BAKAR INUWA 46

“Maah! Lafiya kuwa naga kamar ranki a ɓace?”.
Duk da tasan halin ɗiyar tata na rashin ɗaukar abu da muhimmanci hakan bai hanata fara zayyane mata cikinta ba rai ɓace.
“Miyema bai faruba Mardiyya. Yanzu a duniyar nan babu abinda ke cimun rai da ƙonan zuciya sama da auren ɗan uwanku. Na tsani yarinyarnan da duk wani
mai alaƙa da ita a duniya. Ji nake zan iya kasheta da hannnuna wlhy…..”
“Wa’iyazubillah Maah miya kawo wannan maganar haka?”. Mardiyya tai saurin katseta.
“Humm Mardiyya kenan, yanzu ke tunda kike a duniya kin taɓa jin matar shugaban ƙasa mai shekara sha takwas? Jahila da ko karatun sakandire banajin ta
kammala? Daɗin daɗawa ƴar karuwai marasa tarbiyya da kowa yasan aikinsu a bayyane yake.” hawaye suka silalo mata, ta kai hannu ta share da cigaba da faɗin,
“Mardiyya na tabbatar a ƙuntace Ramadhan yake, biyayyar da yakema kakanninku ce kawai ta sakashi haƙura ya amshi raunanniyar yarinyar nan, wai dan takaici
sai yanzu take shiga jami’a. Matar shugaban ƙasa fa daya kamata ta zama vary educational, wayayya ta nunawa a duniya, wadda duk inda tasa ƙafa zata fiddashi
a kunya muma ta fiddamu. ALLAH dai ya tsinema wannan aure na Ramadhan albar…….”
“Haba dan girman ALLAH Maah wane irin furicine haka babu daɗin ji. Idan kin tsinema auren Brother tamkar shi kika tsinemawa dan zata iya yuwuwa yanzu
haka an samu rabo tsakaninsu. Maah ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ni wlhy banga wani aibu ga yarinyarnan ba. Inma iyayenta sunada wancan halin ai ba
itace kedashi ba. ALLAH kuma yana fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Karatu ko karancin shekarunta normal ne ni a wajena. Miye
amfanin ya auri wayayyar mai ilimin tazo ta zame masa damuwa shi da mulkin nasa damu kammu. Yanzu ko shi zai bama matarsa tarbiyyar data dace akan tsarin
mulkinsa ta tashi akai kuma yay alfahari anan gaba Maah. Dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan ki musu addu’a sai kiga wataran komai ya zama yanda kike so.
Kwana nawane zata kammala karatun ma, ina amfanin ya auri sa’arsa tazo ta rigashi tsufa……..”
Hannu Gimbiya Su’adah ta ɗaga mata a fusace. Cikin zafin rai ta nuna mata ƙofar fita. “Tashi ki fitarmin kafin na saɓa miki Mardiyya. Nama manta tare
nake da mara kishin kanta balle waninta. Shasha kawai da batasan abinda ke mata ciwo ba”.
Miƙewa Mardiyya tai ta ɗauka bag dinta da faɗin, “ALLAH ya huci zuciyarki Maah, amma nidai gaskiya na gaya miki, ita rayuwa bata da tabbas. Banga kuma
aibun yarinyarnan ba, hasalima yanda take da ƙarancin shekaru idan kika jata a jiki zakisha mamakin ribar da zaki samu akan shi kansa Ramadhan ɗin da kike
ganin kamar an nisantaki da shi. Ni na wuce dama zuwa nai na dubaku tunda ban samu shigowa gidan ba koda babbar salla”.
Ko kallonta Gimbiya Su’adah bata sakeyi ba. Itama saita fice a ranta tana nemawa mahaifiyar tasu shiriyar ALLAH da fatan ganewa. Dan tuni ta fahimci Adda
Asmah na ɗaya daga cikin masu rikita lissafinta akoda yaushe. Su kansu wani lokacin haɗata ake dasu taita zuba musu tujara kamar ba ita ta haifesu ba.
Waɗan nan maganganu na Mardiyya sun sake harzuƙa gimbiya su’adah. Rai ɓace ta shirya bayan sallar zuhur ta nufi sashen Anne. Abinda takan haɗa kwanaki
huɗu batai ba. Dan gaida surukai kullum baya cikin tsarinta duk da gida ɗaya suke rayuwa. Anne tayi mamakin zuwan nata amma sai ta danne ta tarbeta kamar
yanda suka saba. Babu wani ɓoye-ɓoye gimbiya Su’adah ta sanarma Anne abinda ke a ranta.
