BAKAR INUWA 43

Chapter 43
43
………Ta najin shigowar motocin da suka ɗakkosa gidan ta miƙe a ɗan zabure wai zatai fitsari. Bilkisu da tuni ta gama fahimtar a tsorace take tai saurin riƙota tana danne dariyarta.
“Hi madam! sai fa Brother yaga kwalliyar nan ya shaƙi daddaɗan ƙamshin nan, dan haka babu inda zaki gudu”.
Fuska sosai Raudha ta marairaice kamar zatai kuka. “Aunty Please, kuma fa da gaske nak…….”
Sauran maganar ta maƙale sakamakon haɗa ido da sukai da abinda take tsoron gamuwar. Cak numfashinta ya ɗauke daga maƙoshinta har gangar jiki, sai da taji tana neman shiɗewa ne ta haɗiyi wani bushashshen yawu da ƙyar fuskarta na sake narkewa alamar dai da gaske a tsorace take, dan har yanzu ruwan masifar daya zuba mata shekaranjiya tana zaune daram a brain ɗinta, kowace daƙiƙa cikin bitarsu take a zuciya. Ga mai kallonta kuma a yanda tai ɗin babu maraba da shagwaɓa….
A hankali Bilkisu dake murmushi itama idonta akan Yayan nasu ta saki hanunta tana masa sannu da zuwa kafin ta ɗan zunguri Raudha ɗin alamar ta tashi ta tarbesa…
Ko gaisuwar bilkisun ma bai amsa ba, sai wata ƴar harara daya zuba mata na tabbacin har yanzu a ƙule yake da su yayi da idanunsa da sukai ɗan ja. Hakama saman hancinsa jajur yake da alamar murace ta kamashi.. wucewarsa yay zuwa bedroom ɗinsa jikinsa duk yay masa nauyi, saboda murar daya tashi da ita a safiyar yau. Gashi wahala mura ke bashi inhar ta damƙesa.
Nannauyan numfashi suka saki kusan a tare, sai kuma suka kalli juna suka ƙyalƙyale da dariya. Raudha da sosai ta saki jiki da Bilkisu a kwanakin nan tace, “Kai aunty B wlhy kema a tsorace kike fa”.
Dariya sosai Bilkisu tayi, cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Wlhy bazaki gane bane, Brother da kike gani ɗan daru ne bana wasa ba. Idan ya birkice babu mai iya tarosa sai Anne ko Bappi”.
Sake tsargawa cikin Raudha yayi har Bilkisu najin ƙara ƙulululu!!!, kasa daurewa tai sai da ta ƙyalƙyale da dariya. Yayinda Raudha kuma ta ɗan dafe cikin tana yamutsa fuska.
“Kinga tashi ki bisa da ruwa, naga ma kamar mai mura fa. Kuma mura na wajigashi idan ta kamashi”.
“Aunty B wlhy tsoro nakeji. Kinga kuwa harar daya bamu ko amsa sanun da kikai masa baiyiba fa”.
“Karki damu zai huce. Kedai kawai abinda zakiyi ko yayi magana yanzu karkice komai sai ban haƙuri. Ko bayani kar kice zaki masa za’a samu matsala dan ya tsani maimaita magana”.
Cikin tausayin kai Raudha ta jinjina mata kai tare da miƙewa. Dan koda bata son sa bazata taɓa son ace ta gagara sauke hakkin aure da ke a kanta ba. Idan ko ta tuno gargaɗin mahaifinta bazataso aurenta ya mutu ba har abada koda batajin daɗi a cikinsa. Ruwa da cup ta haɗa saman wani ƙyaƙyƙyawan golden tray mai yarfin fari kaɗan da fresh milk duk da tasan duk akwaisu a ɗakinsa. Ta gyara lulluɓin mayafinta har saman kai kamar wacce zata fita duk da ba wani babba bane ba. Yanda ta fahimcesa ma idan tace zata fita waje da mayafin ai zai iya halaka ta.
“Kimin addu’ar fitowa lafiya dan ALLAH aunty B”.
Ta faɗa cikin marairaicewa lokacin da tazo saitin Bilkisun. Cikin danne dariya Bilkisu tace, “Fatan alkairi aunty Babba. Insha ALLAH babu ma abinda zai faru sai alkairi da tsarabar kiss”.
Kunyar maganar ƙarshe ta saka Raudha saurin yin gaba tana ɗan tura baki. Bilkisu ta ƙyalƙyale da dariya har ranta tana sake jin ƙaunar yarinyar.
