BAKAR INUWA 41

ENGLAND (LONDON)
A kwanaki biyun da suka rage tawagar shugaban ƙasa Ramadhan sun fahimci bashi da walwala. Kai bama walwala ba gaba ɗaya a cikin yanayin fushi yake. Dan komai yana yinsa ne cikin faɗa-faɗa. Ko a wajen meeting da sukai na ƙarshe kalaman da yay amfani da su da suka nema tada ƙura a ƙasar NAYA ya sake tabbatar da zuciyarsa a wuya take.
Dan daga Bappi har Anne da Pa kai tsaye suka fahimci haka lokacin da suke kallon labaran. Sai dai mai magana da yawunsa ya sake faɗaɗa kalaman yanda zasu cire ƙulli a zukatan ƴan ƙasar musamman waɗan da suka ƙullacesa a rai. Wasu sun gamsu wasu ko sun riga sun hau da takaici matuƙa…
Oho shi baima san sunayi ba. Dan in yana a irin wannan yanayin bawai yana gane yaren kowa bane ba. Shi kansa baya gane kansa ballantana wani. Hatta da su Anne dan karsu kirasa ya kashe wayarsa ne. Sai dai hakan bai hana Bappi bin ta ɗayan layinsa ba shi ya kirashi. kamar bazai ɗaga ba ya dai daure ya ɗaga. Da ƙyar yake magana hakan ya sake tabbatar ma da Bappi akwai matsala…
Koda ya matsa masa da tabbaya bai ɓoye ba ya sanar masa abinda ya ɓata masa ran. Dan tun yana ƙaraminsa Bappi da Anne sune abokansa, aminansa, iyayensa, kakaninsa. Da wahala yayi wani abu batare da shawararsu ba ko bijirema umarninsu idan sun masa.
Dariya sosai ta kama Bappi amma sai ya gimtse ta da ƙyar sai murmushi yake. tsaf ya fahimci kishi mai tsanani ke ɗawainiya da Ramadhan. Ya daɗe da sanin jikansa nada kishi mai zafi irin nasa. Dan shima haka yake da tsananin kishi ga matarsa Anne. Kafin suyi aure yasha fasa bakin samari idan ya gansu tare da Anne koda ƴan family nasu ne. Kishinsa na ɗaya da ga cikin abinda yasa iyayensu aurar da su batare da sun jira sun kammala karatunsu ba.
“To ALLAH ya huci zuciyar maza”.
Bappi ya faɗa murmushi faɗaɗe a saman fuskarsa idonsa akan matarsa data zuba masa ido da son jin mike faruwa da jikan nata.
Bappi ya cigaba da faɗin, “Bilkisu itace mai laifin bata ƙyauta ba sam. Amma ayi haƙuri a kori gaba. Na tabbata da Aminatu tasan zata ɗaura zata hanata tunda tasan baka so…”
“Amma Bappi wando da riga fa ta saka itama ta fita waje matsayinta na matar aure. Da bata sa kayanba ita Bilkisun zata ɗauketa hoton ne?…”
“Uhm itama tayi laifi anan, amma bilkisun ai ta girmeta ya kamata ta fita hankali tunda tare suka fita. Sai dai ina roƙa mata afuwa a tari gaba, idan ta ƙara ni kaina zance a hukuntata kaji babban mutum. Ayi haƙuri zuciyar ta huce haka nan dan ALLAH, dan naga muma ƴan ƙasa fushin ya shafemu har ana mana dogon gargaɗin da gashinan ya tashin hankalinmu baki ɗaya”.
Murmushi Ramadhan ya saki mai sauti yana kai hannu a goshinsa yana murzawa. “ALLAH Bappi bamma san na faɗa ba yarinyar nan ce duk ta harmutsani.”.
Dariya sosai Bappi ya ƙyalƙyale da ita da faɗin, “Ja’iri da alama dai kazo hannufa. Ni nasan Aminatu na ba kalar matan da za’a kira na cushe bane ai”.
Ramadhan ya ƙyalƙyale da dariya harda kwanciya a kujera. “Oh sweet bappi karda ku cika baki, dan nidai cusamin akai”.
“Nima naga alamar hakan kuwa yau”. Bappi ya faɗa yana dariya shima.
______________
Wannan waya itace sanadin hucewar Ramadhan tun a london. Yayinda ita Raudha kenan NAYA cikin damuwa da fargabar karya hanata makarantar daya kwaɗaita mata tunda ya mata gargaɗi tun farko. Gashi gobe idan ALLAH ya kaimu zata fara zuwa monday kenan. Shi kuma yau Lahadi zai dawo kamar yanda ya faɗa kuma aka sanar a labarai. Bilkisu har yanzu tana gidan duk da sanin halinsa ta gwammaci zama harya dawo ta wanke laifin Raudha dan tasan itace da laifi ba Raudha ba. Bata son zama silar haɗa rikicin ma’auratan duk da bata taɓa zama ƙarƙashin inuwar aure ba. Ballema wannan auren nasu na ɗora ɗafini da take ganin matsala kala-kala baibaye da shi, dan duk ƙulle-ƙullen su Maah ta sani bata nunawane kawai tana musu fatan shiriya da ganewa.
