BAKAR INUWA 43

Wani irin yamutse fuska Raudha tai, kai kace amai ne zai kufce mata. Sai kuma ta fashe da kuka ta ɗauki dustbin ɗin ta fice.
Da kallo ya bita ta saman jaridar, sai kuma ya saki guntun murmushi da taɓe baki lokaci ɗaya yana ɗage kafaɗa irin ko’a kwalar rigarsa ɗin nan.
Cikin sa’a Raudha ta samu bilkisu bata falon, kitchen ɗin dake falon ta shiga, kuka tayi sosai dan har cikin rai taji zafin abinda yay mata, yayinda wani gefe na zuciyarta ke ƙoƙarin nusar da ita abinda yayi ɗin ba komai bane, sai dai taƙi saurarensa. Sai da ta fidda duk wani takaicinta sannan ta wanke fuskar tas har kwalliyar tana faɗin “Anma fasa kwalliyar ALLAH bazaka sake gani ba”. Shayin da yace ta haɗa masa ta haɗa cikin flask mai ƙyau bayan taje ƙasa ta ɗibo kayan data san ana dafa masa shayi da su da yawa.
Maimakon a ɗaki data barsa sai ta iskesa a falo zaune yanzun. Bilkisu na daga zaune ƙasan carpet itama kusa da ƙafafunsa da alama haƙuri take bashi. Dan yanda tai kalar tausayi ya isa tabbatar da haka. Shiko yayi wani kicin-kicin da fuska har yanayin nasa yasa Raudha sake shiga hankalinta. Bayan ta ajiye a gabansa ta zuba shayin tare da saka masa sugar ɗinsu na masu diabetis da yake amfani da shi. Komai baice ba ya ɗauka abinsa ya fara sha.
Kanta a ƙasa tana ɗan wasa da yatsun hanunta tace, “A kawo abincin nan?”.
Cikin mamaki da al’ajab ɗinsa taga ya wani zuba mata idanunsa da mura ta gama firgatawa. Dan harsun kumburo fatarsu tai jaa ga ƙyallin ruwan a ciki, tsaf ya fahimci kuka tayi, sai kuma ya ɗanji babu daɗi. Amma a fuskarsa bazaka taɓa fahimtar hakanba. Dan wani yamutse fuskar yayi ma ya ɗauke kansa bayan ya zuba mata nunanniyar harara.
“Zan sha wannan, idan da buƙatar hakan daga baya na ci”. Ya faɗa bayan yaja wasu sakanni.
Baki ta taɓe zata bar wajen Bilkisu ta ƙyafta mata ido alamar karta tafi. Ta marairaice fuska kalar tausayi da alamar roƙo wa Bilkisun. Da ido Bilkisun tai mata nuni da Ramadhan da ya maida hankalinsa ga jarida… Sai kuma ta ɗauke kanta da faɗin, “Yaya dan ALLAH fa nace, i promise hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma kuskure ne wlhy kuma nice nayi banda Aunty Raudha dan batama san na ɗaura ba”.
Shiru kamar bazai tanka ba sai kuma ya ajiye jaridar yana furzar da huci kaɗan. A takaice ya ce, “Tashi kije”.
Ta san ya haƙura kenan, dan haka cikin jin matuƙar daɗi ta miƙe fuskarta washe da murmushi tana faɗin, “Thanks you Yaya. ALLAH yasa aunty Raudha ta haifa mana ƴan biyu”.
Hannu ya ɗaga kamar zai kai mata ranƙwashi ta kwasa da gudu tana dariya. Shima dai murmushi ne ya subuce masa a bazata. Yana matuƙar son Bilkisu a duk cikin ƙanensa. dan tanada hankali da nutsuwa. Gata da addini, wani lokacin akance halinsu na kamanceceniya da juna. Hakama a fuska suna matuƙar kama. Har lokacin da ɗan murmushi a fuskar tasa ya maida dubansa ga Raudha da mamakin dama yana wasa haka ya narkar da ita. Haɗa idon da sukai ya sata janye nata tai gefe da shi tana tura baki, dan har yanzu a fushi take. Sai kuma tai saurin yunƙurin barin wajen itama……
“Ina su Muneera?”.
Tambayar tasa ta sakata tsayawa cak, sai kuma ta juyo kanta a ƙasa. “Inaga suna can gida, Yau kwanansu biyu”.
“Kinaga? Bamaki da tabbas kenan?”.