Tamkar wadda tazo sata a ɗofane tai knocking ƙofar batare da tunanin zaima jita ba. Jin shiru ya sata ƙara ɗan bugawa nan ma tsitt. Hannu ta kai zata sake bugawa a bazata aka buɗe ƙofar hanunta ya sauka saman kirjinsa da babu riga. Hasalima daga shi sai towel yana ta raɓar ruwa alamar wanka ya fito.
Da ƙarfi Raudha ta rumtse idanunta da ƙoƙarin janye hanunta daya haɗu da laushin fatarsa da laimar ruwan ɗumin dayay wankan da shi. “I…am sorry. ALLAH ban san ka taho ba”.
Ta faɗa kamar zatai kuka idanunta har lokacin a rumtse suke ji take kamar ta saki gudawa. Jin shiru ya sata ɗan buɗe ido ɗaya kaɗan. Wayam baya a wajen, gaba ɗaya ta buɗe tana haɗiye yawun da ya kasa wuce mata a maƙoshi da ɗan dafe ƙirji ta sauke numfashi. sai kuma tai saurin ɗago hanun ta kalla tare da kai masa duka da ɗayan hanunta tana cije baki kamar maiyi da wani (????ba man kai … Lol)
“Malama ki rufen ƙofa inba shigowa zakiyi ba”.
Ta tsinkayi muryarsa da ke nuna tabbacin mura yake. Dan baima kai ƙarshen maganar ba ya saki atishawa a cikin tissue ɗin dayay saurin ɗorawa kan bankinsa.
(Masifaffe). Ta ayyana a ranta tana ɗaukar tray ɗin data ajiye a drawer glass da akai ado da shi gab da ƙofan ɗakin nasa. Koda wasa batai gigin kallonsa ba, dan shi ya fuske abinsa duk da kuwa daga shi sai towel. A ɗan table ɗin gaban sofa’s ɗin ɗakin ta ɗora, kanta a ƙasa tace, “Ina yini? an dawo lafiya?”.
Sarai ya jita, amma yay banza yana cigaba da shafa mansa lokaci-lokaci yana atishawa, yabi ya tara uban tissue a ƙasa da yake tarewa da shi. Raudha na ƙoƙarin barin ɗakin cikin takaicinsa dan ta tsani wulaƙanci duk da bata da yawan hayaniya ya katse hanzarinta da faɗin, “Bani dustbin”.
(Yadai fi). Ta faɗa a ranta tunawa da wahalar da tasha wajen gyaran ɗakin nasa lungu da saƙo. Shi kansa lokacin daya shigo yaga ɗakin sai da yaji a ransa ba gyaran Tahir bane. Yanda bai tanka ba data gaishesa itama hauka ta manna masa taki tankawar ta fice. Kallo ya bita da shi cikin jin haushin bata amsa maganar da yay mata ba (ƙarfin hali???? lallai wanzami baya son jarfa).
Guntun tsaki yaja da cirar tissue ɗin ya sake atishawa a ciki. Idanunsa sun kara kaɗawa da ja har suna tara ruwa a ciki. Jijiyoyin goshinsa kam duk a miƙe suke alamar ciwon kai.
Yana ƙoƙarin saka shirt mai ɗan kauri ta shigo, bata yarda ta kallesa ba, cikin ɗan yamutsa fuska da bata san tanai ba tasa yatsu biyu tana a yanayin ƙyanƙyami ta dinga ɗauke tissues ɗin daya tara a ƙasa tana jefawa a dustbin ɗin. Cak ya dakata da abinda yake yana kallonta, a ransa ya ce, (Da gaske yarinyar nan ta bala’in rainani, wai ni take ƙyanƙyami?) a fili kam sai ya taɓe baki ya ɗauke kansa. Ƙarasa shirinsa yay ya ɗauka misk zai ɗan shafa dan baya buƙatar saka wani spray turare saboda mura, dai-dai Raudha ta gama kwashe tissues ɗin sai wani kwaɓe fuska take hanunta a buɗe tabbacin ƙyanƙyami. Dariya yaji tazo masa tsabar muguntar daya shirya mata. Amma sai ya gimtse kayarsa bama zaka taɓa fahimtar hakan a fuskarsa ba. Raudha na ƙoƙarin gyara mayafinta kawai taji saukar atishawa a fuskarta har biyu a jere.
“Innalillahi…..” ta faɗa cikin subutar baki tana sakin dustbin ɗin ƙasa. Misk ɗin daya gama shafawa ya ajiye saman mirror yabar wajen tamkar baima san abinda yayi ba. Yaje saman sofa ya zauna ƙafa daya kan ɗaya. Cikin bada umarni da isar daya gada ga Gimbiya Su’adah ya ɗauka jaridar dake ajiye saman stool ɗin gefen kujerar yana faɗin, “Sai kiyi ƙyanƙyamin da hujja yanzu ai ko? Ina bukatar shayi kuma”.