Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 45

    “Amma garin yaya haka ta kasance Aminatu?”.

  “Uhm..uh…m Anne jiyanne ransa ɓace ya kwana saboda abinda ya faru a ƙauyan can, daga baya ma kulle kansa yay a ɗaki”. 

   Sosai Anne ta sauke numfashi mai nauyi tunda tasan halin kayanta idan ransa ya aɓaci. Alhmdllhi ma an samu canji bai sauke damuwar kan ƴar mutane ba,

koda yake bawai komaine ke ɓata ran nasa ya aikata ba. Cikin katse tunanunta tace, “Ai mijin nan naki kam sai addu’a Aminatu, wani lokacin idan ya birkice

tamkar mai iskoki a ka haka yake. Sai kinta haƙuri kinji. yanzu dai asamu kayan ƙamshi ai masa shayi da su citta ya fito sosai a ciki harda tafarnuwa. A

abincin da yace yana so ma asaka yaji ya ɗan fito. Nasan sa da son wanka da ruwan sanyi ki hanashi, hakama ruwa mai sanyi karki bari yasha koda fura ne ko

madara. Ruwan shansa ya zama da ɗan ɗumi haka, ƙafarsa ta kasance cikin safa. Yasha magani idan yaci abinci insha ALLAH zai taimaka masa hakan dan haka nake

masa idan yana mura. Zuwa anjima zan kira, idan zazzaɓin bai sauka ba sai a turo Dr Shamsu.”

     Raudha dake jin lisaafin kamar na ɗan goye ta jinjina kanta kamar tana a gaban Anne. “To Anne insha ALLAH yanzu duk za’ayi. ALLAH ya ƙara lafiya da

nisan kwana.”

   “Amin Aminatu ALLAH ya saka miki da alkairi yay miki albarka.”

  Cike dajin daɗi Raudha ta amsa mata kafin suyi sallama……..

      Wayar ta sauke da ga kunnenta tana sauke numfashi. Sai kuma taɗan kallesa ta maida kanta ƙasa da sauri ganin ita tsurama idanunsa kumburarru. “Mizaka

ci to sai a girka kafin magrib insha ALLAH an kammala?”.

    A hankali ya janye idanunsa a kanta batare da yasan ya shagala a kallonta ba tun tana waya da Anne. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar yarinyar ƙyaƙyƙyawa

ce, sai kuma baijin zai….. Kasa ƙarasa abinda zuciyarsa ke son faɗa yayi badan yasan dalili ba. Cikin dasashshiyar muryarsa ya sake dubanta yana magana a

hankali tamkar mai raɗa. “Koma miye ki dafa zanci”.

   Kanta ta jinjina masa tana miƙewa. Ya bita da kallo harta nufi stairs. Sai da ta ɓacema idanunsa ya sauke numfashi da ƙyar yana ɗaukar remote ya canja

television zuwa inda zaiga labaran shida na yamma.

   Sanin maitarsa da nama ya saka Raudha haɗa masa farfesun da taimakon mama ladi. sai kunun gyaɗa, madarar shanu dake gidan ta tafasa itama ta juye masa a

flask sai shayi. Aikin bai wani jasu da nisa ba tunda kaɗan iya cikinsa ne. Kuku kuma sukai sauran iya dai su dake sashen.

    Da taimakon mama ladi ta hauro da kayan anata kiraye-kirayen sallar magriba. Ya tashi a falon, dan haka Raudha ta amshi sauran kayan hanun mama ladi

tana mata godiya. Ɗakinsa ta nufa, tai knocking har uku bataji motsi ba, sai kawai ta tura ƙofar ta shiga da tunanin ko yana alwala. Ɗakin na nan tsaf yanda

ta gyarashi da safe, sai dai duk ya watsar da kayan daya dawo office akan gado da ɗan stool ɗin jikin gadon zuwa ƙasan carpet. Kayan hanunta ta ajiye tana

kwashe kayan, sai lokacin idonta ya sauka kansa a gado nannaɗe cikin bargo. Tausayi ya sake bata, ta ƙarasa ta gefesa, ɗan ranƙwafowa tai a ɗarare takai

hannu taja bargon daya rufa har saman kansa, rawar sanyi ma taga kamar yanayi, yana ƙoƙarin ture hanunta da son hanata janye bargon sai hanun ya shiga cikin

nashi, damƙewa yay da iya ɗan ƙarfinsa ya fisgota. Abinka da ba ƙarfi ɗaya ba sai gata gaba ɗayanta a kansa.

    “Wayyo ALLAH na”. Ta faɗa cikin matse fuska saboda ƙirjinta daya bugi jikinsa, sauƙinma laushin bargon ya bata kariya sosai. Ƙoƙarin tashi take kamar

zata fasa kuka, hakan ya bashi damar ɗaga bargon ya turata ciki. Rawa jikinta ya farayi, dan al’amarin yazo mata a bazata, ta shiga son fita da janye

jikinta daya tura a nasa ya matse, duk da a halin ciwo da yake ciki hakan bai hanashi sauke ajiyar zuciya ba. Cikin rawar muryar da ke tabbatar da baida

lafiya yake magana a kunenta cikin raɗa da sambatu na ciwo (Dan idan yana ciwo tofa akwai sambatu kamar su oh eh????. bazan faɗi suna ba dai???? lol.)

     “Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko’ina ciwo”.

    Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na

matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar

murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.

    Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”.

Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I’m sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana

sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.

    To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya

gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu

sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa

badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da

bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin

salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi. 

    “Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.

    Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.

    Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da

zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka

daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da

ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai

taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka’ar

ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button