Yanda yay maganar a dake ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. kasancewar idanunsa a kanta suke saita janye. Duk da zafi da zuciyarta ke mata sai ta danne. Banda ma ya raina mata hankali su Lubnah dake manyanta ne zai nuna kamar laifintane barinsu fita. A fili kam cikin sanyin murya da ɗan fushi-fushi tace, “Nasan can ɗinne kawai zasu je. Kuma ni da zasu wuce basuyi sallama da ni ba ai miye nawa”.
Yanda taɗan tunzura baki ya fahimci haushi taji. Batare da yace mata komai ba ya ɗauke kansa kawai gareta ya maida ga jaridarsa. Itama ganin haka ya sata barin wajen tai wucewarta bedroom.
BAYAN SALLAR ISHA’I tana zaune a ɗaki ita kaɗai dan bilkisu na ɗakin da su Lubnah suke tana waya da saurayinta ne. Yunwa takeji sosai shiyyasa tana idar da salla taje falo ta ɗibo abinci….
A hankali ya turo ƙofar waya manne a kunensa, kan agogon ɗakin ya fara sauke idanunsa kafin ya maida kan Raudha da mamakin shigowar tasa ya sakata shagala a kallonsa.
Takawa ya cigaba dayi inda take a hankali, tsabar yanda ta tafi wani tunani daban yasa harya iso gabanta bata sani ba. Firgigit ta dawo hayyacinta jin an hure mata idanu. Yanda ya ɗan ranƙwafo fuskarsa gab da tata har yana busa mata numfashinsa ya sata ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya saka hannunsa jikin kujerar ya tokare. Koda ta matsar da kan nata sai ya sauka akan hanunsa. Saurin ɗagawa tai hakan kuma sai ya ƙara basu kusancin da take gudu. A haka ya cigaba da wayarsa cikin harshen turanci idanunsa cikin nata, yayinda yatsansa ke shafa girarta.
Fuska Raudha ta ɓata kamar ta fasa ihu da wannan dabaibayi nasa data gagara fassarawa, acan kuwa zuciyarta na liguden daka, sai dai duk yanda taso ɓoye firgicinta ya riga ya gama karantarta, dan duk ta daburce. Hatta cokalin da take shan farfesun gabanta ya suɓuce a hanunta ya faɗi saman table ɗin. Duk yanda ya fahimci takurata yay yaƙi janye jikinsa. Sai ma cigaba da wayarsa yay hankali kwance numfashinsa na sauka saman fuskarta itama yanajin nata a wuyansa, ta rasa yanda zata fassara lamarin nasa.
“Ina yini”.
Ta faɗa kamar zatai kuka dai-dai yana sauke wayar a kunensa alamar ya kammala wayar, dan wannan kusanci nasu ya matuƙar sakata cakwalkwalin ruɗani. Kaɗan ya rage dariya ta suɓuce masa amma ya danne. Janye jikinsa yay da ga gareta ya kai zaune a kujerar gefenta cikin basar da gaisuwar tata.
Da ƙyar ta iya sakin numfashin data riƙe a ƙirji. Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki itakam dan al’ajabinsa. Bata gama dawowa hayyacintaba ta tsinkayi muryarsa still da wani furicin.
“Har yanzu kina ƙyanƙyamin nawa?”.
Babu shiri ta kallesa ido a zare. cikin marairaicewa ta ce, “Ni yaushe nace ina ƙyanƙyaminka?”.
Yanda tai maganar ya sashi tsura mata idanunsa da mura ta cika. Sai kuma ya janye yana sake tamke fuska. Kamar yanda itama ta ɗaure tata tamau.
Fuskarsa ya ɗan sake matsarwa gab da tata, still yanzu ma suna shaƙar numfashin juna. “Idan ma baki faɗa da baki ba ai sirrin zuciyarki ya fito, shiyyasa na baki numfashina naga idan kin ɗauka ke kuma yaya zakiyi da kanki?”.
“Ya ALLAHU!”. Ta faɗa cikin subutar baki da waro idanunta waje gaba ɗaya kansa. Yatsun hanunsa biyu ya ɗan kaɗa mata, sai kuma ya duba bowl ɗin gabanta mai ɗauke da farfesun kayan cikin da Bilkisu tai musu. Yunwa ce ta addabeta dan tun safe rabonta da abinci, fargabar dawowarsa da tuna azabar masifar da yay mata a waya ya hanata sake cin wani abu. Dama da safen Bilkisu ce ta takura mata……..