Murmushi kawai Anne keyi jin bayanin surukar tata. Ita bazata hanata zartar da hukuncin aurawa Ramadhan wata matarba, sai dai bazata amince a cutar mata
da jika ba dan ita kanta ta jima da fahimtar wacece Adda Asmah.
“Shike nan kije zan samu Dattijo da batun, zai kuma nema Ramadhan ɗin yaji tabakinsa. Idan ya amince da auren mu masu murna da farin cikine akan hakan.
Fatanmu ALLAH ya basu zaman lafiya kawai.”
Duk da ranta ya ƙara ɓaci sai ta amsa da amin. Ta fice zuciyarta na ayyana mata maganin Ramadhan da zatayi. Dan bazata taɓa yarda ya nunama kakaninsa
baya son auren ba. Tasan yana bijirewa shikenan bazasu bata goyon baya ba.
,,,,_,,,,__
Barci ya sake sha sosai har wajen sha ɗaya. Ring ɗin wayarsace ma ta tilasta masa buɗe idanu da ƙyar. Ido a rufe ya kai hannu a side drawer da nufin
kashe wayar sautin ring ɗin ya hanashi hakan dan yasan Maah ce. Komai bai kawo ransa ba sai tunanin taji baida lafiya maybe. Ya buɗe ido da ƙyar yay picking
yana kaiwa kunnensa.
“Barka da asiba Maah!”.
Gaban Gimbiya Su’adah ne ya faɗi, tai saurin cire wayar a kunenta tana kallo…..
“Maahhh!”.
Daya sake faɗa cike da kasala da barci ya sakata gaskata zarginta. Da sauri ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kanta na juya mata. (Har ita Ramadhan zai
amsawa waya yana tare da mace. Innalillahi….. Shikenan yaronta ya gama watsewa hanun jikar karuwai)…..
A ɓangaren Ramadhan kuwa tunanin network ne ya sashi sake dialing number ɗin tata da ƙyar yana kaiwa kunne da lumshe idanu. Sai dai switch up ma ake
sanar masa. Yanayin rashin ƙarfin jikin har yanzu ya sashi ajiye wayar kawai da tunanin zuwa anjima zai nemeta. Sai dai ya sake jan ƴan mintunan a kwance
kafin ya tashi zuwa bayi, sosai yunwa yakeji na ci masa hanji, badan haka ba baya tunanin zai iya tashi yanzun.
Shigarsa wankan baifi da mintuna biyu ba Raudha ta shigo hanunta ɗauke littafin data rubuta lecture ɗin jiya tana ɗan bitar abubuwan da bata fahimta
ba, dama tun ɗazun take zaryar dubashi da ga falo zuwa bedroom ɗin. Jin motsin ruwa a bayi ya sata yanke shawarar gyara ɗakin a gaggauce ta fice kafin ya
fito. Littafin ta ajiye a stool ɗin mirror batare data rufe ba. Cikin rashin sa’a tana tsaka da gyara kayan saman mirror ɗinsa dake a wargaje ya fito. Sosai
ta diririce, tai azamar juya masa baya zuciyarta na luguden daka….
Duk abinda tai akan idonsa ne, har yayi kamar zai basar yanda ya saba sai kuma ya canja shawara. Inda take ya cigaba da takawa yana goge sumarsa da
ruwa yaɗan taɓa kaɗan zuwa gefen wuyansa da kunne. Cak ya tsaya sakamakon idanunsa da suka sauka akan littafin nata, ya ƙurama hand writing ɗin ido
zuciyarsa na wani irin zillo, hatta da numfashinsa sizing yake wajen fita daga ƙirjinsa…..
Jin kamar tsayuwar mutum a kanta ya sata saurin juyowa saboda tsorata, dan bataji motsin ƙarasowarsa inda take ba. Yunƙurin barin ɗakin tai gaba ɗaya
taji ya cafko hanunta tare da fisgota ta dawo baya, gaba ɗayanta ta faɗa masa har ɗayan hannunta na ƙoƙarin sauka akan ƙirjinsa dake nason ruwa. Ido ta
rumtse da ƙarfi da son ɗage hannunta ta tokare tsakkiyarsu, sai hakan ya taimaka mata bata faɗa masa jiki gaba ɗaya ba. Sai dai kuma a bazata da tai niyyar
jan jikinta baya cikin in..ina tana faɗin, “I’m sorry”.