BAKAR INUWA 45

Chapter 45
45
………Yanda yay maganar kamar bashiba yasa Raudha ɗan taɓe baki da marairaice fuska. “Ni dai tunda banyi ba ai Alhmdllhi”.
Bai tanka mata ba, sai dai ya sake buɗe idanu yana kallonta. Sosai zuciyarta ke gudu a ƙirjinta dan ta fahimci abinda yake kallon. (Oh ita Raudha taga
takanta, mima ya kaita fitowa ba hijjab ko mayafi?) ta ayyana a zuciyarta a fili kamar zatai kuka.
“35, 32, 38… Uhhm da alama zaki iya….”
Saurin buɗe ido tayi jin ta ɗan zama kanta na son ganin kuma mi yake ma lissafin numbers haka? Da cewa zata iya. Saurin son zame masa kai tayi a ƙafarta
sai ya ɗan mintsini cinyarta. “Hi kokin manta sadaki na biya malama. Stay quite ko kiji a jikinki”.
Daina motsa ƙafafun tayi, sai dai tasa hannu ta kare ƙirjinta tana tura baki dan ta fahimci lissafin seize ɗinta na ƙirji, ciki, hips yake yi. Ji take
inama ƙasa ta tsage ta shige kawai ta huta dan kunya. Ita kam al’amarinsa yanzu ya daina bata mamaki sai dai tsoro.
Ganin yanda ta kare ƙirjin nata ya sashi ɗan yamutsa fuska da taɓe baki. “Yarinyar nan anya kuwa bazaki lalatani ba. To banda son lalatani inda na dosa
daban inda kika dosa daban tabbacin abinda ke ranki kenan”.
Ji Raudha tai mizai hana kawai ta saki kuka ta huta, kafin ta lalubo abinyi ya tashi zaune cike da ƙarfin hali yana gyara zamansa sosai a gefenta
dab. Fuska a yamutse idonsa ƙyam a kanta yace, “Da alama yarinyar nan zaki tsufa da wuri, dan ƙiba zakiyi bata wasa ba mtsoww nidai an cucan..” ya ƙare
maganar da ɗaukar kofin kunun da take sha. Zamansa ya gyara tamkar bashi ya gama zuba zancen ba ya kai kofin bakinsa bayan ya ƙarema abinda ke cikin kofin
kallo ya fahimci kunun tsamiya ne da Anne nayi, kuma Alhmdllhi yana matuƙar son sa.
Yunƙurawa Raudha tai zata tashi dan ya gama dabaibaiyeta a cikin cakwakiyar kunya ya dakatar da ita. “Amma gaskiya baki da tausayi Ameenatu! Haka akace
ki kula da miji idan baida lafiya!?…”
Yanda ya ƙarasa maganar da saki wata wahalalliyar atishawa da jin sunanta a bakinsa ya sakata dakatawa. Zuciyarta da ɗan fargaba ta dubesa dan tun dama
yazo wajen ya fara magana da ɗumin dataji kamar a kansa daya ɗaura jikinta take tunanin yana lafiya kuwa? Sai dai tsokanar magana daya ɓige da mata yasata
ture tunanin. Dubansa tai cikin ƙarfin hali, ganin yanda fuskarsa tai jaa musamman saman hancinsa, sai kuma idanunsa da ya buɗe suka haɗa ido suma sun sake
koɗewa fiye da jiya alamar babu lafiya. Saurin kauda nata tayi tausayinsa na ɗarsuwa mata a rai, dan tun fil azal haka take da saurin jin tausayin mutum
koda mugune (akwai lokacin da aka taɓa kama ɓarawo a makwaftansu, gashi dai itama haushinsa takeji saboda ya taɓa haurawa gidansu yay sata. Amma yanda aka
dinga jibgarsa sai itama taita kuka tana roƙon a barsa ya tafi).
A bazata taji ya damƙi hanunta ya kai saman goshinsa da ya ɗauka zafi sosai har tanajin harbawar jijiyoyin wajen. Cikin tsoro da tausayinsa da ya bayya a
cikin idanunta ta buɗe baki zatai magana sai dai ya rigata. Cikin taushi da sanyin murya da batasan yanada su ba. “Ki bani abinci naci kiban magani”.
Tausayinsa sosai ya sake kamata. Cikin damuwa da sake sanyaya muryarta itama mai sauƙin faɗi tace, “Murance har yanzun?”.
