Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 37

★★★

Ramadhan da bai san anai ba tuni Dr Hauwa ta bama Raudha duk wani taimako da ya dace, ta kuma tabbatar masa da Raudha zata samu barci mai ƙarfi da zai taimaka mata wajen samun nutsuwa. Amma kar suyi wasa bayan ta samu lafiya ta sameta a asibiti. Da ga haka sukai masa sallama zasu wuce bayan Bilkisu taje ɗakin Raudha ɗin ta ɗakko mata part da pant data fahimci tana bukata. Sai dai a ranta tana jin daɗi da mamakin yaushe Raudha suka ɗinke da Yayan nasu haka har da kwana a ɗakinsa. Koma dai miye tayi farin ciki ita kam dan tana ƙaunar wannan haɗin har cikin ranta.
Sosai Raudha da barci ke ɗibar idonta taji daɗin abinda Bilkisu ta ɗakko mata. Tana son tace zata koma ɗakinta ta kasa ɗaga baki saboda barci. Dole ta haƙura ta lumshe idanun bayan ta sake cusa pant da part ɗin cikin hijjab ɗin jikinta wai kar Ramadhan ya gani.
Ya jima zaune bai motsa ba a inda suka barshi har Raudha tai nisa a barci. Abubuwane birjik a cikin kansa da UBANGIJI kaɗai yake fatan yay masa tallafi a kansu. A hankali ya miƙe ya nufi gadon saitin inda Raudha ke kwance a baki-baki, dan a nufinta ta ɗan kwanta ne idan su Bilkisu sun tafi itama ta koma ɗakinta.
Tsaye yay a kanta ya zuba mata idanu kawai tamkar mai son gano matsalar tata a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. A hankali ya turo iskar ƙirjinsa zuwa baki ya fesar dai-dai lokacin da yake kai hannu ya ɗage hijjab ɗin jikinta da nufin cire mata gudun karya cutar da ita………✍

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button