BAKAR INUWA 44

damuwa tattare da shi.
★Tabbas umarnin shugaban ƙasa Ramadhan yayi matuƙar tasiri, dan cikin ƙanƙanin lokaci dukkan abinda ya lissafa aka ninkashi ga jama’ar wannan ƙauye.
Kafin wayewar gari tako ina garin jami’an tsaro ne har cikin dazukan yankin da sauran ƙauyikan, ga helicopters na sojoji sai yawo suke ta sama. Na asibitima
suna samun ƙyaƙyƙyawar kulawa. Waɗan da sukai musabbabin fara haɗa rikicin da CP ya bada umarnin dankosu sai ga gawarwakinsu a cikin waɗanda suka mutu.
(Dama haka fitina take, a mafi yawan lokaci wanda ya takalota shi take fara zubarwa a ƙasa. ALLAH ka zaunar da ƙasashenmu lafiya. ya gafarta mana
kurakuranmu ka wadatamu da tsarkakakkiyar zuciya????).
★★★
Da ga Raudha har Ramadhan idan sunyi barcin kirki a wannan dare sai dai ɓarawo. Ga mura ta mugun addabarsa da zazzaɓi mai zafi ma ya kwana. Yayi waya
da Bappi yayi da Pa duk akan lamarin. Anne ma ta kwantar masa da hankali ta hanyar nasiha sosai da muhimmincin tashi tsaye akan addu’a .
Basu kaɗai ba hatta Bilkisu da damuwar ta kwana. Duk da dai nata tsananin tashin hankalin nada nasaba da halin da taga Yayansu da Raudha a ciki. Adalilin
hakan ma yau a ɗakin Raudha ta kwana. Ita kuma Raudha a ɗakin Ramadhan suka kwana tare.
Da sassafe shugaban ƙasa Ramadhan yabar gidan batare da sanin su Raudha ba, dan ɗakinta ta tafi yin sallar asuba bayan ya fita massalaci shima. Sai da
suka fito sukaci karo da shi a tv ana nunasa a cikin ƙauyen Kauci, abinda zai birgeka har da shi cikin tawagar masu zana’ida duk da karancin lokacin dake
garesa. Ana kammalawa suka baro garin sai dai yabar jama’arsa suna sake zagaya ciki da bai ɗin ƙauyen. Tare suke da gwamnan jihar Kuddo ɗin. Daga ƙauyen
asibiti suka wuce nanma shugaban ƙasa Ramadhan ya duba wanda suka sami raunika. Da ga haka bai ƙara ko minti biyarba a jihar Kuddo suka nufo Bingo dan da
ƙyar yay squeezing time ɗinsa dama. Sai dai abinda yayi ɗin ya kara masa kima da daraja a idanun talakawan ƙasar NAYA. Gaba ɗaya a yinin nan babu abinda
kakeji sai ruwan albarka da ake jera masa tako’ina.
Yayinda a ɓangaren su Alhaji Yaro glass kuma sukai yinin baƙin ciki da ƙunci dan basuyi zaton shugaban ƙasa Ramadhan zaije har ƙauyen ba domin nuna
kulawa. Ba ƙaramin shiri ya wargaza musu ba akan hakan.
A ɓangaren mai gayya mai aiki kam Ramadhan yau ya yini ne cikin damuwa da ɗunbin fargabar wannan mulki mai cike da ƙalubale kala-kala. Tun ba’aje ko
inaba fa kenan, inaga nan gaba kuma da shekaru huɗu da watanni kusan bakwai ke jiransa. Kai anya kuwa zaya iya?.
Da wannan tunane-tunanen ya yini a office ga mura da ciwon kai ga zazzaɓi ga kuma aiki. Yini gudan nan kuma bai ci komai ba ƙishi ma sai da yaji
maƙoshinsa na neman fara yayyankewa sannan yasha ruwa, dan daya tuno jinin daya gano a Kauci sai tsigar jikinsa ta dinga tashi.
Duk da wannan damuwar hakan bai hana wakilan da yasa minister ya naɗa zaman mitin da masu kwangilar nan ba. Sun kuma gudanar da zaman tamkar yanda ya
bada umarni. Yanayin zazzaɓi daya rufesa ya sashi barin office tun 2pm ya shiga gida.
★Koda ya shigo gidan ya iske Raudha bata gidan, shi shaf ma ya manta da batun fara zuwanta school yau. Ɗaki ya shige ya kwanta, duk da abinci ya kamata
ya fara ci ya sha magani hakan bai faruba, sai dai yaji ciwon kansa na ƙara tsanani ya ɗauka man zafi ya shafa ya sake lulluɓe jikinsa gaba ɗaya cikin
duvet.