Idanunsa daya ɗan maida ya lumshe ya sake buɗewa. Sai kuma ya kwanto kansa kan kafaɗarta yana faɗin, “Kin damu da nine balle ki sani? An baki amanata
kin kasa riƙewa”. Nanma zafi taji jikinsa. Tai saurin rumtse idanu kunya na sake dabaibayeta da dariyar maganarsa (wai an bata amanarsa. Bama itace aka
bashi amanarta ba) Tasan ya kamata tun a jiya data fahimci ya dawo da mura tabi shawarar Bilkisu na kai masa magani. Amma ganin kamar Bilkisu ta manta sai
itama ta share batun dalilin abinda ya sake harmutsasu na faɗan ƙauyen Kauci. Dai-dai tana janye hanunta a goshinsa yace, “Kiramin Anne”.
A sanyaye tace, “Amma za’a tayar mata da hankali ai”.
Komai bai ceba ya ɗaura hanunsa saman cinyarta idanunsa a lumshe ya hau laluben wayarta. Saurin riƙe masa hannu tai a ɗan firgice jin yanda yake lalubeta
kamar da gayya.
“Ki daina fassarani da abinda bashi nake nufi ba, ni waya nake nema”.
Duk da idonsa a rufe yay maganar hakan bai hana Raudha ƙyaɓe fuska ba da tsuke ta. Sai dai batace komai ba ta tura masa wayar ta dunguri hanunsa datai
saurin saki a nata. Shima komai bai sake cewa ba ya ɗauka wayar ya ɗaura bisa hanunta. Murya babu wasa yace,
“Kiramin Anne”.
Badan taso ba tabi umarninsa tai kira number Anne ɗin. Sau biyu tai wringing aka ɗaga, a hanunsa ta ɗora wayar dan ita kam bata san mizatace da Anne ɗin ba.
Shima komai baice mata ba ya tashi da ga kafaɗarta ya kwantar da bayansa a kujerar yana kai wayar kunnensa. Dai-dai Anne na ambaton sunan Raudha cike da
kulawa….
“Anneee!”.
Ya kira sunanta cikin katseta. Ɗan jimm tayi kafin tace, “Ramadhan!”.
“Uhhyim”
Ya amsa yana sakin atishawa cikin rashin ƙarfin jiki. A take Anne ta rikice, dama tun jiya ta tsargu a muryarsa da suna waya. Amma koda ta tambayesa sai ya
nuna mata lafiyarsa ƙalau.
“Baka da lafiya ko! Haba Ramadhan abin nan kasa a ranka harya kwantar da kai haka?”.
“Anne cool down mura ne tun a uk nataho da shi”.
Sanin wahalar da shi da mura keyi ya saka Anne sake shiga damuwa. Cikin ƴar rikicewa tace “Haɗani da Aminatu”.
Maimakon bama Raudha da akace sai cayay “Anne ni dai kizo dan ALLAH, ko kuma na taho nan”.
Murmushi tayi mai sauti, ita kanta tasan badan raino irin na uwa taima Ramadhan ba tabbas a taɓare zai tashi. Sai dai batai sakancin masa rainon kaka ba
ta tsaya kansa da tarbiyyarsa tamkar uwa, kai ko uwarsa batajin idan da a hanunta yake zai samu tarbiyya makamanciyar wadda yake a yanzu. “To naji bani
Aminatu nace”.
Fuska ya tsuƙe yana ɗorama Raudha wayar a kunne sai kuma ya tashi zaune ya ɗauka kunun ya cigaba da sha badan yana masa daɗi a baki ba, saboda gaba daya
baida appetite. Gashi kuma yaji tasa sugar sai dai baiyi ƙarfi ba shiyyasa bai damu ba tunda yana ɗan sha wani lokacin duk da yana wahalar da shi idan akai
rashin sa’a…
Cikin damuwa Anne take amsa gaisuwar Raudha. Kafin ta ɗora da roƙo akan Ramadhan ɗin. “Ameenatu kiyi haƙuri nasan bazaki barsa cikin ciwo ba amma dan
ALLAH ki kula dashi sosai kinji. Ramadhan nada matuƙar rauni akan ciwo bai da juriya, ga rakin tsiya. Dan gaba ɗaya shafkewa yake tamkar yaron goye musamman
mura da bata masa kamun wasa. Wajigasa take matuƙa ga wannan ma naji kamar ta masa ƙarfi sosai halan baisha ko magani ba tun jiyan?…”
Cikin ɗan in ina da kunya Raudha tace, “Eh Anne gaskiya inaga bai sha ba, dan yau tunda safe ya fita a gida”.