BAKAR INUWA 43

“Ammafa wannan cin amana ne, aci nama ina gidan nan babu ni, wannan ƙawancen dake tsakaninmu kuwa na tsoron ALLAH ne Ustazah?”.
A yanda yay maganar ya sata kasa daurewa sai da ta kallesa. Ganin idonsa a kanta ya sata ɗauke nata da sauri tana tura baki. (Na shiga tara ni Raudha, ALLAH yasa dai da gaske ya huce kenan) ta faɗa a ranta, a fili kuwa sai ta ja kwanon namanta gabanta da faɗin, “Naji a kwance, idan na gama ci sai mu shirya”.
“Ko? to andai ji kunya Ustazai da rowan nama, idan kina son kanki da arziki muje ki bani nawa naci kokuma na ɗiba rabona a can”
Yay maganar cikin ɗage mata gira ɗaya yana miƙewa. Batare da ya jira cewarta ba ya fice abinsa. (Uhm, su Ramadhana an fara zama ƴan is…????????????)
Filo Raudha ta ɗauka ta balla masa cizo tana matsesa a ƙirjinta. Sai kuma ta tillashi ƙasa tare da dafe kai tana faɗin, “Ni Raudha yama haukatar dani”.
Babu yanda ta iya dole ta miƙe ta ɗau mayafinta na ɗazun dan kayanne a jikinta har yanzun ma ta fita. Tsaye ta samesa a falo hankalinsa gaba ɗaya akan television da ake nuna labarai. Koke-koke da taji anayi a tvn ya sata saurin kallo gabanta na faɗuwa. Jikinta ya kama rawa, domin kuwa rahotone na wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gaman dake jihar Kuddo faɗa ya ɓarke a tsakanin ƙabilun dake ƙauyen. Gawarwakine zube na yara da manya harma da dabbobi, wasu jina-jina da raunika abin babu daɗin gani. Ga wasu nata kuka durkushe gaban gawarwakin ƴan uwansu da aka kashe ko aka raunata.
Kuka da Raudha ta fashe da shi ne ya maido Ramadhan da ga ɗaukewar numfashi da ya tafi na tashin hankali. Ya kai zaune jib cikin kujera hajijiya na neman ɗibarsa. Ba yau ne aka fara irin wannan rikicin a ƙauyen ba, sai dai bai taɓa gani ba kamar yau, ga shi yau ɗin daya gani kuma yana amsa sunan shugaban kasar NAYA ne da hakkin kowa ya rataya ne a ƙarƙashin mulkinsa….. Yanda jikin nasa ke rawa ya sakashi riƙo Raudha data kai dirƙushe a gabansa tana kuka ya rungume, itama ƙanƙamesa tayi kawai tana sakin wani sabon kukan…..
Wayarsa ya fara laluba da hannu ɗaya a aljihu, yayinda ɗayan ke tallafe da Raudha. Yana cirota kafin ma ya aiwatar da abinda yake shirin yi kira ya shigo masa. Da ƙyar ya iya controling kansa tsabar ruɗani ya ɗaga, da ga can hankali tashe cos ya ce, “Ranka ya daɗe kaga abinda ake nunawa a tashar Q-TV kuwa? Kodai halin ƴan adawa ne kawai….”
“No Jafar, karka kawo wannan, ka bincika yanzu abun ke faruwa ne ko tun ɗazun?”.
“Okay sir ina zuwa”.
Wayar ya jefa saman kujera, ya kai zaune shima har yanzu Raudha na jikinsa tana sharɓar kuka. Ji yake kamar shima ya fashe da kukan, amma ya daure ya ɗago Raudha, cikin dakiya yake faɗin, “Please Ameenatu relax mana. Kukanki sake tadamin hankali yake, bayan daga gareki ya kamata na samu ƙarfin gwiwa”.
Hannu tasa tana sharar hawayen, “Kayi haƙuri”. Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga saman cinyarsa da take zaune ɗare-ɗare gudun kar Bilkisu ta fito, kuma a karankanta ma dai da kunya ai.
Komai baice mata ba, sai wayarsa data fara ring ya kai hannu ya ɗauka ganin cos ne.
“Ranka ya daɗe a yanda suka faɗa su dai yanzu ne. Amma dai yanzu I.G ya tabbatar min tun kusan magrib ne abun ya fara faruwa kamar yanda C.P ɗin jihar Kuddo ya sanar masa. Sai dai ka kwantar da hankalinka ya tabbatar min komai ya dai-daita zuwa yanz…….”
A matuƙar tsawace shugaban ƙasa Ramadhan ya katse cos, “Taya zan kwantar da hankalina Jafar? mutane na cikin irin wannan tashin hankalin!! Ka duba fa kaga mata ne da yara kanana a cikin jini saboda rashin imanii!!! Yanzu da akan familyna ya faru zakace na kwantar da hankalina ne? Na shiga uku ni Ramadhan!……..”
A yanda yay maganar dole ne ya baka tausayi ya kuma tayar maka da hankali, dan abun al’ajabi sai ga hawaye na sakko masa. Wayar yay jifa da ita tare da dafe kansa yana yamutsa gashinsa da duka hannayensa biyu.
Sosai Raudha ta sake rikicewa itama, dan yanda yake birkita sumarsa yana hawaye da ambaton ya shiga ukun itama sai ta sake fashewa da kukan da zuwa gabansa ta durƙushe hannayenta duka biyu akan gwiwoyinsa…………✍