakan mata haka wata biyu uku wani lokacin kafin yazo. Ramadhan dake acan falonsa na ƙasa ya ɗan lumshe ido yana sake lafewa jikin kukerar da yake zaune. Sai dai idonsa na kan COS dake daga ɗan gefensa.
“Wa’alaikassalam”.
Ya bata amsar da ta ɗan sata zabura tana cire kan wayar a kunnenta ta kalla da mamaki. Sai dai maganar da taji kamar yana sake yi ya katse mata tu’ajibbin nata ta sake maida wayar a kunnenta.
“Ki sameni a downstairs”.
Wani irin kakkauran numfashi Raudha ta fisgo daga ƙirjinta ta fesar, sai kuma tai tagumi tana jujjuya abun a ranta dan ji take kamar mai mafarki. (Itako mi zata masa yanzun? Yau fa tsahon kwana uku bata gansa ba ma. Kai ko motsinsa bataji ba). Rashin mai tayata zancen ya sata miƙewa kawai. hijjab fari ta ɗauka ta saka a jikinta har ƙasa, sai ta ɗan ƙara turare kawai a jikinta saboda tunawa da shawarwarin Bilkisu.
Sanin downstairs na fadarsa yake nufi ya sata nufar can kai tsaye, dan tunda take dashi bata taɓa ganinsa a falukan da zai kawoka sashen nata ba. Ta can yake shiga tacan yake fita. Inba dare ba bazaka taba ganinsa ko’a falon upstairs ɗin ba ma sai dai na downstairs din. Itako sau biyu kacal ta taɓa zuwansa.
Tun kafin ta gama sakkowa ta ƙare masa kallo shi da COS, kayan data gani a jikinsa jallabiya baƙa da adon golden ya sata tabbatar da ba yanzun ya dawo ba. Koma bai fita a gidan yau ɗinba ma oho masa. Duk da a nutse take tafiya hakan bai hana flat shoes ɗinta ɗan bada sautin ƙarar da ta saka Ramadhan duban stairs ɗin ba ta wutsiyar idanu. Ganin sanye take cikin kayan mutunci ya sashi ɗan furzar da numfashi ya maida hankalinsa ga sakama takardun da COS ya kawo masa hannu.
Da sauri cos ya mike tsaye domin girmamawa a gareta, ya ɗan risinar da kansa yana faɗin, “Barka da fitowa ranki ya daɗe”.
Raudha da taji abin gingiringin ta haɗe yawu da ƙyar tana aro jarumta ta yanama kanta. A tausashe ta ce, “Barkan ka ya ƙoƙari?”.
“Alhmdllh Ranki ya daɗe”.
Cos ya sake faɗa cike da girmamawa. Ramadhan dabai ɗago ba duk da yana saurarensu yay mata nuni da kujerar gefensa da hannu kafin ya ɗan dago ya dubi cos bayan Raudha takai zaune zuciyarta sai faman gudu take a ƙirjinta.
“Barka da dare”.
Ta faɗa yanda take da tabbacin shi kaɗai zai iya jin gaisuwar tata. Bai amsa ba, bai kuma daina abinda yake ba har tsahon minti guda da wasu sakkani. Ya miƙama cos file ɗin da ya gama dubawar sannan ya dubi Raudha data fidda rai da zaton zai amsa matan.
“Kina lafiya?”.
Ya faɗa shima a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa. Ɗan ɗagowa Raudha tayi tana amsa masa a tunaninta har yanzu idonsa akan takardun yake. Ido suka haɗa, tai ƙoƙarin janye nata ya hana ta hanyar cafko yatsun hanunta da take ɗan murzawa a hankali alamar a takure take. A dolenta ta ɗan ware idanunta cikin nashi, shi kuma yay amfani da damar wajen kashe mata ido ɗaya cike da salon da ya nema birkita mata lissafi. Sai dai kafin ta dawo hayyacinta ya ɗauka envelope ɗin saman table ɗin gabansa ya aza mata bisa cinya.
“Ki duba a cikinsu ki zaɓi guards biyu da zasu dinga kasancewa da ke”.
Tamkar mai koyon magana ko mai tsoron buɗe laɓɓa tace, “Amma….”
“Shiiii!!”
Ya faɗa a hankali yana ɗaura pen ɗin hanunsa saman lips ɗinsa tausasa kalar pink. Dole ta haɗiye yawu a hankali dan har yanzu idonsa na cikin nata tace, “Thanks”.
Wani tattausan murmushi yay mata yana wani lumsha idanu da janye yatsun hanunsa dake murza nata ya maida hankali ga cos da yay ƙasa da kansa tamkar hankalinsa nakan takardar da yake dubawa. Sai dai kuma a munafunce yake satar kallon wannan soyayya ta Mr president da first lady. Sai da ya ga Ramadhan zai juyi ne yay saurin maida dukkan hankalinsa ga takardun sosai.
Oho daga Ramadhan har Raudha basu san yanayi ba. Dan tuni Raudha ta zaro hotunan cikin envelope ɗin tana dubawa. Ƴammata ne cikin shigar uniform na aiki, wasu kuma suit na mata. Dukansu bazasufi shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai talatin ba. Sai da ta duba duk hotunan guda biyar sannan ta zaɓa na mutum biyu dake sanye da baby hijjab alamar musulmai ne, maybe ma yarenta ne duka.
Kamar mai jin tsoron maganar yanzun ma tace, “Waɗan nan sunyi”.