Bilkisun ce ta ƙarfafa mata gwiwa suka shirya masa abinci mai ƙyau, ta kumaje ɗakinsa ta gyaro kamar yanda bily ta nusar da ita karta sake yarda wani yay mata gyaran ɗakin miji da ranta da lafiyarta. Sai kuma tai ƙoƙarin kwashe drinks ɗin da aka zuba masa a fridge duk da bata da tabbacin wannan ɗin akwai guba sakamakon har yanzu wancan kukun bai koma bakin aiki ba ana kan binciken ta yanda aka saka mata ƙwayar zubda ciki tasha kamar yanda taji a bakin Mama Ladi.
Da taimakon mama Ladi suke wannan ƙoƙarin na canja drinks ɗin a duk sanda aka zuba shi, sai dai ita kanta mama ladi batasan dalilin Raudha nayin hakan ba. Ko data sanarma Anne zancen catai “Bana tunanin yarinyar nan zata cutar da shi Ladi, anya kuwa babu wani abu a ƙasa data sani? Dan akwai wani saƙo da ya zo mana ana gobe ɗaurin aurensu kuma bamu san waye ya aiko ba, da kuma muka bincika mun samo abinda aka nusar damu akansa. Shiyyasa gaba ɗaya gidan gwamnatin nan a tsorace nake zamansu a cikinsa. Amma karki damu, insha ALLAHU munama Ameenatu ƙyaƙyƙyawan zato bazata aikata wani abu na cutar da Ramadhan ba”. A lokacin kai mama ladi ta jinjina tana murmushi kamar tana a gabana, cikin jin sake ƙaunar tsohuwar tace, “Insha ALLAHU Anne” Daga haka ta yanke wayar, bakuma ta sake maganar driks da Raudha ke ƙoƙarin canjawa ba a duk sanda aka zuba a frighe ɗin sama dana bedroom ɗin Ramadhan.
Dan haka yanzu ma tare sukayi a sirrance tamkar koyaushe. Daga haka tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa da tai mata ƙyau sosai. Light make up bilkisu ta mata badan taso ba. Sai zuga ƙyawun datai takeyi da ƙarfafa mata gwiwar ya kamata ta koya kwalliya kuma ta dingayi dan tana ƙara mata ƙyau. Ita dai murmushi tayi kawai amma batace komai ba, dan kunyar Bilkisu takeji sosai, bama ita ba ko su Fatisa bilkisu ta girma, amma ita Bilkisun ba ruwanta ta saki jiki da ita sosai tamkar ƙawarta ma. A ranta tana faɗin, (wa zanma kwalliyar? Wannan birkitaccen yayan naku da bai iya komai ba sai jin kai da azabar masifar tsiya yaushe ma na ishesa abin kallo? Yau ka gansa normal gobe bajimin zaki kamar ɗan aljanu).
Har ɗauri sai da ta mata, ta kuma tilastata suka fito falo suka zauna dan su Lubnah tun randa ya suka fita basu dawo ba wai bikin ƙawar Aynah akeyi suna can gidan Adda Asmah.
Ita dai zaune take kawai amma badan tana fahimtar abinda suke kallo a television ɗin ba har aka nuna saukar jirgin tawagar shugaban ƙasa Ramadhan da shi kansa. Shine ya fara fitowa lokacin da aka buɗe jirgin. Kamar yanda ya tafi cikin suit haka ya dawo cikinsu sai dai na yanzu sky blue ne, rigar ciki light yellow. Bai sa necktie ba dan maɓallan rigar cikin ma guda uku a buɗe suke.
Fuskarsa ɗauke take da ɗan murmushi lokacin da yake gaisawa da masu tarbar tasu sai dai bamai tsawwalawa ba. A hankali Raudha ta sauke numfashi tana lumshe ido ganin fuskarsa da ɗan sakewa saɓanin yanda tai zaton gani, ita kanta ta yarda Shugaban Ramadhan ƙyaƙyƙyawa ne kuma ya iya ado, ba duk mace bace zata kallesa ta iya ɗauke kanta batare da taji wani abuba, ita kanta yana mata kwarjini da cika ido, badan ya ɗara sauran maza ko mutane ba. sai dai ita bata taɓa jin son sa ba.
Sake buɗe idanun tai tana kallon television ɗin, sai dai ranta cike yake da fargaba lokacin da ake nuna ya shiga mota ɗan jaridar na sanar da tahowarsa gida kai tsaye domin hutawa……….✍