Duk da burin da taci akan wannan rana ta fara zuwanta makaranta abinda ya faru jiya sai ya rage masa armashi, Bilkisu ce ma da zuwan Ramadhan ƙauyen ya
ɗan ƙarfafa mata gwiwa. Sai dai kuma kafin ta wuce ta ɗauka shawarar zuciyarta, so take tai karatu tankar kowane ɗalibi batare da ansan ita wacece ba. Hakan
kuma bazai kasance ba sai idan bata tare da dogarawanta da aka tanada mata. Gudun karta aikata ba daidaiba ta sanarma Bilkisu shawarar data yanke a yau game
da karatunta. Ɗari bisa ɗari Bilkisu ta yarda da tunanin Raudha, amma itama sai ta kira Anne ta sanar mata. Hakan ya burge Anne ta kuma bama Raudha goyon
baya tare da yabama ƙyaƙyƙyawan tunaninta. Daga ƙarshe Anne tace zata turo mata Adamu driver ya kaita kafin a samu drivern da zai kaita. Idan kuma zata
dinga tafiya da su Basma ne sai su na biyowa ɗaukarta inhar tanada lecture tare da su tunda makarantar tasu ɗaya ce.
Hakan yay mata, takumayi godiya sosai har sai da Anne ta ƙwaɓeta. Babu jimawa kuwa Malam Adamu yazo ɗaukar tata. Kasancewar securitys ɗin sun ganesa
saboda yawan kawo family ɗin shugaban ƙasa da yake gidan yasa bai samu wata matsala ta shigaba. A ɓangaren Raudha shigar mutunci tayi dogon hijjab harda
niƙaf, tafukan hanunta kawai kake iya gani hakan yasa bayan Mama ladi babu wanda yasan da fitarta.
Taji daɗin kasancewar ta a wannan makaranta da ta daɗe da fidda ran ganin kanta a ciki. Babban farin cikinta kuma department ɗinsu ɗaya da Rumaisa da
Basma. Fadila ce kawai take daban dan abinda take karanta yanada banbanci da su Basma. Suturta jikinta ya matuƙar ɓoyeta ga kowa sai su Basma da suka sani.
A nutse komanta ya gudana a wannan yani cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Har a waya ta kira Asabe tai mata addu’ar fatan alkairi. Hakama M. Dauda ta
kirashi sai dai Larai ta ɗaga cikin masifa tace baya nan. Ko jira su gaisa bataiba kuma ta kashe wayar. Murmushi kawai Raudha tayi dan halin matar baban
nasu ba sabon abu bane a wajenta.
Ƙarfe huɗu da wasu mintuna su Basma suka kawota gida, sai dai basu shigoba suka juya. Yunwa takeji sosai dan har wani dishi-dishi take gani saboda ta
fita ko karyawa batai ba. Kuma har taje ta dawo ruwa kawai tasan tasha. Sam batai tunanin samun Ramadhan a gida ba tunda tasan yana office, dan haka kai
tsaye ta wuce ɗakinta. A daddafe ta watsa ruwa ta canja kayanta zuwa doguwar riga mara nauyi, sai hula data saka da Slippers ta fito. Ba komai a dining, ita
kuma tacema mama ladi kar ai komai sai dare tunda itama bata gida hakama bilkisu. Taɗan riƙe ƙugu da hanunta dake riƙe da wayarta, ɗayan kuma tana murza
goshinta dake mata ciwo ta ciki kaɗan-kaɗan tabbacin yunwa da rashin isashen barci na damunta.
Rasa inda zata kama ya sata kiran Mama ladi a waya ta sanar mata ta dawo. Sai kuma ta kai zaune cikin kujera cike da rashin ƙarfin jiki tana shafa ciki
da ɓata fuska. dan da gaske yunwa takeji fa irin ta fita hankalin nan. Minti goma ba’a ƙulla ba sai ga mama ladi da basket na kayan abinci, ai tunkan ta
ƙaraso inda take ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo mama gaskiya kina sona”.
Ƴar dariya mama ladi tayi tana ƙarasowa gareta. Cike da girmamawa ta ce, “Barka da dawowa ranki ya daɗe ai bansan kin shigoba wlhy”.
“Bamma jimaba mama, dan ko mintuna talatin bana zaton nayi, dan na fara wanka ne shiyyasa. Kamar kinsan da yunwa na dawo gidan”.
“Ai nasan za’a rina, tunda naga kun fita baki karyawar kirki ba. shiyyasa na tashi na haɗa miki wannan karki dawo ba’a kammala abincin dare ba”.