BAKAR INUWA 44

“Nagode sosai mama ALLAH ya saka da alkairi”.
Cike da jin daɗi mama ladi ta amsa mata. ta tsiyaya mata kunun tsamiya daketa ƙamshi dan ta fahimci Raudha naso sosai, zata zuba mata sauran abinci ta
dakatar da ita. “Mama bara nasha wannan tukunna dai to”.
Cikin ƴar dariya mama ladi tace, “Yunwar dai bata kai ko’inaba ma kenan to”.
Dariya kawai Raudha tayi itama tana saka sugar. Mama ladi ta miƙe tana faɗin, “Bara na barki kici abinci naje kitchen muga mi za’a girka kar adalin
shugabamu ya dawo da wuri. Amma mi za’a girka masa da kema kanki?”.
A cikin zuciya Raudha tace (shi wannan mina sani zaɓinsa inba nama da fura ba) a fili kam sai tace, ko tuwon alkama za’ai masa ne, sai a haɗa da
farfesun kayan ciki asa yaji da ɗan yawa dan yana mura….. Kodaima mama ku jirani naci abincin zanzo kitchen ɗin kawai”.
“To shikenan a fito lafiya”.
A nutse Raudha ta cigaba da shan kununta hankalinta nakan wayarta tana karatun wani littafin hausa da Bilkisu ta tura mata. Bayi take ba, amma yanda
Bilkisu ke zuga littafin ya sata fara dubawa shekaranjiya. Sai kuma kamar wasa labarin ya tafi da ita ta nutsu a karatunsa. Dan ita bama tasan bayan
marubutan dake buga littafi ba akwai na online sai yanzu. Kodan bata da wayar ne shiyyasa. Kuma ko sanda suke hutawa bata damu da waya ba shiyyasa bata taɓa
maida hankalinta ga nasu Fatisa ba, amma tasha jin suna sauraren littafi a waya ta zata na masu bugawa ne da ake karantawa a gidan redio.
Yunwa ce ta hana barcinsa tasiri shima. Duk da dai babu laifi ya ɗanyi tunda gashi har makara sallar la’asar yayi. Da ƙyar ya tashi zuwa toilet ya ɗan
watsa ruwa duk da zazzaɓi dake jikinsa ga ciwon kai. A kallo guda zaka fahimci murar ta sake masa rugu-rugu dan saman hancinsa ya ƙara jaa sosai abinka da
fari. Hakama idanunsa sun kumburo fiye da jiya fatarsu tai jajur. Ga shi dama baiyi wani barci isashe ba da daddare. Sama-sama ya shafa mai ya saka wando da
riga masu ɗan kauri na kamfanin adidas harda hula a jikin rigar, sai dai bai ɗora hular a kansa ba ya saketa saman bayansa. Slippers ya zura cike da dauriya
ya fito falon hannayensa duka a aljihun wandon, gara ya samu ko tea ya sha kozai samu nutsuwa ta wani ɓangaren. Tun daga nesa idonsa ke kanta, yayinda sam
ita batasan dashi a wajen ba dan gaba ɗaya hankalinta ya tafine akan littafin da take karantawa mai suna SIYASA KO ƘABILANCI? na (marubuciya Bilyn
Andull ƴar ƙasar Nigeria). Labarin ya matuƙar ɗaukar hankalinta saboda kamanceceniyarsa da tsarin da mijinta kamar yake kai a yanzun.
Tafiya yake a hankali kamar baya so, saboda rashin ƙwarin jiki harya iso inda take, ya kai zaune a kujerar 3seater ɗin da take zaune sam bata fargaba.
Sai da ya kai kwance ya ɗaura kansa bisa cinyarta tai saurin ɗagowa a zabure dan tsabar firgitar ganin kan mutum bisa cinyarta a baza .
“Shut up!”.
Ya faɗa da yanayin tsawatarwa ganin zatai ihu sai dai muryar a ɗashe take fita da sanyi-sanyin dushewarta a dalilin mura da damuwa. Hannu Raudha tai saurin
ɗaurawa a bakinta, sai kuma ta lumshe idanunta zuciyarta sai lugude take a ƙirjinta kamar zata faɗo.
“Sai shegen tsoro”.
Ya sake faɗa a hankali yana lumshe idanunsa da harɗe hannayensa a ƙirji ya miƙar da ƙafafunsa har bisa hannun kujerar da ƙyau. Raudha da sanin shi ɗinne
baisa ta dai-daita ɗari bisa ɗari ba ta buɗe idanunta a hankali ta sauke bisa sumar kansa da ko ba’a faɗa ba kasan tana cin kuɗi kodan ƙyallin da takeyi duk
da kasancewarta irin sumar baƙaƙen fata mai tauri da cika.
Cinyarta ta ɗan motsa cikin ɓata fuska, a ganinta adalilin miye wannan taɓara da zaizo ya kwanta mata cinya babu gaira babu dalili. Motsa ƙafafun nata ya
sashi buɗe idanunsa sai suka shige cikin nata da take hararar masa kai. Da sauri ta kauda kanta gefe da gyara yanayin fuskarta tace, “Ina yini”.
Kamar koyaushe yanzun ma bai amsa ba, sai dai ya zare hanunsa guda daga saman ƙirji ya kamo haɓarta ya dawo da fuskarta yanda take. Cikin sake tsuke
fuska ya ce, “Hararata kikeyi?”.
Idanu Raudha ta ɗan zaro. “Ka rufamin asiri, ni yazanyi na hahareka?”.
Kamar zaiyi magana sai kuma ya saki fuskar da maida hannayensa a ƙirji yana faɗin, “Inma kin hararenin ne iyakarki hararar, kuma duk matar dake harar
mijinta dai kinsan aljanna sai dai ta gani dajin ƙamshi a maƙota”………✍