Kai kawai Ramadhan ya jinjina mata batare da ya ɗago ba. Dan rabin hankalinsa na ga abinda yake dubawa a file ɗin hanunsa. Kusan mintuna uku sannan ya ɗan duba cos da alamar ɓacin rai a fuskarsa… “Jafar! Abinda ke rubuce anan kuwa gaskiya ne? Ko idona ne?”.
“Tabbas gaskiya ne ranka ya daɗe. Dan duka mutane goma sha ukun nan daka gani akwai kwangilolin ayyuka a kansu, wasun su sun fara basu ƙarasa ba, wasuma ko niyyar farawar basuyi ba. Kuma munada tabbacin kuɗaɗen aikin sun fita a bitalmani harda saka hanun shugaban ƙasa mai sauka. Waɗan nan sune evidences na fitar kuɗaɗen duka”.
Yay maganar da miƙa masa wani file ɗin. Sosai Raudha ta ɗago tana kallonsu yanzun kam, dan zancen nasu haka kawai ya ɗauka hankalinta. Ta ɗan kafama Ramadhan daya dafe kansa bayan duba takardun idanunta.
“Cos!!”.
Ya faɗa a kausashe.
“Yes your excellency!”.
“Ina buƙatar a tura ma dukansu takardar gayyata, ku zauna da su kai da minister Abubakar Gandu Ku tattauna dasu domin bibiyar gaskiyar lamarin. Bayan kun tabbatar da gaskiyarsu ku basu kwanaki biyu kacal su dawo da kuɗaɗen kafin mu miƙa sunansu ga hukuma”.
“Okay sir!”.
Ɗan murmushi Raudha ta saki daya ƙawata fuskarta, cike da ƙarfin halin danne ciwon marar dake tsinkulinta, sai hakan yay dai-dai da ɗagowar Ramadhan suka haɗa idanu. Harara ya sakar mata yana sake tsuke fuska. Sai kawai murmushin ya sake suɓuce mata batare data shirya hakan ba. Idanu ya ɗan ƙanƙance ɓacin ransa na sake bayyana a fuskarsa, tai saurin girgiza masa kanta da kama kunuwanta dake cikin hijjab alamar “Am sorry”.
Baya ya ɗanyi da jikinsa yana lumshe idanu da furzar da huci. Hakan da yay ya saka Raudha cikin dauriya tace, “Ranka ya daɗe idan babu damuwa nace wani abu dan ALLAH?”.
Babu shiri ya buɗe idanunsa dan baiyi zaton jin hakan daga gareta ba. Ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “Dan ALLAH abokina”
Tai maganar cike da marairaicewa. Sai yanayin yay kama da wadda shaƙuwa ke tsakaninsu sosai take masa shagwaɓa. Harga ALLAH sai da zuciyar Ramadhan ta motsa. Domin shima dai mutum ne tamkar kowa, sannan zuciya gare a ƙirji ba kuma dutse bane….
Kafin ya gama dawowa hayyacinsa ta ce, “Ranka ya daɗe maimakon a damu da zancen su dawo da kuɗin kuma su sake faɗawa hanun ɓata gari kafin su koma a bital mali, mizai hana a zaman da zakuyi dasu, mizai hana ku tilastasu ƙarasa aikin da suka fara, waɗanda basu faraba su fara kawai. Idan da buƙatar ƙarin wani abu da zai inganta aikin fiye da farko ko zai kammalashi sai ku daɗa musu. Koba komai hakan zai sa talakawa su tabbatar aiki kukazo yi da gaske……”
Yanda ya kafeta da idanu ya sata haɗiyar yawu da ƙyar. Cikin ɗan shakku da ganin zaƙewarta ya sata faɗin, “Ban faɗi haka dan ganin gazawar maganarku ba. Sai dan kawai a nawa hasashen shari’a da su tamkar zaman ɓata wani yanki na lokutankune masu muhimmanci ga alƙawran da akaima talakawa. Dan fallasasu zai ɗauke hankulanku ne kacokan ya maida can, aikin da kukai burin yi lokacinsa yayta tafiya. Bai kuma zama lallai su da suka basu kwangilar ba su yarda su tozarta kai tsaye tunda maybe akwai ƴan uwansu ko abokansu a ciki da makamantan hakan. Ƙila kuma dalilin hakan da zaku musu su shiryu su koma mutanen kirki wajen gyara halayyarsu har na ƙasa dasu masu tasowa suyi koyi idan kun ɗorasu akan irin wannnan matsayin. Idan na shiga hurmin daba nawa ba a gafarceni ranka ya daɗe”.
“Raf! Raf! Raf!”. Cos ya fara sakin tafi bakinsa a washe da murmushi.
“Oh my god uwa garemu. Ranki ya daɗe wannan shawara ce mai daraja data warware kowanne irin tarnaƙi cikin sauƙi ai. ALLAH ya kara girma da nisan kwana masu albarka.”
A ɗarare Raudha tai murmushin yaƙe. Dan bata da tabbacin mai gayya mai aikin shi ya amshi zancen kamar yanda taga cos ya nuna jin daɗinsa kai tsaye ba.
Cos da ya sha jinin jikinsa ga yanayin shugaban ƙasar shima yay saurin dakatawa yana faɗin, “Ranka ya daɗe m….”
Hannu shugaban ƙasa Ramadhan ya ɗaga masa yana buɗe idanunsa da furzar da iska mai nauyi………..✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button